SHAFI NA BIYAR

70 11 2
                                    

*WUUF*
  
    © *AMEERA ADAM*

               SEASON 1

   AUREN ABU TSIGAI DA
               ALHAJI AUDU CHOGAL

_Ban yadda wani ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izinina ba. Don haka a kiyaye._⚠

☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO*

       SHAFI NA BIYAR

    Abu warwas ta yi a ƙasa tana sauke numfashi da ƙyar, tana daga nan a kwance ta jiyo ihun Chogal. Mariya ce ta ƙarasa wurin a ɗan ruɗe don ba ƙaramin mamaki ta yi ba ace yau Chogal ne amarya ta taso shi har yana neman taimako. A cikin ɗaki Uwar Ƴaƴa na jin ihun Chogal bata yi wata-wata ba ta sake maka masa muciya a baya tana faɗin, "Kai da Badarun na haɗa ku na ɗebe muku albarka. Munafukai da girmanku kuna bibiyar gidajen ƴan mata ko uwar me za ku yi musu? Shi ma Badarun Allah ya shigo da shi sai na sheme shege a wurin nan in ya so ayi haihuwar guzuma Ƴa kwance Uwa kwance." Uwar Ƴaƴa cikin takaici ya sake bugawa Chogal muciya a ƙafafunsa, wannan karan shiru ta ji ko motsi Chogal baya yi bare ya yi yunƙurin ihun da za a kawo masa taimako.Tsoro ne ya ɗan kama Uwar Ƴaƴa a zuciyarta take ayyana karfa ta kashe mutum a cikin ɗakinta, kamar wacce aka zubawa bulala haka ta zabura ta fice daga ɗakin don sanarwa da matan gidan abin da yake faruwa da su.

  Tana fita ta ci karo da Mariya a tsaye tana sanɗa, Abu na kwance tana sauke numfashi. A tsorace ta kalle su ta ce, "Mariya ba dai ɗakinku ya fara faɗawa ba?" Mariya ta ɗauka Chogal Uwar Ƴaƴa take nufi don haka ta ce, "A'a ina zai faɗa ɗakina ai ya yi nisa, naki ɗakin dai kin ga shi ne a kusa nan ya faɗo." Uwar Ƴaƴa ta sauke ajiyar zuciya sai faman zare ido take kamar an jijjiga ɓera a buta ta ce, "Ina jin fa ya mutu! Saboda dukan da na yi masa bana jin shirun da ya yi lamɓo ya yi." Da sauri Mariya ta ja baya tana zare ido, Abu da ke cen gefe cikinta ya bada wani sauki ƙuuuu. Nan take ta hau haɗa gumi tuni ta daina jin zafin faɗuwar da ta yi tana fargabar halin da za ta shiga idan aka ce Chogal ya mutu, amma gudun kar su gano ta ya sa ta ci gaba da kwanciya a inda a take tana satar kallonsu a ƙasa-ƙasa.

Mariya ta leƙa ɗakin a tsorace amma duhun ɗakin ya hanata gane abin da Uwar Ƴaƴa ta faɗa, fashewa ta yi da kuka tana faɗin, "Yanzu shi ke nan gatanmu ya ƙare. Wallahi dama gudun komawa rugarmu ya sa na haƙura nake zaman gidan nan amma tun da babu shi na ga ta kaina." Uwar Ƴaƴa ta dube ta da mamaki ta ce, "Mariya wai me kike faɗa akan Kwarto kike kuka me ye haɗinki da shi." Mariya ta tsahirta da kukan ta ce, "Waye Kwarton Uwar Ƴaƴa."

Uwar Ƴaƴa ta nuna ɗakinta tana faɗin, "Ga shi cen kwance cikin su Raliya." Salame ce ta ƙaraso wurinsu a hankali tana dafa bango, jin haka ya sa Mariya ta ce, "Uwar Ƴaƴa Alhajin ne ya koma Kwarto? Kin ga fa Amaryarsa nan can dai ta su ce ta haɗo su shi ne ya fito ya faɗa ɗakinki. Sai a lokacin idon Uwar Ƴaƴa ya sauka akan Abu da ke gefe suna haɗa ido Abu ta zaro mata ido da harshe haɗe da taune baki tana hura hanci, nan take gaban Uwar Ƴaƴa ya faɗi da sauri ta janye idonta. Fargaba goma da ashirin ce ta haɗewa Uwar Ƴaƴa, ga ta dukan Mijinsu da ta dinga yi bata san hukuncin da zai yanke mata, ga kuma ta muzuran da ta ga Amaryarsa ta na yi mata, don da alama ta lura yarinyar kamar me iskokai ce.

  Kamar Kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka Uwar Ƴaƴa ta dubi Mariya ta ce, "Wallahi na ɗauka Kwarto ne ya faɗo mana na dinga tafka masa Muciya a ƙafa shi ne na ji shi ya yi shiru ina tsammanin ko mutuwa ya yi." Mariya na jin haka ta faɗa ɗakin tare da kunna ƙwan lantarkin ɗakin, nan take ɗakin ya yi tarwai da haske. A cen cikin su Raliya ta hango Chogal ya yi sharɓan sai numfashi yake saukewa da ƙyar.

   Gabaɗaya suka shige ɗakin dan jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Abu na daga nan in da take ta ɗago da kai ta leƙa ɗakin ta hango Chogal na sauke numfashi da ƙyar. Murmushi ta sauke tana jinjina kai ta tashi saɗaf-saɗaf ta koma ɗakinta ta datse kofar ɗakin.

WUUF HAUSA SERIES NOVELWhere stories live. Discover now