WUUF*
© *AMEERA ADAM*SEASON 1
AUREN ABU TSIGAI DA
ALHAJI AUDU CHOGAL_Ban yadda wani ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izinina ba. Don haka a kiyaye._⚠
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO*
SHAFI NA BIYU
Alhaji Saminu ya sunkuya ya fara cukwikwiyo babbar rigar Alhaji Audu Chogal yana yunƙurin tashinsa tsaye, nan take ya fara nishi har tusa ta ƙwace masa ba tare da ya sani ba. Takaici ne ya kama shi ya dangwarar da Alhaji Audu Chogal yana faɗin, "Audu don Allah ka dinga taɓukawa haba! A ce mutum ya saki jiki sharaf ji har tusa na ƙwace mini yanzu da yarinyar nan tana tsaye mutumcina be gama zubewa ba? Don Allah ka tashi kar yara su fara taruwa a wurinmu." Alhaji Audu Chogal irin mutanen nan ne gajeru masu faɗi, ba laifi yana da ƙiba sosai don ba za a sashi a sahun marasa jiki ba. Alhaji Lamiru ya miƙa masa sandarsa yace, "Don Allah ka ta shi mu tafi yarinya ƙarama ta dinga yaƙunaka, sai kace ita ce autar mata. Alhaji Audu Chogal ya yi ƙwafa ya yunƙura da ƙyar ya tashi ya kalli Abokansa da suka ɗaure fuska saboda takaicin abin da Abu ta yi musu. Dafe ƙafarsa ya yi mara lafiyar ya wurgata gaba sannan ya gyara tsayuwarsa yace, "Ale Saminu duk abin da za ka faɗa tsaya iya kaina amma muddin za ka faɗi magana mara daɗi akan Abu wallahi za mu raba gari da kai." A hassale Alhaji Saminu yace, "Wallahi kuwa indai yarinyar cen ce sai ta kusa kashe ka muddin ka aureta, tun da akan kunnenka ta ce za ta mayar da kai gundul. Idan ta gunduleka sai in ga wacce uwar za ka ƙara chogalawa har kaje zance." Yana gama faɗa ya zagaya ya buɗe murfin mota ya shiga, Alhaji Audu Chogal ya ci gaba da mita yana bambami sannan ya buɗe mota suka shiga sannan suka bar ƙofar gidan.Abu na shiga gida ta faɗa kan Inna ta fashe da kuka tana cewa, "Inna don Allah ki yi wani abu wallahi bana son waccen tsohon ni ƙyanƙyaminsa nake ji." Inna zuciyarta a dagule ta fara lallashin Abu cikin tausayawa, "Abu ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara domin kin san halin Malam da kafiya idan za ki mutu tun da yace wancen Alhajin za ki aura shi za ki aura. Ke dai mu ci gaba da Addu'a In sha Allah komai zai zo mana da sauƙi, kuma sai mu yi fatan Allah sa haka shi ya fi alheri."Miƙewa Abu ta yi ta faɗa ɗaki ta ci gaba da kuka.
Da daddare bayan isha'i Abu na zaune tana ta cika tana batsewa, don ko abincin da Innarta ta bata ta ƙi ci. Fatsime ce ta shigo cikin shirin tafiya dandali, har ƙasa ta tsugunna ta gaishe da su Inna. Baba da yake cin tuwo kallonta yake a watse sama-sama ya amsa gaisuwarta, miƙewa ta yi ta ce, "Inna Abu tana ciki?" Da sauri Baba ya haɗiye lomar tuwo saura kaɗan ya ƙware yace, "Keeee maza zonan zo me Abu za ta yi miki?" Fatsime ta hau sosai kai ta ce, "Dama dandali na biyo mata mu tafi." Baba ya ware hannuwa ya watsa mata daƙuwa yace, "Gidanku! Dandalo ba dandali ba. Ba tun rannan na gargaɗeki akan biyo mata zuwa dandali ba? Ko baki san an yi mata mijin aure ba? Za ki fice mini daga wurin nan ko sai na ƙarya ki uku." Tun be rufe baki ba Fatsime ta fice daga gidan saboda ta san halin Baba sarai yana iya zane ta ciki da waje. Abu da ke rakuɓe a bakin ƙofa tana jin fitar Fatsime ta rushe da kuka har tana buga ƙauren ɗakin saboda takaici. Baba kallon wurin ya yi yace, "Ba kuka ba idan kukan jini za ki yi wallahi ba za ki fita wurin waccen figaggen yaron ba." Inna ba ƙaramin tausayin Abu take ji ba don haka ta kalli Baba dukda bugawar da zuciyarta take yi ta ce, "Malam saboda Allah ka na ganin wannan abin da kake yi wa yarinyar nan shi zai sa ta ƙaunaci mutumin nan, Malam har kullin ana gargaɗin iyaye akan auren dole. Yarinyar nan fa ita kaɗai gare mu ka tuna kafin mu same ta sai da muka shafe sama da shekara goma sha, wannan be isa ka bar ta ta zani abin da ranta yake so ba. An ya Malam wannan baka ganin nan gaba za ka bar baya da ƙura? Na fi kowa sanin halin Abu da taurin kanta tun da ta nuna bata son mutumin nan wallahi ba za ta taɓa karɓarsa ba. Mutumin nan fa ba yaro bane ko kai fa ya girme maka amma wai ka haɗa shi da ƴarka dududu shekarar Abu nawa yarinyar da ko sha takwas bata cika ba." Tsawa ya buga mata yana faɗin, "Dama ai na daɗe da fahimtar ke kike ziga ta wallahi aure kam babu fashi, ga gidan da za ta je ta huta muma mu huta uwar me za ta samu a gidan Bukar yaron da tireda gare shi sai aikin kanikanci da yake. Uwar me za ta samu ban da wankin kayan baƙin mai..." Be rufe baki ba Umaru ɗan maƙotansu ya yi sallama hannunwamsa ɗauke da buhun semovita ɗayan hannun ɗaurin doya ce. Da sauri Baba ya miƙe yace, "Umaru su Alhajin sun ƙaraso ne?" Ajiye kayan Umaru ya yi yace, "Ba Alhajin bane amma ance a yi sallama da kai."
YOU ARE READING
WUUF HAUSA SERIES NOVEL
Short StoryAbuh bata damu ba ta ci gaba da jijjiga ƙafar tana cewa, "Chogal wallahi ka kiyaye ni, na rantse da Allah idan ka takura wata rana sai na jirge ƙafa na mayar da kai Audu gundul ba audu chogal ba." Tana gama faɗa ta saki ƙafar ta wuce cikin gida, sai...