💫 KYAWUNA JARABTA TA💫
✍️M SHAKUR
EPISODE 1️⃣
Tudun Yola, Kano!
Baban Anguwace kuma sabuwa dan babu mutane haka sosai a anguwan, saidai irinsu uncompleted building da ake kan ginawa dakuma sababbin gidaje da ba'a dade da tarewa cikiba.Baban gidane dayasha fenti milk color, kana ganin ginin gidan kaga ginin irin family house dinan, tsakar gidan mai bala'in fadi, ga katuwar bishiyan mangwaro a tsakar gidan datai y'ay'a sosai dudda basu nunaba, flat biyune agidan wani babban dankareren flat saikuma wani karamin flat mai kamada boys quarters agefenshi, gidan kana ganinshi kasan bawani gidan mai bala'in kudi bane gidan rufin asiri ne dai namai karfi daidai, motoci biyune parke atsakar gidan wata bus mai kyan gaske milk color saikuma mota sienna ash da mai gadi ke wankewa ga dukkan alamu motar maigida ne sabida yanda ya kuke yana wanketa yanabin wakan sangaya dake tashi a karamin radio daya ijiye kan plastic chair.
Bude kofar karamin flat din dake kusada babban flat din akayi, wani Matashi ne baki dogo baida jiki sosai yana sanye da jallabiya brown hannunshi rikeda makullin mota yafito, takalmi yasaka sanan yasauko daga matattakalan bakin kofarsu yadumfaro babban flat din, da sallama yabude kofa ya shiga ciki.
Babban falo dakeda girman gaske, wani Babban Magidanci ne zaune akan kujera akalla zaiyi 60years kokuma 59, kana ganinshi kaga mai gidan, bakine yanada jiki, hannunshi rikeda jarida dayake budewa yana karantawa.gefenshi kuma wata Mata ce mai kiba Hajiya Balaraba akalla zatai 40yrs tasaka wani hadadden lace tana kurban shayi a cup, saiga yara dasuke zazzaune akasan carpet suna breakfast kowanne nashan tea da bread da soyayyan egg dinshi, Mata uku ne a tsakar falon da maza biyu wanda duk kasansu daya, Amal that is 14, sai Asiya 13yrs, sai Aneela dakenan 11, Mazan kuma Muhammad dakenan 11 sai Mudasir wanda shine autan gidan 6yrs, gabaki dayan yaran kana ganinsu kaga mahaifinsu tundaga bakin fatar da jikin dan dukansu tuluka tuluka dasu very fat gwanin ban sha'awa kana ganinsu kasan sunacin lafiyayyen abinci, dukansu suna sanyeda uniform din makaranta da alamu hadda zasu danyau sunday.
Kitchen aka bude, wata black beauty Matace dan itama ba yarinya bace akalla zatai 38yrs tafito tana sanyeda doguwan rigan atampa mai kyau da akama stonework tana rikeda tray dawasu hadaddun kwanuka ke kai, hada ido tayi da wanda ya shigo dakin dukbasu luradashi ba yasa tace "this children zasusa kayi latti for your program Ya Hamad" kiran sunan shi datayi yasa duka yaran dakowama na falo yadagokai ya kallai, atare duka yaran suka gaidashi "Ya Hamad good morning" batare daya amsasu ba yakarasa shiga falon har gaban Abba yakarasa sanan yazauna agefenshi yace "ina kwana Abba" sanan yakalli matar dake gefenshi yace "Ina kwana Mum" daidai lokacin dayan matar taja coffee table zuwa gaban mijin nasu ta dauramai tray akai tace "your food is ready Daddy Hamad" jaridan ya linke tareda mikamata, karba tayi dayan matan tadauke kai Abba kuma yatura hannu a aljihun sanan yaciro wasu kudi yamikama Hamad yace "inka kaisu kabiya musu kudin makaranta" sanan yajuya yakalli matar dake gefenshi yace "me yaran nan sukeyi asama har yanzu basusan zasu makaranta bane"? dasauri tace "kumafa su tuntuni sukai break, Nanaa, Hawwa" daga chan sama aka amsa, wasu yan mata manya masu jiki guda biyune suka sauko daga stairs, yaran zaka dauka yan biyu ne dan suna kama, irin kama na jini dinnan, Nana itace Babba 26yrs take tana final year a BUK tana karanta Mass Com, sai Hawwa 24yrs tana 300level tana karanta international relation itama a Ado Bayero, Hawwa na kama da Hamad sosai, dukansu suna sanyeda lemon green hijabi na haddan, dukansu ransu abace yake dan sun tsani zuwa hadda suna uni amman suna wani zuwa hadda shikuma Babansu yanuna babu wacce ta isa tabar hadda cikinsu kodako PHD sukeyi, tashi duka yaran sukayi sukama iyayensu bye suka fice, sanan Ya Hamad din yatashi yace "bari nakaisu Abba" gyadamai kai kawai yayi dan haka Babansu yake baifiye son magana ba, sanan yawuce yafice.
Kaman ance tadaga kanta sama taga gittawan mutum dasauri an bude kofa anshige daki batare da an bari sun hada ido da Mami ba. Ahankali Mami tasauke ijiyan zuciya dudda bataga fuskanba but ko amafarki aka tadata tasan waye.
YOU ARE READING
KYAWUNA JARABTA TA
General FictionSTORY OF A GIRL THAT STRUGGLE WITH HER BEUTY, she believed that her beauty is her curse.