MANUFATA. 7/8

28 4 0
                                    

❤‍🩹MANUFATA❤‍🩹

        Na

Maryam Abubakar Datti




P7-8


wani irin hargitsa gidan ta keyi ko ina tayi kacakaca har 'dakin Nasrin saidai ko alama babu kuma tabbas bashi ma ya hawo da akwatinanta ba wani mai taxi ne to ina xata ganshi kuka ta saki tana 'dora hannuwanta a kanta sakamakon tunawa da tayi da tulin sarakunanta tun daga aurenta na farko xuwa yanxu duk ciki ta ha'da don ma dama tasha sayar da wasu in aurenta ya mutu yawanci sarakunan ke rufa mata asiri tana kashe wutar gida da na kanta wani irin kuka take mai ban tausayi kusan awa hudu tanayi ta gaji kuma sam bata zargin kowa face wannan mai taxi sabida ranar daga ita har Nasrin hawowa su kayi suka barshi yana kawo musu kayansu



kallon matar yayi tana bayaninta

Yadikko ta kalli Inna yace da kin daure kinci abinci kinsha magani kinga likita yace harda rashin cin abinci.. Kwalla Inna ta share komai baya ranta illa fatan xaman lafiyar auren Hanifa yadikko da tasan damuwarta ta fara magana

kinga mariya ki rage wannan damuwar domin b xata kaiki ga komai ba sai ara miki ciwo yarinya nacan tana kokarin kula da mu kunanan kina 'dagawa kanki hankali ai na fiki fahimtar Hanifa yanxu na kuma tabbata ko mai xai faru a wannan karon da wuya ta kashe auren saidai ta tauna aya don tsakuwa taji tsoro kuma ma addu'a ya kamata muna mata

Inna ba tace komai ba har yadikko ta gama maganarta ta ara da ki kwantar da hankalinki IA suna tare har mutuwa ni kaina xanyi komai wannan karon domin ta kasance da mijinta "Allah yasa Inna tace.. yadikko tace amin suka cigaba da hira


ganin ya kusa dawowa tayi tunanin karma ya dawo ya gane wani abu ya faru ta mi'e ta fara gyara komai ta gama ta shiga kitchen yau IA xan baka mamaki in bawa kaina mamaki take furtawa domin cikar burina xanyi komai saidai tayi shiru kuma tana ajiye wukar da take yanka vegetables da shi tayi shiru tana kwalla bansan mai take tunani ba naga ta saki kuka tana jifa da wukar taji muryarsa yana furta "Ya dai baby?

ha'diye kukan tayi taje tana son rungumarsa cikin kissa saidai ta kasa hakan ya fahimta ya furta xo ki rakani na cire kaya nagaji yau sosai yana ri'o hannunta suka nufi 'dakinsa

jawota yayi xai manna da jikinsa ta xame tana sunkwi da kanta irjinta na bugawa har yana hangowa 'dan arasawa yayi dukda mamaki da yake ciki na yanayinta kamar wacce batasan Namiji ba ya ara kamo hannunta xai mannata ta xame har tana fa'duwa kujera tashiga kwalla

cikin mamaki ya furta Hanifa how long xaki cigaba da waina ni a kan hakkina?  hawayen ne ya gangaro yana kallonta saidai ba tayi magana ba yaci gaba

aurenki fa uku kafin ni mainene ya saura baki sabib.. ta furta pls kayi hakuri

yace bangane inyi hakuri ba kindai san ba xamu cigaba da xaman aure a haka ba ko? ba tayi magana ba yaci gaba yana furta gaskiya xan 'dauki komai amma wannan baxan jure ba yayi shigewarsa bathroom ta kama kanta tana hawaye

yana fitowa wankan yaga tana inda take yayi tsaki ya furta kije kawai u are not usefull so banga anfaninki ba gaskiya... cikin fargaba ta mi'e tana furta pls kayi hakuri IA xan gyara yace toh wai me ke baki tsoro?  ko sona ne bakiyi?  ko da yake komai na saka ki bakyayi is lyk xaman kanki kikeyi kawai wannan auren bayada anfani ko ka'dan ina ganin gara mu hak... yaji ta pls kayi hakuri xan gyara IA ta matsa tana tayashi fitar da kayan da xai saka dukda ya lura tana kakkaucewa batason kallonsa 'daure da tawul


shiru yadikko tayi ita kanta tana yawan tanbayar kanta shin mai yake sakawa da zarar Hanifa tayi aure sai rashin jituwa ya fara tsakaninta da mazajenta shin laifinsu ne ko nata saidai tayi shiru ta jawo wayarta tana lalubar nombobi ta kalla ta furta da ku xan fara IA wannan karon xanyi maganin abin wannan auren mutu ka raba ne inma wani ke saka mata hannu xan binciko in kuma ita ke da wata matsala xan gano IA kuma xanyi komai in gyara domin Hanifa 'ya ce duk taurin kanta da rashin ji tanada son Iyayenta da burin 'daukakasu nan haka kan ma Adnan ya aureta tasa ya biyawa Malam Hajj ganin malam bashida lafiya lokacin tana tsoron kada ya rasu baiyi hajj ba tunda wannan butulun mustapha in ya kasa biya masa....

MANUFATAWhere stories live. Discover now