END OF SEASON 1

55 8 0
                                    

*WUUF*
  
    © *AMEERA ADAM*

               SEASON 1

   AUREN ABU TSIGAI DA
               ALHAJI AUDU CHOGAL

_Ban yadda wani ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izinina ba. Don haka a kiyaye._⚠

☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO*

       SHAFI NA GOMA

    🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

    Abu ba ƙaramin buguwa ta yi ba saboda Chogal da iya ƙarfinsa ya hankaɗe ta, sai da ta dafa ƙasa tana runtse ido sannan ta samu ta fice da sauri don tana tsoron kar ƴaƴan Chogal su fito su same ta su yi mata lilis don ta san idan ta shiga hannunsu babu mai cetonta sai Allah.

  Chogal gudu ya rinƙa yi ko waiwayen bayansa baya yi saboda yana gudun kar Gundundun ta biyo bayansa. Kamar daga sama Ale Saminu dake cikin mota ya hangi Abokinsa na gudu yana ɗan tisgiɗawa har yana haɗawa da adungure, kamar wanda aka cewa Kura ta kunto daga kejinta. Da sauri ya faka motarsa ko ƙarasa kashe ta bai yi ba ya rufawa Chogal baya don ganin ya taro abokin nasa domin idan har ya ce zai bishi da mota yana  iya shiga wani lungun da mota bata iya shiga. Saboda ya lura abokin nasa baya cikin hayyacinsa. Kasancewar unguwar ba wata cikakkiyar unguwa ba ce mai mutane da yawa, unguwar ta yi tsit babu mutane sosai sai jefi-jefi.

  Chogal yana gudu jikinsa ya bashi wani na biye da don haka yana waigawa ya hangi Fuskar abokinsa Ale Saminu, a zatonsa Chogal ya ɗauka Abu ce ta fara rikiɗa zuwa wata siffar don ya gama tsorata da lamarinta. Hakan ya sa ya ji hanjin cikinsa ya ƙara yamutsa masa ya ƙara ƙarfin gudun nasa, yana fatan ya samu ya shiga cikin jama'a ko sa taimaka masa. Daga can farko layi Chogal ya hangi wata runfar mai shayi cike da matsa, wani sanyin daɗi ya ji don ya tabbata ko ba komai ya zo wurin mafaka.

Ga duk wanda ya ga yadda Chogal yake gudu ba ƙaramin mamaki zai yi ba, domin karon farko idan ka ganshi ɗauka za ka yi sabon mahaukaci ne mai ci da hauka tuburan, saboda fararen kayan jikinsa duk sun yi buɗu-buɗu kamar wanda aka sassaƙo daga cikin ƙasa.  Ga shi yana gudun yana haɗawa da adungure saboda matsalar ƙafarsa idan ya ce zai ta fi da gudu ya rinƙa gurɗewa kenan yana kifa goshi a ƙasa. Wannan ta sa ya yi wa kansa liɗifi ya rinƙa haɗawa da adungure saboda ya samu ya fita daga wannan ƙangin na Aljanu. Lokacin da Matasan nan suka hangoshi tsayawa suka yi suna kallo wasu daga cikinsu har da masu dariya. Sai dai babban abin da ya ɗan ɗaga hankalinsu ganin wani tiƙeƙen mutum na biye da shi a baya. Da yake Ale Saminu ya fi Chogal ƙiba da tumbi wannan ta sa yana tafe tunbinsa na taya shi, shi ya sa ya kasa cimma Chogal.

  Chogal na zuwa wurinsu ya rarumi ƙafar wani matashi da yake yankar biredinsa yana lakuta bota (Blue band) yana limshe idanu alamar shayin ya matuƙar yi masa daɗi. Bai yi aune ba sai ji ya yi antankwaɓo masa shayi mai zafi  jikinsa, ai kuwa cikin jin zafi shima ya saki kofin sai a kan ƙafar Chogal mai lafiya. Zafi da raɗaɗin ruwan zafin ya sake firgita Chogal don a tunaninsa da gaske tsotse ɗayar ƙafar tasa Gundundun za ta yi. Kamar yadda ya ji Abu ta faɗa kafin ya fito. Wani irin yanayi ya rinƙa ji kansa na neman juye masa, ga hasken rana da ya haske masa fuska wacce ta hudo daga jikin saman kwanon rumfar mai shayin. Wannan hasken ya sa Chogal ya kasa tantance a wace duniyar yake domin ya gama saddaƙarwa da shi dai rayuwarsa ta zo ƙarshe.

Ale Saminu ne ya rankwafa kan Chogal ban da haki babu abin da yake yi. Mamaki ne ya kashe shi a tsaye yana ganin yadda Abokinsa ya yi zuru-zuru duk ya fita hayyacinsa kamar wanda ya daɗe yana jinya, ga kansa hagu da dama gabaɗaya ya yi molo gabasa da yamma, kudu da arewa. Cikin tausayawa ya ce, "Alhaji Audu sannu!"

Chogal na ɗagowa ya ga fuskar Ale Saminu sai kuwa ya zabura zai tashi da gudu, da sauri Ale Saminu yace, "Ku taimaka min don Allah ku danne mini shi." Ai kuwa Chogal na sake jin haka ya fara kai musu duka ta ko'ina don a wannan karon ya ci alwashin ba zai sake bari waɗannan aljanun su yi galaba a kanshi ba, don a tunaninsa Abu ce take biye da shi da tawagartata aljanu suke ƙoƙarin zuƙe ɗayar ƙafar tasa. Mutanen da ke gurin sai da suka yi da gaske sannan suka samu suka riƙe Chogal ƙam suna mamakin wannan sabon lamarin da ya sami wannan dattijon mai shekaru. Saboda duk ɓangaren unguwar babu wanda bai san Chogal ba, saboda yawan auri sakinsa da yawan aure-aurensa a kai-a kai. Wasu daga cikin mutanen wurin har sun fara ɗora zarginsu a kan tsohon saurayin Abu wato Bukar, don babu wanda bai ji labarin auren Abu tsigai da Alhaji Audu Chogal ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 24, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WUUF HAUSA SERIES NOVELWhere stories live. Discover now