SHAFI NA TARA

40 6 2
                                    

*WUUF*
  
    © *AMEERA ADAM*

               SEASON 1

   AUREN ABU TSIGAI DA
               ALHAJI AUDU CHOGAL

_Ban yadda wani ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izinina ba. Don haka a kiyaye._⚠

☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO*

       SHAFI NA TARA

     Wannan lamarin ba ƙaramin ɗaga hankalin Chogal ya yi ba don bai yi tunanin haka daga wurin Abu ba, a zatonsa yanda ta faɗa haka za ta aiwatar, ƙanƙame Ɗanlami ya yi a jikinsa saboda dukan da Abu ta yi masa har cikin zuciyarsa. Shi kansa Ɗanlami ya gama tsorata da Abu don ko haɗa ido  da ita baya son yi, ban da wagen Abu babu abin da yake yi saboda azaba. Abu can gefe ta ja ta zauna kamar mutuniyar kirki tana bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo, damin kuɗin hannunta ta kalla sai ta kalli su Salame ta ce, "Kuɗi! Waye yake son kuɗi?" Haɗiye yawu Salame da Mariya suka yi maƙwat! Har sai da sautin haɗiyar yawun ya bayyana a fili. Abu ta yi murmushi a fakaice cikin zuciyarta tana cewa, "Za ku shigo hannu ne muje zuwa..."

   A yanda Abu ta nutsu sai ka rantse babu wani iskanci da take yi musu, kallon Chogal ta yi da sauri Ɗanlami ya sunne kai ƙasa, saboda tsoron Abu. Ta fara juya kuɗin hannunta ta ce masa, "Gundundun uwar albarka. Gunduma uwar Badaru da Mai gatari. Kowa ya yi shiru ya saurari abin da Uwar Badaru za ta faɗa, domin yau ranar tonon asiri ce. Yeeeeh Mai bankaɗa bankaɗo mana sirrin da Chogal ya binne a kan matansa." Tun bata rife ba cikin Chogal ya bada wani irin sauti ƙuuu! Duk yanda ya so daurewa kasawa ya yi domin wani gumi ne ya shiga karyo masa ta ko'ina. Ɗanlami da ya tsorata da jin muryar Abu ya sake ƙanƙame Mahaifinsa yana kuka. A zuciye Chogal ya kife yaron da mari yana cewa, "Shegen yaro ni za ka yi wa iskanci zauna nan kamar yanda sauran 'yan uwanka suka zauna. Ja'iri kana fama da goshi kamar jirginya doso tasha sai tiƙeƙiyar ƙeya kamar zangero." Chogal na gama faɗa ya dongwarar da shi a ƙasa cikin takaici, Ɗanlami na jin haka ya ƙwaƙume ƙafafuwan Mahaifinsa yana ihu.

Abu ta ce, "Chogal kana safarar kawunan bil-adam mun ji ka fara cinikin kawunan Mariya da Uwar 'ya'ya." A firgice suka ɗago suna kallonsa. Ɗanlami ya fara kuka yana cewa.

"Baba afata ciwo, wayyo keyata"

   Ganin hankalin mutanen ɗakin ya tafi kan Chogal ya sa Abu ta fakaice su ta ƙyasta laita (lighter) a jikin labulen da take jiki a zaune ba su yi aune ba suka ga hayaƙi na tashi. Wani tsalle ta daka ta bar wurin ta ci gaba da furjin yawu tana ɓaɓɓaka dariya kamar mahaukaciyar gaske. Kallon Ɗanlami ta yi ta ce, "Kai ko ka yi mini shiru ko na sa Batoyi ya ƙone ka mu sha romon kayan ciki." Salame da ke gefe ta fasa kuka tana cewa, "Don girman Allah kiyi haƙuri Abu..." Tun bata rufe baki ba Abu ta buga mata tsawa tana cewa,

   "Gundundun nake uwar Badaru idan kika sake ce mini Abu sai na sa miki wuta." Haɗiye yawu Salame ta yi, Abu ta mayar da kallonta ga Chogal ta ce, "Ka fito ka gayawa iyalanka gaskiya tun Gundundun bata tona maka asiri da kanta ba." Chogal ban da maiƙo babu abin da yake yi, ya yamutsa fuska kamar ya ci kashi baki na rawa ya ce, "Ni kuma me na aikata? Wallahi bansan wani safarar kawuna da ka ce ba."

    Abu ta fakaici su Uwar 'Ya'ya ta ga yanda suka yi musu duru-duru ta ɗebi kuɗi ta watsa musu nan take suka hau budirin ɗiban kuɗi suna wawaso. Abu ta yi murmushi mara sauti ta ci gaba da cewa, "Adadin kuɗin da mutum ya ɗiba adadin bulalar da za a yi masa." Kamar waɗanda ta gindayawa sharaɗin Mutuwa da sauri suka rinƙa wurgar da kuɗaɗen suna matsawa daga jikin kuɗin kamar waɗanda suka ga wuta. Su Raliya da suke gefe sun cika fam saboda takaicin abin da Abu take yi a gabansu babu halin ramawa.

  Abu ta waiga wurin Uwar 'Yaya ta ce, "Ke da za mu wahalar da ke ba domin ke me haƙuri ce, kuma ta kanki za mu fara tun da kece giwar gida." Uwar 'Yaya ban da zare idanu babu abin da take yi, cikinta na kaɗawa ta fara miƙa hannuwa alamun roƙo tana yi wa Abu magiya. Abu ta fuske dariya na son ƙwace mata ta ce, "Uwar 'Ya'ya tusar Fararen aljanu kawai za ki yi mana ki fice daga ɗakin nan shi kenan kin gama aikinki." Hawaye bibbiyu na bin fuskarta ta ce, "Gudundun ta mun rai wallahi ko kalarsu ban sani ba bare na san yanda suke tusa." Abu ta murtuke fuska ta ce, "Wato kina nufin ba mu da galihu a wurinki kenan?" Da sauri Uwar 'Ya'ya ta ce, "Wacece ni banza wofi, ba haka nake nufi ba." Abu ta zurawa Chogal ido sai kuma zarowa Ɗanlami ido ta mayar da kallonta ga Uwar 'Ya'ya ta ce, "Kin ƙarawa kanki laifi, kuma sai na gwada miki yanda ake tusar Fararen aljanu kin ji a jikinki. Kafin nan ki yi mana tusar jinsinku." Uwar 'Ya'ya ta taƙarƙare za ta yi tusa amma ta nemi tusa ta sara. Duk yanda ta so ta yi tusa abin ya garara tana shirin yin magana Abu ta ce, "Za a ɗumama miki jiki domin kin bijirewa Gundundun."

WUUF HAUSA SERIES NOVELWhere stories live. Discover now