*WUUF*
© *AMEERA ADAM*SEASON 1
AUREN ABU TSIGAI DA
ALHAJI AUDU CHOGAL_Ban yadda wani ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izinina ba. Don haka a kiyaye._⚠
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO*
SHAFI NA UKU
Chogal ido ya zubawa Abu da take ta fisge-fisge a gefe ɗaya yana murmushi a ransa don ya san wannan abun tana yin sa ne saboda bata son sa, don idan be manta ba kusan haka suka yi da Mariya wacce take ta uku yanzu, lamarin Mariya sai da ta kai su har da cize-cize. Abu tana haɗiye wata tsokar nama ba ƙaramin daɗinta ta ji ba, gudun kar ya gano Aljanun ƙarya take yi ya sa ya ta kafe ledar naman da idanu, sai kuma ta kalli wata kusurwar bango lokaci ɗaya ta bushe da wata irin dariya. Idanunta ta kai kan kaskon ƙasa da yake cike da wuta saboda yanayin sanyi da ake ciki, lasar baki ta fara yi tana dumfara wutar ta ce, "Wutaaaa wayyooo wutaaa! Ki zo kin zo a kan gaɓa."
Cikin Chogal ne ya kaɗa yana fargabar abin da Abu za ta yi, don yadda ya ga ta nufi wutar gadan-gadan ba ƙaramin tsoro ya ji ba. Tunowa ya yi da kashedin da ta yi masa ana gobe ɗaurin aure lokacin da ya sa aka turo masa ita ƙofar gida, ban da cika da batsewa babu abin da take yi. Murmushi ya yi mata ya janyo hannunta yana faɗin, "Amaryata wallahi na matsu gobe ta yi a shafa fatiha ki zama mallakina, a ranar zan nuna miki irin muhimmancin da kike da shi a wurina." Da sauri Abu ta fisge hannunta ta ce, "Wallahi ina tsammanin tsautsayi ne yake neman ratso da kai, shi ya sa ka kafe kai da fata sai ka aure ni. Amma na rantse har da Allah ka nemi wani abu a wurina sai na nemi makami na gundule ka sai na ga da uwar me za ka yi auren gaba." Tana gama faɗa ta yi gaba. Wata dariyar Chogal ya saki yana shafa farin gemun bakinsa yace, "Yaro man kaza. Mariya ma mun buga da ita ta haƙura yanzu ga ta da cikin na biyu. Kema wuyarta ki shiga hannun Chogal ikon Allah za ki yabawa aya zaƙinta."
Firgigita ya dawo daga duniyar tunani lokacin da ya ji Abu tana ƙoƙarin kinkimar Kaskon wutar, da sauri ya fisgo hannunta shi da ita suka faɗa kan gado. Shirgegiyar ƙafarsa ɗaya ya ɗora akan ruwan cikin Abu, hannunsa ɗaya yana kan ƙirjinta har yana iya jin yadda bugun zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri. Chogal ji ya yi wata sabuwar ƙaunar Abu na ƙoƙarin jefa shi a wata duniya, tuni ya kasa riƙe kansa Abu ba tayi tsammani ba sai jin gemun Chogal ta yi a gefen fuskarta, tunanin hanyar da za ta ƙwaci kanta take don ta san ko bacci Chogal yake ba za ta iya hankaɗe shi daga jikinta ba.
Saitin kunnensa ta laluba ta gantsara masa cizo cikin shammata, don lokacin da Chogal ya riski bakin Abu a gefen fuskarsa har ya fara lulawa wata duniyar yana lumshe ido, saukar azabar cizon ya sa ya taƙarƙare ya kwara wani irin ihu haɗe da miƙewa a cikin gigita, don a wannan lokacin har ya take ƙafarsa mara lafiyar be sani ba. Cen jikin bango ya koma ji kake rigija ya faɗi yana dafe kunne, saboda yadde yake yi masa kuɗa kamar zai gutsire.
Mariya da Sabuwa suna laɓe a bakin ƙofar su Abu dama haka suke yi duk lokacin da Chogal ya yi aure za su laɓe domin jin abin da zai wakana tsakaninsa da amarya. Inna Salme ita ce matarsa ta biyu uwar gidansa ta rasu shekaru masu yawa, a lokacin da ta rasu su biyu ne kawai matansa daga Inna Laraba sai Inna Salame. Inna Salame macece me haƙurin gaske shi ya sa zamanta da Chogal ya yi ƙarko, ya yi aure-aure babu a dadi tun yana auren zawarawa har ya fara nemam ƴan mata yana aure dukda yawan shekarunsa. Mafi yawa daga cikin ƴan matan da yake aure be fi su yi haihuwa ɗaya zuwa biyu ba auren yake ɓalɓacewa saboda tsarin gidan Chogal da ake yi masa kallon kitse...
