SHAFI NA ƊAYA

296 18 14
                                    

*WUUF*
  
    © *AMEERA ADAM*

               SEASON 1

   AUREN ABUH TSIGAI DA
               ALHAJI AUDU CHOGAL

_Ban yadda wani ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izinina ba. Don haka a kiyaye._⚠

☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO*

       SHAFI NA ƊAYA

  
   Tafe suke da bokitan roba saƙale a wuyansu, hannun Abuh ɗaya yana riƙe da ledar gyaɗa tana ɓarewa tana kaɗa ledar tana wasa da ita. Fatsime da yawunta yake ta biyawa ta ce, "Abuh saboda Allah wai ba za ki sammana amaron ba?" Abuh ta kuma murje biyu ta watsa a baki ta ce, "Fatsime wallahi ko ke mayyace sai dai idan na ci ki haɗa da ƴan hanjina ki cinye." Ƙwafa Fatsime ta yi ƙasa-ƙasa don ta san muddin Abuh ta ji ta kashinta ya bushe. Tsoronta suke kamar uwarsu don ko iyayensu basa tsoro kamar yadda suke tsoron Abuh, Abuh ta zura hannu ta ɗebo wata gyaɗar tana niyyar ɓarewa Salele da ya taho da gudu ya warci ledar gyaɗa ya ƙara da gudu a guje ya sha kwana. Abuh kallon kwanar da ya sha ta yi ta cire bokitin da ke wuyanta ta ce, "Ƙundun uba! Wallah yau idan cikin Babah Laraba za ka koma sai na bika na karɓi a bata." Da gudu ta rufa masa baya ta sha kwanar da ya sha Abuh bata tsaya ko ina ba sai ƙuryar ɗakin Babah Larba, Baba Laraba da ke ɗinkin muhuci da sauri ta matsar da ƙafafuwanta don saura kaɗan Abuh ta bi ta kansu ta wuce. Cen bayan gado ta ƙwaƙwulo Salele ta murɗe masa hannu ta kwato gyaɗarta.

   Babah Laraba ta zuba tagumi cokin takaici tana kallon Abuh, tana shirin magana Abuh ta haure ƙafafuwanta ta fice daga ɗakin tana gyara zani.  Fitarta tsakar gida ke da wuya ta hango shigowar Bukar, murmushi ta yi masa tana sunne kai ƙasa ita a dole kunyarsa take ji. Gabansa ne ya fadi don yadda ya ga Abuh ya tabbata ba lafiya ce ta shigo da ita cikin gidansu ba, ƙarasawa ya yi yace, "Abuh yau ke ce a gidan namu?" Abuh ta ɗaga ledar gyaɗarta tana nuna masa ta ce, "Wallah Salele ne ya fisgen gyaɗa ni kuma na biyo shi na ƙwace a bata." Babah Laraba ta leƙo da kai cikin takaici ta ce, "Saboda Allah Abuh ai ko mutuwa tana gudun idon mahaifi, ban da ma haka Salele fa ƙaninki amma tsabar rashin mutumci irin naki ki biyo shi har cikin gida ki murɗe shi ki kwaci abar ki."

Abuh ta ɓata fuska ta ce, "Wallahi ya ci darajar Bukar ma da sai na kusa ɓalle hannunsa, kuma gobe ma ya ƙara." Tana gama faɗa ta yi gaba, Baba Laraba ta ce, "Wannan ƙaddara gara da Allah ya sa aka yi haka, gayyar tsiya ki je gara ma Alhaji Chogal ɗin ya kwasa. Wannan masifar idan aka kawo mana gida ai mun shiga uku." Bukar bin bayan Abuh ya yi ya fara lallashinta ya ci gaba da faɗin, "Abuh kin ga ke fa budurwata ce kuma Salele ƙanina ne duk abin da ya yi miki be kamata ki bi shi har ɗakin Babah ki hukunta shi ba, da kin gaya mini sai na siyo miki wata gyaɗar." Abuh sai da ta ɓare gyaɗa uku ta watsa a baki ta ce, "Amma Bukar ka san dai yadda Salele ya raina ni." Bukar yace, "Ki barni da shi zan koma gidan." Ɗan sauya fuskarsa ya yi cikin damuwa ya ci gaba da cewa, "Wai kuwa ya maganar Alhaji Audu Chogal ina fatan ne yanzu babu ita." Idon Abuh ne ya ciko da ƙwallah ta ce, "Ɗazu na ji sun yi waya da Baba wai yau zai turo manyansa, dama niyyata daga ɗiban ruwa na wuce shagonka. Bukar anya ba za mu gudu ba kuwa, wallahi bana ƙaunar Chogal a shekaru fa ina jin ya girmi Babanmu." Hankali a tashe Bukar yace, "Abuh ba za mu gudu ba! Amma gaskiya ba a yi mini adalci ba Abuh, a ƙallah na shafe shekara biyar ina dakon soyayyarki babu wanda be san soyayyarmu ba, yanzu haka za a ɗauke ki a bawa mutum tsofai-tsofai da shi?" Abuh ta fara share hawaye ta ce, "Wallahi ni bana ƙaunarsa bana sansa kawai ya siye Baba  da kuɗi ne"

  Bukar ya haɗiyi yawu me ɗaci yace, "Abuh jeki gida bari na je na samu Baffana ko zai iya wani abu akai." Yana gama faɗa ya juya da sauri zuciyarsa na wani irun  zafi.

