*WUUF*
© *AMEERA ADAM*SEASON 1
AUREN ABU TSIGAI DA
ALHAJI AUDU CHOGAL_Ban yadda wani ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izinina ba. Don haka a kiyaye._⚠
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO*
SHAFI NA HUƊU
Su Mariya dake laɓe a bakin ƙofa da sauri ta ja da baya tana kallon Salame da alama ta jiyo ihun Chogal, a ɗan tsorace ta taɓo Salame ta ce, "Salame an ya yarinyar nan ba wani mugun abu take yi wa Alhaji ba, ni fa na fara tsorata kin ji ihunsa fa. Kin san kuma abin zai sa Alhaji kuka dube shi ƙara. Gani nake mu afka ɗakin karta kashe shi mu shi ga uku, don mu ta cuta tun da mune masu ƴaƴa." Salame ita ma jikinta ya yi sanyi amma sanin halin chogal idan ya yi sabuwar amarya ya sa take ganin duk ihun da zai yi ba za ta iya tura ƙofar ba. Suna nan tsaye suka ji Chagal ya ƙara fasa wata ƙarar tare da jin wata irin ƙarar sulba ƙwaaaal. Da sauri Mariya ta dafa ƙofar za ta buɗe Salame ta fisge hannunta sa sauri tana faɗin, "Mariya kin shirya ta fiya ki bar 'Ya'yanki wurin Uwar 'Ya'ya ne? Karki manta Alhaji idan ya yi amarya baya ganin kan kowa da gashi, idan kin manta na tura miki Adama Uwar Salihu ina ce a daren da aka kawo ki Alhaji ya sallame ta, saboda mun ji yana ihun kuna artabu da ke har kina cizonsa, wai ita me miji ta tura ɗaki domin ceto shi amma daga in da yake ya danƙara mata saki. Yanzu ga Salihu yana galantoyi wurin Uwar 'Ya'ya. Ni kam ba da ni ba gaɗa a makwantai, duk lalacewa na fi son na zauna da 'Ya'yana ko ba komai za su dinga jin ɗumina. Tun da haka Allah ya ƙaddara mana, bar su cen su ƙarata kwashe-kwanshe ne ya kai shi kwaso wacce za ta gasa masa aya a hannu. Dama na ji an ce yarinyar bata ƙaunarsa."
Mariya na shirin magana suka ƙara jin ƙwaaal sai kuma suka ji rigijaaaa alamar faɗuwa, Mariya jiki a sanyaye ta fara cewa, "Maganarki na hanya Salame gara da kika tunatar da ni da tuni na yi wa kaina wai Allah da fa haka zan ta fi na bar Abashe ina ji ina gani." Salame ta saki murmushi tana faɗin, "In sha Allah ma bubu in da za mu duk wuya ma jure in dai ba don kansa zai sallame mu ba idan ya gaji da mu."
Lokacin da Chogal ya f
ga da gaske Abu take, nan take hantar cikinsa ta fara kaɗawa saboda fargaba, a zabure ya ci gaba da faɗuwa yana tashi babban burinsa kawai ya samu sukunin zare sakatar ɗakin da ke cen saman ƙofa, amma tashin hankali da faɗuwar da yake yi ya hana shi damar buɗewa. Cikin sarewa ya juyo da niyyar yi mata magana nan idanuwansa suka suka akan hannunta da ke ɗauke da wata sharɓeɓiyar sabuwar wuƙa. Wulwulata take yi a hankali sai kuma ta murtuke fuska kamar bata taɓa dariya ba ta fara faɗin, "Ka zagi Gundundun ko? Yau me hana in gundule ka sai Allah. Matso-matso gara a yi komai ta laluma amma idan ka bari Gundundun ta harzuƙa ba iya gundul zan mayar da kai ba, sai na bi kinnuwanka duka na yanke na bawa Ɗan uwatana Buɗur ya cinye su." Chogal da ya rasa mafita ya tausasa murya yana faɗin, "Don Allah ki yi haƙuri Abu wallahi ba zan ƙara zaginki ba..." Da sauri ta buga masa tsawa tana cewa, "Ni ba Abu bace, cene Gundundun mu ji." Kamar wanda take biya masa karatu Abu na faɗar Gundundun Chogal yana biyawa, "Gundundun! Gundundun!" Ta koma bakin gado ta zauna tana nuno shi da wuƙar ta ce, "Miƙe tsaye mana ba a faɗar sunan Gundundun a zaune, kuma ka dinga yi kana zaro idanu da harshe domin Gundundun ba kanwar lasa bace."Jiki na rawa Chogal ya miƙe tsaye yana dafa ƙafarsa mara lafiyar, saboda ba zai iya jurar tsayuwa ba tare da madogari ba. Haka ya dinga zaro harshe haɗe da zaro ido yana faɗin, "Gundundun! Gundundun!"
Mariya ta kalli Salame ta ce, "Wai kina jin me nake ji kuwa Salame?" Salame ta daɗa matsawa har tana bangaje Mariya ta ce, "Ina zan sani Mariya duk kin kankane matsa na ji." Salame ta sake manna kunne a jiki kamar za ta huda jikin ƙofar. Salame ta saki wata dariya tana kallon Mariya ta ce, "Kin ji abin da nake gaya miki ko? Wallahi idan ka shiga tsakanin Chogal da amarensa kaine kwaɓarka za ta yi ruwa. Kina ji fa wai har waƙa suke wai, tsundundun masoyiya. Ke kuwa sun tsunduma duniyar masoya ba dole Alhaji ya ya rangaɗa waƙa ba." Salame irin matan nan ne da komai suka ji sai sun ƙara gishiri akai, Mariya ta ƙara kara kunnenta ta ce, "Ke Salame ni daɗi na dake ƙara gishiri a miya ni ba wani Masoyiya da na ji ya faɗa, na ji dai kamar ya ce Tsundundun ki rage ƙarya don Allah." Salame haushi ya ɗan kama ta ta ce, "Ai abincina ce. Aikin banza ke ranar na ki amarcin ina ce har rawar Salawaitu kuka yi." (Gaskiya na yi kewar salawaitun Inno da Goggo, Jariri fans fatan alheri😂 )
YOU ARE READING
WUUF HAUSA SERIES NOVEL
Short StoryAbuh bata damu ba ta ci gaba da jijjiga ƙafar tana cewa, "Chogal wallahi ka kiyaye ni, na rantse da Allah idan ka takura wata rana sai na jirge ƙafa na mayar da kai Audu gundul ba audu chogal ba." Tana gama faɗa ta saki ƙafar ta wuce cikin gida, sai...