Chogal ɗan kasuwa ne da duniya take gara masa yake fantamawa yadda ya kamata, a cewarsa idan da kuɗi me zai hana shi jin daɗin rayuwa ya auri wacce yake so kuma a lokacin da yake so. Inna Salame tana ji tana ganin yadda Chogal yake cin karensa babu babbaka da aure-auren, sai dai ita a yanzu ta sallama shi don sai su shafe wani lokaci babu wani da ya shiga tsakaninsu. Yadda ya bata matsayin Uwar ƴaƴa ita ma ta karɓi wannan sunan na Uwar ƴaƴa saboda duk wacce ta fita ita take ajiyewa ƴaƴanta. Mariya ita ce matarsa ta uku amma bayan ita sai da ya auri ƴan mata biyu da bazawara ɗaya sannan ya auro Abu.
A ƙa'idar Chogal kafin ya yi aure ya kan tara matasansu ya ɗebi kuɗi kamar dubu goma-goma ya bawa kowaccensu, sannan ya kora musu jawabin cewar aure zai yi. Suna jin haka sun san inda maganarsa ta dosa, saboda ƙa'idarsa ce idan ya auri Budurwa sai ya kwashi wata guda a ɗakinta idan kuma bazawara ce sati biyu yake yimata. Wannan dubu goma-goman da yake basu ladan kwanansu ne, Uwar ƴaƴa ce kawai yake iya rufe ido ya bata dubu ashirin saboda yawan yaran da ke ƙasanta. Wannan dubu goma kuwa idan ya ba su ji suke kamar sallah domin kuɗi baya taɓa fita daga hannun Chogal komai siya yake ya ajiye haka kayan abincin ma sai yadda ya ɗiba za a sarrafa. Idan kina amarya a gidan Chogal ko kallansa kika yi kika wanka masa mari ba zai ji zafin marin ba saboda tsantsar ƙauna da kulawar da yake baki, amma da zarar ya fahimci kin yi lagwai wato kin ɗauki ciki kin fara laulayi za ki koma cikin sahun matan gidan.
Mariya da Sabuwa ne suka kalli juna saboda yadda Ihun Chogal ya karaɗe kunnuwansu, Sabuwa ta yi ƙasa da murya ta ce, "Mariya yau Alhaji ko ya gamu da gamonsa ne? Na ji ban ji ihun Amarya ba sai ihun Ango ba kamar yadda muka saba ji ba." Mariya ta kuma manna kanta jikin bango don ta ƙara tabbatarwa abin da kunnenta ya ji ta ƙanƙance murya ta ce, "Wasa ne farin girki. Ya ɗaga mata ƙafa ne amma ko cinya ɗaya ya sharɓa mata za ta gane kurenta."
Abu da ke gefe tana mayar da numfashi ta fisge ɗankwalin kanta sai ta ɗare kan gado ta miƙe tsaye a kai, ɗaga kanta sama ta yi tana wani irin girgiza kai kamar me shirin tayar da bori. Fuskar gadon ta je ta riƙe da hannuwa biyu ta fara jijigawa nan take gadon ya fara girgiza tana faɗin, "Don Allah ku daina jana wallahi ba ni bace wayyo Allahna." Mariya da ke laɓe ta saki dariyar mugunta ta ce, "Ai na gaya miki sai dai idan ba Chogal ba."
Chogal fusata ya fara yi da wannan iskancin na Abu don ya tabbata da tana da wata cutar za a sanar masa kafin lokacin auren, kuma yadda ake ba shi labarinta ya san za ta aikata fiye da haka don haka ya ɓata fuska yace, "Ke Abu meye haka kike yi har sai mutanen gida sun ji mu..." Be rufe baki ba ta wurga masa fulo sai kuma ta suri fulo ɗaya tana kai duka ko'ina tana cewa, "Ni ba Abu bace, ni Gundundun ce." Chogal a fusace yace, "Gundundun ɗin uwarki ni za ki rainawa hankali." Abu ta wani zabura ta buga tsalle ta jefar da Fulon hannunta ta ce, "Gundundun kake zagi? Wallahi yau sai mun Gundule ka."
Daga kan gadon ta zuba uwar sufa ta faɗa kan ruwan cikin Chogal da ya yi ɗaiɗai a gefe, a firgice ya buga ƙara har sai da Abu ta tsorata cikin zuciyarta take tsoron karfa ta yi masa illa, ganin yana lafiya ya sa ta suri kwandon wanke-wankenta da yake cike da kwanuka, cokula da wuƙa ta fara wurgi da kwanukan tana cewa, "Tun da ka zagi Gundundun wallahi sai mun gundule ka." Chogal na ganin haka ya zabura da ya miƙe tsaye sai dai rashin nutsuwar yadda zai sarrafa ƙafarsa ya sa ya dinga faɗuwa yana tashi don gudun gundulewar da Abu za ta yi masa.
😂😂😂😂🤣🤣🤣 Ina muku fatan alheri.
Masu comments Allah ya biya ku wallahi bana zama shi ya sa bana replay. Amma billahi ina mugun yin ku.🥰
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
YOU ARE READING
WUUF HAUSA SERIES NOVEL
Short StoryAbuh bata damu ba ta ci gaba da jijjiga ƙafar tana cewa, "Chogal wallahi ka kiyaye ni, na rantse da Allah idan ka takura wata rana sai na jirge ƙafa na mayar da kai Audu gundul ba audu chogal ba." Tana gama faɗa ta saki ƙafar ta wuce cikin gida, sai...