   Abuh na karya kwana ta hango su Fatsime kawunansu ɗauke da bokitan ruwa, na ta ma sun ciko shi da ruwa sun yi kama-kama. Ƙarasawa ta yi fuska babu walwa ta karɓa, suma basu tanka mata ba saboda sun lura da halin da take ciki, kuma ko ba a faɗa musu ba sun san zancen ba zai wuce maganar aurenta da Alhaji Audu Chogal bane.

Ba su yi tafiya me nisa ba su Fatsime da Laure suka shige gida ba kasancewar gidansu akan hanya yake. Tun daga nesa ta hango motarsa tsaye a ƙofar gidansu, tsaye yake a jikin motar shi da wasu abokansa biyu. Ɗaure fuska ta yi tamau ta ci gaba da tunkarar wurinsu, Mahaifinta ta hango ya fito daga gida ya tsaya a wurinsu Alhaji Audu Chogal da alama gaisawa suke yi. Guntun tsaki ta ja har ta kusa shigewa gida Mahaifinta yace, "Ke Abuh me kike yi haka wannan wanne irin sakarci ne kina ganin mutane za ki wuce, ban hanaki irin wannan sakarcin ba?" Alhaji Audu Chogal ya gyara tsayuwarsa yana gyara ƙafarsa mara lafiyar ya sakarwa Abuh murmushi yace, "Baba ayi haƙuri ƙuruciya ce. Sannan Baba wannan ɗiban ruwan kamar yana wahalar da ita, zan turo masu haƙar rijiya su haƙa muku ko daga gefen bishiyar cen ne, amma kafin lokacin zan bayar da wani abu a samu yara su dinga ɗebowa." Baba ya washe baki ya shiga zabga godiya, Abuh da ke gefe baƙin cikin duniya ya cika ta. Baba ya kalli Abuh yace, "Maza ki shiga ki shirya ki zo suna jiranki." Abuh bata amsa masa ba saboda takaici ta wuce ciki tana shiga ciki ta ji shigowar Baba, haka ya tasa ta a gaba har sai da ta sauya kaya ya sata sako mayafi ya tasa ta a gaba ta fito waje.

   Tana zuwa tsaye ta yi ko sallama ba ta yi musu ba, Alhaji Audu Chogal ya yi murmushi yana kallon Abuh yace, "Barka da zuwa Gimbiya." Abokinsa da ke gefe Alhaji Lamiru yace, "Amaryarmu fushin me ake yi da mu?" Abuh ta kalle su wani baƙin ciki yana ƙara rufeta musamman da ta kalli yadda gashin bakinsu da gemunsu yayi fari fat da furfura, ga gijibgi duk ya saukar musu (Naman tsufa) fatar fuskarsu duk ta tattare. Alhaji Saminu da ke ɓangaren hagu yace, "Abuh nace a cikin ƙawayenki ko akwai wacce zaki haɗa haɗani da ita? Don sababbin jini irinku su tafiya ta fi miƙawa da ku." Abuh ta buga musu harara ɗaya bayan ɗaya ta murtuke fuska ta ce, "Audu Chogal wallahi ka fita sabga ta! Na gaya maka bana son ka bana ƙaunarka, me zan yi da kai abu tsofai-tsofai, Saboda Allah wanne irin zalinci ne wannan? Ka san ina da masoyi ne amma ka nemi rabani da shi. Wallahi matuƙar ka aureni shafin tashin hankalinka ya buɗe kenan" Alhaji Audu Chogal ya yi wata dariyar Shaƙiyanci yana lasar baki yace, "Abuh ban da abinki meye marabar dambe da faɗa? Irinmu da kike gani mun fi yaran kula da tattali ga mace, tsaf za a ji mu luf ni da ke abinmu nawa ne aka yi haka da su, kema ki saki jiki ayi wannan tafiyar da ke kawai." Ya da fa gwiwar ƙafarsa mara lafiyar ya wurga ta gaba ya ƙarasa wurin Abuh, bakinsa ya fara turawa saitin kunnenta yace, "Yarinyar karki yi wa kanki buƙulu ni da kike gani na fi matashi sabon jini nagarta." Da sauri Abuh ta matsa gefe aikuwa Alhaji Audu Chogal suka kalli juna shi abokansa suka fara dariyar shakiyanci, Abuh ta rasa wanne abu za ta yi ta fanshe baƙin cikin da suka ƙunsa mata, da sauri ta ƙarasa wurinsa ta shatalo ƙafarsa mara lafiyar ta fara jijjigata, Alhaji Audu Chogal ya layi ji kake dim ya faɗi a ƙasa.

Abuh bata damu ba ta ci gaba da jijjiga ƙafar tana cewa, "Chogal wallahi ka kiyaye ni, na rantse da Allah idan ka takura wata rana sai na jirge ƙafa na mayar da kai Audu gundul ba audu chogal ba." Tana gama faɗa ta saki ƙafar ta wuce cikin gida, sai a lokacin Abokansa suka ƙarasa suna masa sannu. Alhaji Audu Chogal ya jinjina kai yace, "Ƙwal uba ni yarinyar nan za ta yi wa lalata, ta jawa kanta da wata biyu na yi niyyar a saka rana amma wallahi sati biyu za a saka."

To gamu a wannan duniyar🤭 Idan na ga kun bani damar ci gaba sai mu lula amma idan babu comments sai na ja gefe kamar yajin ƙosai.

Coming soon👇🏼
15/12/2021

Ummou Aslam Bint Adam🌚

WUUF HAUSA SERIES NOVELWhere stories live. Discover now