*WUUF*
© *AMEERA ADAM*SEASON 1
AUREN ABU TSIGAI DA
ALHAJI AUDU CHOGAL_Ban yadda wani ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izinina ba. Don haka a kiyaye._⚠
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO*
SHAFI NA SHIDA
Abu na ganin haka da sauri ta dira ƙasa tana ja da baya don wannan karon ta tsorata fiye da koyaushe, a hankali ta lallaɓo tana leƙensa ta fara cewa, "Badaru maza ka zo ya faɗi, muuuuuu ku zo gayyar ahalina na baku gangar jikinsa gabaɗaya." Abu ta yi haka ne don ta gane Chogal ba luff ya yi mata ba, ta san idan ta ƙara razana shi to shakka babu zai watssake ya koma saman gado domin ya kamo fanka. Amma babban abin da ya ƙara tayar mata da hankali sai ga Chogal tsit ko motsi bai yi ba bare ta saka ran zai tashi. Cikinta ba ƙaramin kaɗawa ya yi ba har a fili ya bada sautin Ƙuuu! Nan take gumi ya gama wanke mata jiki fargaba ta kamata tana ayyana yadda za a wayi gari da mutuwar Chogal a cikin Ƙauyensu. Tuno labarin wata amarya ta yi da aka ce ta sawa mijin da aka aura mata guba a abinci, har ta ji labarin an yanke wa Amaryar hukuncin ɗaurin rai da rai. Wani wawan kuka ne ya kwace mata wanda ba ta zace shi a wannan lokacin ba, kamar sabuwar munafuka haka ta fara matse ƙwalla ta ƙarasa tana buga ƙafarsa tana cewa, "Alhaji ta shi dare ya yi." Ta faɗi haka ne ita ala dole aljanun jikinta sun sauka don bata son wani ya gano aljanun ƙarya take yi.
Wannan karon ma shiru ya yi mata babu amsa babu motsi, don dole haka ta zage ta sunkuya ta fara ƙoƙarin juyo da shi amma ta kasa, can gefe ta zauna ta ci gaba da rusar kuka don ta rasa mafitar abin da za ta aiwatar. Motsi ta ji daga waje ta ji muryar Uwar 'ya'ya na yi wa Salame magana, da sauri ta fita don ta shaida musu halin da ake ciki don gabaɗaya ta gama tsorata. Uwar 'Ya'ya na ganin Abu ta fito ta juya ɗakinta a guje baka ganin komai sai tashin da zanin jikinta yake yi sama, don tun kafin ta shiga ɗaki zanin ya rufawa kansa asiri ya nemawa kansa matsuguni yashe a tsakar gida. Salame da sauri ta saki butar hannunta tuni ruwa ya samu abin da ya jima yana nema wato ya fara malalewa a ƙasa, buta ta yi gabas murfinta ya yi yamma. Salame ko kallon gabanta bata yi ta faɗa ɗaki ɗankwalinta na ƙoƙarin faɗuwa. Abin duniya goma da ashirin ya kwaɓewa Abu takaici ya kamata, jiki ba ƙwari ta ƙarasa ƙofar ɗakin Salame tana bubbugawa. Daga cikin ɗaki ƙaramin yaron Salame da tun shigarta ya farka ya fara cewa, "Umma fooo" Salame ta fisgo shi da sauri tana toshe masa baki ta ce, "Yi a nan dan ubanka, da safe na ƙwashe na fita da shi da mu fita mu jawowa kanmu jafa'i." Yaron ganin bai saba sakin fitsari da kashi a ɗaki ba ya sa ya maƙale kafaɗa yana fisgewa yace, "Ummm-ummm ni Fooo!" Haushi ya kama Salame ta zuba masa ranƙwashi ta ce, "Fooo ɗin ubank? Za ka saurara mini da zan cen fooo ɗin nan ko sai na fyaɗe ka."
Jin zafin ranƙwashi ya sa yaron ya fashe da kuka cikin fushi ya sauka da gudu ya nufi bakin ƙofar yana kiciniyar buɗe ƙofar har Allah ya bashi nasarar buɗewa. Da sauri Abu ta riƙo hannunsa don ta san idan ba haka ta yi ba Salame ba za ta buɗe ƙofar ba. Salame na ganin haka ta yi kukan kura haɗe da zuba uwar kabbara tana tofawa Abu ta fisgo hannunsa Ɗanta, Abu na ja Salame na ja jin wuya ta yi wuya ya sa Ɗan Lami ya fara kuka yana, "Wayyo haƙarƙarina! Hammtata!" Bai rufe baki ba Allah ya bawa Salame sa'a ta hankaɗe Abu ta fisgo ɗanta ta rufe ƙofa ji kake kiriiiif ta danna sakata tana sauke ajiyar zuciya.
Uwar 'ya'ya da ke ɗaki tuni ta sharkaɓe zaninta da fitsari, don yadda ta fara jin gwagwarmayar su Abu tuni zuciya ta hau saƙa mata abubuwa kala-kala. Lokacin da ta ji bugun kofa ta jiyo Ɗan Lami yana ihu tuni ta fara ayyana ko su Badarun da ta ji Abu na ambata sun fara tsotse ɗan wurin Salame, kuka ta rushe da shi ta yi ƙasa da murya tana cewa, "Dama na faɗa! Wallahi a kwashe-kwashen Alhaji sai ya kwasowa kansa yanzu ga shi abin bai tsaya iya kansa ba har an haɗa da Salihu..." Ba ta rufe baki ba ta ji ƙarar bugun ƙofarta, tsit ta yi kamar ruwa ya cinyeta, Abu ta ci gaba da buga ƙauren tana kiran Uwar 'ya'ya.
YOU ARE READING
WUUF HAUSA SERIES NOVEL
Short StoryAbuh bata damu ba ta ci gaba da jijjiga ƙafar tana cewa, "Chogal wallahi ka kiyaye ni, na rantse da Allah idan ka takura wata rana sai na jirge ƙafa na mayar da kai Audu gundul ba audu chogal ba." Tana gama faɗa ta saki ƙafar ta wuce cikin gida, sai...