*WUUF*
© *AMEERA ADAM*SEASON 1
AUREN ABU TSIGAI DA
ALHAJI AUDU CHOGAL_Ban yadda wani ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izinina ba. Don haka a kiyaye._⚠
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO*
SHAFI NA TAKWAS
Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗewa Chogal saboda wannan sabon lamarin da ya gani dangane da iyalansa. Hakanya rinƙa ƙwala musu kira amma babu wanda ya bi ta kansa, ita kanta Uwar 'ya'ya luf ta yi a cikin banɗaki duk ɓuruntun da yake uffan bata ce masa ba.
Jikinsa a sanyaye ya taka zuwa ɗakin Abu tana jin motsinsa ta yi luff kamar mai bacci, zama ya yi a ƙasa ya haɗa kai da gwiwa yana tunani baƙin ciki da suka cika shi. Abu na daga saman gado ta leƙa shi sai ta ji duk ya bata tausayi amma a gafe ɗaya da ta tuna yanda ya rufe idonsa akanta har ya rabota da masoyinta sai ta ji takaici da haushinsa ya lulluɓeta.
MU YI WAIWAYE...
Zainba Mato Magini shine ainihin cikakken sunan Abu Mahaifiyarta sunanta Bishira Mahaifinta sunansa Muhammadu Lawan amma duk faɗin garinsu anfi saninsa da Mato Magini. Asalinsu 'yan garin Rigana ne ɗaya daga cikin ƙauyikan Bichi dake ƙarƙashin jihar Kano. Mahaifanta sun shafe shekara goma da aure sannan Allah ya azurtasu da samunta. Abubukar Bawa shine ainihin sunan Bukar saurayin Abu. Mahaifinsa Malam Bawa aminin Mahaifinta ne ba shi da abokin a faɗin garin Rigana sama da shi.
Abu ta yi karatunta tun daga Primary har zuwa secondry, sai dai tana aji biyu a babbar Sankandire aka cireta a ka yi mata aure. A islamiyya ta yi karatunta daidai gwargwado kuma tana da fahimtar karatu sosai. Abu ba fara bace ruwan tarwaɗa ce kuma ba wata kyakkyawa bace sosai ba za ka kira ta mummuna ba kuma ba za ka sata a kyawawa a jin farko ba. Tana da ɗan gashin kai daidai misali wanda idan aka yi kiso duk baya zai sauka kan kafaɗarta. Doguwa ce amma tana da ɗan jiki amma kallon farko idan ka ganta za ka yi mata kallon doguwa amma idan ka ƙare mata kallo zaka tabbatar 'yar duma-duma ace ajin farko.
Abu na ɗaya daga cikin fitunannu marasa ji a cikin garin domin kowa ya san wacece Abu tsigai tun tana yarinya. Lokacin da tana ƙarama somi samin far rashin jinta Mahaifiyarta har ɗaukanta ta yi ta kaita wurin masu magani don a tunaninta ajlanu ne suka shefe, sai dai duk wurun masu maganin da ta kaita sai dai a ce lafiyarta ƙalau. Lokacin da Abu tana da shekara Takwas akwai lokacin da ta maƙale a ƙarƙashin gado, a lokacin kakatar Inna tana raye tana kwance a bakin gado ta rinƙa tsira mata allura a mazaunanta. Tsohuwa sai ta fara bacci sai cikin bacci ta ji tsuu an tsira mata allura, a firgice take buɗe ido ta yi ta soshe-soshe tana leƙe-leƙe amma Abu na ganin haka take maƙalewa ta gama dube-dubenta ba tare da ta ganta ba. Ƙarshe dai sai haƙura ta yi da baccin. Abu bata son da haka ba tana ɗagowa za ta tsira mata allura sai ji ta yi Inno Kakarta ta zuba ranƙwashi a ka, a gigice ta fice daga ɗakin tana sosa kai nan kakarta ta fita tana ta sababi. Ire-iren ɗiban albarkar da Abu take yi ba ƙaramin damun iyayenta yake ba. Tun tana yi iya cikin gida har ta fara fita tana tsokanar mutane kullin a cikin kawo ƙararata ake yi.Sai dai wani ikon Allah duk cikin faɗin ƙauyen babu wanda yake ƙaunar Abu yake yi mata uzuri a duk abin da take yi sai Bukar tun ana yi masa kallon sakarai har wannan shaƙuwar ta su ta riƙeɗe zuwa soyayya, sai dai lokacin da ta fara zama budurwa duk abin da Bukar ya yi mata nasiha a kai tana rage shi ko da bata daina shi duka ba. Lokacin da take aji biyu na ƙaramar Sakarandire iyayenta dana Bukar suka fahimci halin da ƴaƴansu suke ciki na soyayya. Wannan ba ƙaramin daɗi ya yi musu ba haka daga mutanen garin kowa ya fahimci soyayyar da ke tsakanin Abu da Bukar, amma ƴan tsurku haka suka rinƙa kai suka ga Innarsu Bukar tun bata ɗauka har ta fara ɗaukan zugarsu. Lokacin da Abu take aji uku na ƙaramar sakandire Allah ya yiwa Mahaifin Bukar rasuwa, wannan mutuwar ba ƙaramin girgiza Mahaifin Abu ta yi ba kasancewar kowa ya san yanda suke tare basa rabuwa kodayaushe.
YOU ARE READING
WUUF HAUSA SERIES NOVEL
Short StoryAbuh bata damu ba ta ci gaba da jijjiga ƙafar tana cewa, "Chogal wallahi ka kiyaye ni, na rantse da Allah idan ka takura wata rana sai na jirge ƙafa na mayar da kai Audu gundul ba audu chogal ba." Tana gama faɗa ta saki ƙafar ta wuce cikin gida, sai...