13

1.7K 48 1
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

           ✍️M SHAKUR

EPISODE 1️⃣3️⃣
Har dare hira suke Hajiya da Hamad, kagansu zaka dauka Hamad jikan ta ne, Hajiya wata irin mace da idan kana tareda ita you have no reason or what so ever to hate her ne, kodan sabida yaranta biyu kachal aduniya saisa takeda son mutane haka oho, danta na farko yaranshi uku dukansu Maza kuma kanana dan Mami tariga shi aure yana UK achan yake aiki sai Mami dakeda yara hudu tana aure a kano, Bayan Mami ta haifi wata tarasu, Hajiya is very very educated, lawyer ce babban gaske amman yanzu tai retire saidai she's still an advocate na Human right, batun yauba taso tadauki Du'a, akwai lokacin data kusan kulle Maman Abba wato Kaka, sabida kukan da Mami tamata ne tana rokonta yasa tahakura daga lokacin tai fushi da Mami ta shareta, saisa koda wasa bata taba taka kafarta agidan Abba ba dan batada daukan nonsense and zasuga yanda zata maida yarinyar nan, Du'a tariga tabar gidan nan kenan har abada saidai in bata raye.

Ganin Du'a na gyangyadi akan kujera yasa ta tadata. "Du'a Du'a tashi kije ki kwanta adaki" ahankali ta tashi murya chan kasa tace "saida safe Grandma" murmushi tamata tace "kiyi alwala sanan kiyi addu'a kafin ki kwanta kinji" gyadamata kai tayi sanan tawuce, dakinta tabude tashiga tamaida kofan tarufe, bayi tashiga tadauro alwala kaman yanda aka umurceta sanan tafito, fadawa kan gadon tayi tana karanto addu'an bacci sanan taja bargo ta lulluba tana rufe ido fuskan mutumin nan tagani yay flashing a idanunta  dasauri tabude idanunta tana yaye bargon tafito da kanta waje tanabin dakin da kallo, mutumin daya ciro ta daga rijiya she just saw fuskanshi, lumshe ido tayi ahankali still tana ganinshi saikuma ta girgixa kanta kaman tana kokarin koran abin dan bataso tana ganinshi, ahaka bacci yay awon gaba da ita......

Hajiya tashigo dakin da asuba ganin wutan dakin A kunne, karasawa gaban gadon tayi, zama tayi atabaki bakin gadon tana kallon fuskanta, Du'a is just different! ahankali takai hannunta ta kwashe gashin daya sauka a gefen fuskanta, shafa gefen fuskanta tayi tana kiranta ahankali. "Du'a, Du'a atashi daga bacci asuba tayi" bude idanunta tayi ganin kakanta yasa taji kunya murmushi tayi dasauri Hajiya tace "na tabbata yau zata yalwatu da ni'ima a gareni, wanan kayataccen murmushi dakika gaisheni dashi Du'a, Masha Allah jikata is very beautiful, barakallahu fiki, tashi kiyi  alwala kizo kiyi salla kifito kuyi sallama da Hamad yashirya zai tafi" gyadamata kai tayi Sanna tasauka daga gadon ahankali bathroom tashiga itakuma Hajiya tawuce tafita.

Saida tai salla sanan tafito sanye da hijabi, a falo tagansu suna zaune Hamad na rike da mug yanashan coffee, karasowa tayi ta tsugunna ahankali tace "ina kwana Grandma" "kintashi lpy Du'a ya kwanan Abuja" murmushi tayi tace "I love here Grandma, Ya Hamad good morning" "morning dama ke nake jira zantafi" yatashi bayan ya ijiye cup dinshi, Hajiya tace "sa takalmin ki kiraka yayanki" tashi tayi tasaka slippers din da Hajiya ke nuna mata sanan tabi bayan Hamad suka fita daga falon sauka suke daga matattakala kaman daga sama yace "ya akayi kika fada rijiya Du'a" dawani irin sauri takalleshi ta tsaya batare data cigaba da tafiya ba hakan yasa shima ya tsaya yana kallonta yace "answer me" murya chan kasa tace "Muhsin din Ya Nana ne yazo" dawani irin sauri cikeda mamaki yace "Muhsin"gyadamai kai tayi tabashi labarin komi iya wanda tasani, shiru yayi saikawai yay kwafa yace "muje" binshi tayi harwajen mota, sanan ya tsaya yace "be a good girl kinji, kinga yanda rayuwanki take kasancewa awajena maza so be careful kinji" gyadamai kai tayi shafa gefen fuskanta yayi yace "wuce ki koma ciki bye" waving hannu tamai tawuce shikuma yashiga mota yatada yabar gidan bayan security yabudemai gate.


Ahankali da sallama tabude falonsu tashiga, Hajiya na zaune kan kujera tanacin fruits dake cikin bowl akan cinyanta, ganin Du'a ta shigo yasa tanuna mata gefenta tace "zoki zauna anan Du'a" murmushi tayi takaraso wajen tazauna, bowl din tanuna mata tace "zaki sha fruits"? gizgiza mata kai tayi tace "na koshi" murmushi tamata tace "karki damu nariga namiki friends sunje kano ne but maybe tsakanin yau ko gobe zasu dawo zaki gansu yanmata kaman ke zadan su girma miki but I'm sure u will like them" murmushi tayi tace "thank you Grandma" murmushi tamata sanan tace "yanzu abinda ke mind dina is school, banso kishiga secondary school dan kinyi girma saidai lessons, koda wasa bazakiyi rayuwan kullen nan dakikayi agidan ubanki ba, don't worry I will think of what to do akanki, yanzu dai zansa driver na yadauke ki Razika zata biki kije saloon ama gashin nan lafiyayyen gyara ko amiki kalba ko kitso duk wanda kikeso, sanan amiki gyaran farce right" gyadamai mata kai tayi tana murmushi, Murmushi itama Hajiya tayi tace "answer da naki stop nodding head be acting like a big girl okay" murmushi tayi sosai wanan karan tace "okay Grandma" "good girl, jeki shirya kiduba wardrobe dinki akwai kaya awajen kisa daga nan" harzata gyadamata kai saida sauri tace "Tom" wuce wa sama tayi Grandma tabita da kallo harta bace mata.

Wardrobe din dakin tabude hadaddun karyane wanda mostly abaya ne, dogayen riguna kala kala daban daban, ahankali tadaura hannunta kan wani baki fitodashi tayi daga leda tana kallon rigan kaman Grandma ta aunata shiryawa tayi cikin rigan saikuma dagudu tai wajen madubi tana kallon kanta yanda taga tayi kyau ko Nana su bata taba ganin tasaka doguwan riga mai tsada nan ba, murmushi tayi tadaura dan kwalin saman tadauki hijabinta akai tasaka tafito tasauko kasa Hajiya na ganinta tace "ina gyalen abayan Du'a" dasauri tace "nadaura akai Grandma" dan dariya Hajiya tayi saikuma ta mike tace "zokiga" karasowa gabanta tayi Hajiya ta yaye hijabin dan kwalin ta warware sanan ta gyaramata parking gashin, takalli Razika dake wajen tace "he daukomata handbag a dakinta Razika" da sauri tai sama, taimata rolling gyalen saitai kaman wata balarabiya, saukowa Razika tayi da jaka mai kyau, Hajiya ya karba tabata tace "perfect oya kutafi to driver na waje yana jiranku" takalli Razika tace "stay by her side, saikun dawo, bye Du'a" juyowa Du'a tayi tamata waving hannu alamun bye sanan suka wuce suka fita sai murna take basabamba, mota suka shiga direban yajasu.

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now