14

1.9K 67 3
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

            ✍️ M SHAKUR

Free page
EPISODE 1️⃣4️⃣
Bini bini direban Hajiya dake sanye da uniform ke kallonta tamadubi, hakan yasa Razika takalleta, ganin yanda take kalle kallen hanya tana murmushin nan dake karamata wani kalan kyau nadaban yasa Razika tace "is this ur first time a Abuja Du'a?" juyowa tayi tazubama Razika mayun idanunta dakesa mutum yaji wani kwanciyan hankali harzata gyadamata kai ta tuna maganan Hajiya hakan yasa tace "eh" murmushi sosai Razika tayi tace "Abuja ai nada kyau, nima Hajiya tadaukoni daga kauyen mu takawo ni nan, sanan akwai lesson teacher dake zuwa mana karatu duk asabar da lahadi, Hajiya nason yara, kinga tunda nake a Abuja bantaba ganin yarinya mai kyau kaman keba" dan murmushi tayi saikuma tadauke kanta tamaidashi kan titi tana kallon motoci dan kunya takeji taji ance tanada kyau bamataso adinga cemata haka, ahankali tace "thank you" "yauwa munkawo" Razika tafadi ganin driver yay kwana yashiga wani babban Plaza, parking yayi hakan yasa Razika tace "sauka muje" bude kofa tayi ahankali tafito tana kallon wajen yanda akwai mutane kowa na shiga da fita abinshi, ko yanda takebin mutanen datake gani da kallo ne yasa taga suna kallonta itama oho dasauri tarike hannun Razika gam data fito tace  "muje" tana rikeda hannun Razika suka wuce suka shiga wani hadadden saloon dake nan first floor, ma'aikatan suka taso suna gaidasu kafin Razika tamusu bayanin me za'amata nan aka shiga yi mata gyaran gashin.

"inje insiyomana ice cream a wanchan shagon Du'a" ta tambayi Du'a da ake wankema gashi, murya chan kasa tace "eh" tashi Razika tayi tafice daga saloon din daidai angama wanke ma Du'a tulin gashin aka nannade mata gashin da towel matar tace "tashi muje dryer" tashi tsaye tayi tawuce taje tazauna ana sliding kofan saloon din aka shigo, juyowa tayida sauri tazaci Razika ce, wani Alhaji tagani yaci babban riga milk na shadda dake kyalli da akalla zaikai 60yrs baki dashi mai kyau ga gemu kadan tareda wata mata kana ganinta kaga yar duniya ga hujin hanci akan hancinta guda uku tana rikeda jaka tana taunan cingum tana sanye dawasu kaya dabasu da maraba da babu ajikinta, suna shigowa masu aikin suka taresu. "welcome Alhaji, welcome Hajiya" gyadamusu kai yayi yanabin matan saloon din da kallo one by one, zama matar dake taredashi tayi kan kujera tawani kamo hannunshi ganin ba ita yake kalloba da sauri yajuyo yakalleta jinta kamamai hannu, kashemaai idanu tayi tace "Baby kagaya musu style din da za'a min" washe baki yayi yace "kai wlh mata kun iya rigima yanzu style ne sai an tambayani, ninasan kan style ne" kallon yar aikin dake gabansu yayi wacce ke jiran bayanin su kafin sufara aiki yadan lashe baki sanan yace "okay bari muga" juyawa yayi yacigaba da kallon yan shagon, Du'a yanuna da akema rolling gashinta a roller za'a sata a dryer yace "how about that fine baby style, Zinariya kinason style din"? yamata tambayan still yana kallon Du'a da akema gyaran gashi wacce ko kallonsu ma batayiba madubi take kallo tana kallon abinda ake mata akai wanda is new to her tabama kofa baya, ganin inda yake kallo yasa Zinariya tace "katafi meeting din dakake dashi Sweet, idan kagama saika biyo kadaukeni" tai maganan tana shafamai hannunshi still datake rikedashi, dan juyowa yayi yakalleta kaman wanda ya manta da abinda ke gabanshi yace "ohh meeting dinan, to,to bari inje, saina dawo" yay maganan yana juyawa bude kofan yayi harzai fita saikuma yadawo dasauri yawuce wajen kujeran Du'a ya tsaya tagaban wajen yana facing nata directly yakare madubin datake kallo yana murmushi yana kallonta kaman yanda takedan kallonshi atsorace  yace "nace nawane kudin gyaran kan Zinariya"? Ya tambayi mai gyaran kan Du'a yana kallon Du'a kaman wani tsohon maye wanda baitaba ganin mace ba sai akan Du'a, Mai gyaran gashin Du'a dake kallonshi ne itama cikeda girmamawa  tace "all payments are done to Christy Alhaji gatachan the cashier" tanunamai wacce ketare da Zinariyan shi data daure fuska tana kallonshi, yana kallon Du'a still yace "in that case ba matsala, by the way young lady ur hair is beautiful" yama Du'a magana yana wani kalan kallonta, sai alokacin Du'a tadago kanta ta kallai da kyau wanan sa''an Abban tabe hakan yasa tamai shiru, wani irin hadiye yawu yayi yana lashe baki murya chan kasa yace "bala'i Allah yayi mace anan" rasa yanda zaiyi yasa yawuce yawayance yana kallon Zinariya yace "natafi Baby" yawuce yafita ya shiga hadaddiyar jeep din da aka kawosu ciki daidai lokacin Razika na shigowa rikeda ice cream guda biyu tazo inda Du'a take tamika mata tace "gashi" hannu tasa takarba tana murmushi tace "thank u" gajeren tsaki Zinariya tasaki tadauke idanunta dagakan Du'a kishi nawani irin turnuketa kaman taje tashake yarinyar takeji tadai daure dantafi karfin karaman yarinya haka.
*********

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now