28

1.9K 59 1
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

          ✍️ M SHAKUR

This book is 500 nakusan gama free pages, you can join the group by paying 500 into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na wa.me/+2347012181461  sainai adding naki to the group.

free page
EPISODE 2️⃣8️⃣

Zubomai shayin tayi a mug dakanta sanan tadawo kusada shi kafanshi tadauka tace "sit up my friend" dan murmushi yamata yatashi yazauna tareda mika hannu yakarbi shayin yace "thanks Grandma, you are the best you know that right" murmushi tamai  tace "nasanar da Ammin ka kana nan, ya TV show dakayi angama lpy"? yatsine fuska yayi yakurbi shayin kadan yacire daga baki yace "it was stressful but Alhamdulillah nagama" dan dariya tayi tace "kai Asad, yanzu dai mezan dafamaka yau kaci ka koshi" ahankali yace "rice and beans nakeso Grandma" "kaida shinkafa da wake Asad shikenan zan dafamaka" murmushi yamata yace "Grandma bakiyi fushi dani ba tunda nadawo banzo ba" hararanshi tayi tace "ja'iri ashe kasan kayi laifi" dariya kadan yayi yana kurban tea, tace "ai nayi fushi dakai but Sharif nata gayamin how busy u were saisa andena fushin, yanzu daka gama bagaka kazo ba, ai ba'a raba jika da kakanshi" hira suka cigaba day haryana bata labarin aikinshi sosai taji dadi yanda yasake dudda batamai maganan abinda yasameshi jiya ba, saida yagama tass sanan ya ijiye cup din yace "Grandma bari naje na shirya natafi office, I have huge work awajen ma" tashi tayi tace "tafi Asad, Allah yataimaka kaji, nidai kadingayi kana neman mata inaso naga jikana kafin namutu" yatsine fuska yayi irin ewww dinan bayamason maganan sanan yawuce yafita daga falon yatafi itakuma Grandma takoma tai zamanta dan akwai shirin dazata kalla.
**

Zaunar daita Razika tayi akan gado sanan takoma tarufo kofa dagudu tanadan zaro idanu tace "naga mutumin jiya a falo Du'a biyomu yayi ne" cikin tsoro muryanta dabai gama washewaba sabida yanda tai kuka tace "nima shina gani bansan lokacin da kofi yafadi daga hannuna ba yanzu idan yafadi ma Grandma Yaya zanyi? Wai waye shi? Ya akayi yasan Grandma sosai har yafito daga lungun flawas din falon saman nan eh" hannu Razika tabude itama alamun oho cikeda damuwa tace "oho amman kaman Shemau tasanshi naga ta gaidashi da sauri tana ganinshi  kinsan ita tadade tana aiki agidan nan ni ba'a dade da kawoni ba" shiru Du'a tayi har lokacin gabanta faduwa yake, zama kusada ita Razika tayi murmushi tayi takalli Du'a tace "sonshi kike ko Du'a"? wani irin kwalalo idanu waje tayi tace "so kuma" gyadamata kai Razika tayi tace "eh naga yanda kike ta kallonshi jiya ana koranki kinki tafiya kinata cemai thank you for saving my life keda bakima sanshi ba, sonshi kike ko? Yanada kyau sosai wlh gashi dan gayu gashi mai kudi har ana nunashi a TV, sonshi kike"? Girgixamata kai Du'a tayi tace "a'a kawai nasanshi ne tun a kano, shine yataba cironi daga rijiya saisa dana ganshi nace sainaje namai godiya" gyadakai Razika tayi da gamsuwa tace "to Allah sa shiyace yana sonki wlh danaji dadi" dan daure fuska tayi tace "ni banson maganan nan"  yatsun kafarta dahar jan dasukayi yasoma washewa takalla tace "bazakije office ba? naga yatsun harsun washe kinga yau Monday fashi ranan Monday is a serious offense" Yatsun itama takalla tace "yadena zafi, tayani zabomin kaya kinga banda lafiya saina shirya natafi" hannu Razika tasa ta dungure mata goshi tace "kewai mai wayau ko" tai maganan tana zuwa gaban wardrobe dinta wani ja da bakin abaya taciro mata sabo fill tana kallonshi tace "wowwww abayan nan yay bala'in kyau, Hajiya tasai miki"? murmushi tayi tana girgixa kai tace "Aneesa tazaban min ranan damukaje shopping yay kyau" warware rigan Razika tayi tace "wlh kam yayi kyau kai yayi bala'in kyau ma, oya tashi kizo ki shirya" tashi tayi tana kallon yatsun nata jin sundena mata zafi, wucewa Razika tayi tafice daga dakin tace "saikin fito" tom Du'a ta amsata tana kokarin cire rigan dake jikinta sanan ta ijiye ta shirya cikin rigan kafin tazo gaban madubi tatsaya tana kallon kanta for the first time yau taga kyanta da ake fadi ja da bakin color ya bala'in mata kyau, zama tayi tana daukan ribbon parking kitsonta tayi a tsakiyan kan yay kaman acucu gashin goshinta sun wani irin bala'in kwanta, sanan tai rolling gyalen abayan, man baki talakata ta shafa a lips dinta dayay wani pink sanan ta tashi tana hada jakanta tadau pad tasaka dakomi da Grandma takoyamata sanan tazura wani flat takalmi mai budadden sama daya bayyana fararen cute kumbunan kafanta, ahankali tasa hannu tabude kofarta tana lekawa gabanta nafaduwa ganin babu kowa yasa takarasa karasawa wajen bene tashiga tafiya ahankali, Grandma kadai tagani zaune tana fere apple dawani karamin wuka, dago kanta tayi jin sahun tafiyanta, kasa daurewa tayi sabida yanda tai kyau tace "Masha Allah tubarkalla Du'a kinyi kyau sosai har kafan ya warke ne"? murmushi tayi tana zama kusada ita tana gyadamata kai, Hajiya tace "to dama banda shegen shagwaba naki ruwan lipton wani konewan kirki ne, kedai kawai rakin ki yay yawa, tashi ki tafi aiki yau Monday aka ciki taran latti baruwana wanan da Ogan ku yadawo ai kunbani" dan zaro idanunta tayi sai yanzu ma ta tuna Sharif yacemata this Monday Ogan su zaiyi resuming office, zumbur tamike tace "bye Grandma" murmushi Grandma tayi tabita da kallo sabida yanda yarinyar tai kyau tace "ayi addu'an fita daga gida Allah tsare" tsalle tayi kaman yar yarinya tace "tom" "kidena tsalle" Grandma tafadi tana murmushi ganin yarintarta.

Motan Grandma tashiga zama tayi driver yajata sai alokacin ma ta tuna batai breakfast ba, har campanin yakaita, yau kawai taji tana having wani irin wired feeling kaman tace sujuya su koma gida kartazo aikin.

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now