21

1.9K 59 5
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

            ✍️ M SHAKUR

free page
EPISODE 2️⃣1️⃣

Sosai takebin office din da kallo kaman wacce bata taba ganin office ba arayuwanta, ga katoton TV dake makale a bangon office din, gawani camera Ata sama amakalle shima dabata san koname ba, ahaka tana zaune ita kadai har lokacin azahar tayi, knocking office dinta akayi saikuma aka budo kofan, Sharif ne murmushi lullube kan fuskanshi yana kallonta batare daya shigo cikin office dinba, dan murmushi tasakinmai itama dan wani irin kunyanshi takeji ganin yanada kirki sosai, ahankali yace "is time for zuhur u wanna join me?" Gyadamai kai tayi da sauri dan tuntuni takejin fitsari dama amman kunyan tafita ita kadai takeji taje, tashi tayi ahankali tafito duk yana kallon ta sanan taja kofan office din suka wuce tare har mosque yanuna mata side din mata ta tafi, wucewa tayi bayinsu sai kallonta matan dake wajen suke itadai babu wanda take cema uppan besides ma kanta akasa dan kunyan yanda suke kallonta takeji, fitsari tayi tayo alwala sanan tashigo masallacin ganin cupboard dake cike da hijabai yasa tadauki hijabi tasaka tai salla abinta, tana idarwa ta zauna tana kokarin rolling gyalenta babu yanda batayiba takasa hakan yasa takama gyalen ta wajen wuyanta gamgam tamike tafito, jigine da bango masallacin taga Sharif yay folding hannunshi akirji da alamu ita yake jira, ganinta yasa ya yunkura yataho inda take yana kallonta yace "maiya sami gyalen"? Ahankali tace "ban iya yanda Grandma tamini ba" Dan murmushi yayi yace "then u have to learn dagayau, let's go have lunch" yay maganan yana hawa stairs yay hanyar canteen dinsu tana biyeda shi, shiga sukayi ga few employees dinsu dake wajen suna cin abinci cikeda girmamawa suka shiga gaidashi amsasu yayi batare daya kallesu ba sanan yaja kujera yanuna mata alamun ta zauna zama tayi ahankali tana kallonshi ganin yanda yake wani kulada ita kaman yar kanwarshi, shima zama yayi yakalli yarinyar datazo cikeda girmamawa tace "mezan kawo muku sir" batare daya kalleta ba yace "I want pasta da salad, mezakici Du'a" yay maganan ahankali yana kallonta, kallon yarinyar tayi sanan tace "jallof rice" juyawa yarinyar tayi ta tafi itakuma tasauke kanta kasa tana wasa da yatsunta Sharif sai kallonta yake kaman yamata magana saikuma yay shiru shima ahaka har aka kawo musu abincin, cin abincin shi yafara hakan yasa yace "bazaki ci ba" Dan dagokai tayi ta kalleshi ahankali tadau spoon tafara cin abincin, bini bini yake satan kallonta, ta bala'in yima kyau, komi nata daban ne, harya gamacin abincin shi batai rabin nata ba hakan yasa yacigaba da jiranta, kadan takara akai ta ture hakan yasa yace "u okay" gyadamai kai tayi tasha ruwa sanan ta tashi alamun su tafi tafiya sukayi har office yasake rakata sanan yawuce nashi office din, wuraren 4 tana zaune a office dinta telephone din wajen yahau kara dasauri ta dauka, muryan wani security taji.

"Miss Du'a your driver is here to pick u up" dawani irin sauri ta tashi tana hada yan tarkacenta ajaka ta kosa ta ganta agida sanan tafito tana tafiya ahankali tasauka kasa zatai hanyar kofa taji magana a bayanta. "so you're living without saying goodbye" dawani irin sauri tajuyo ganin Sharif ne yana rikeda waya a kunnenshi da alamun ma waya yake but still saida yamata magana yasa adan kunyace tamai waving hannunta tace "bye" gyadamata kai yayi yacigaba da magana. "yes I can hear u Asad" waje tafita ta shiga motan Grandma dinta driver yatafi da ita, Allah Allah take takai gida, suna kaiwa gida tafito daga motan dasauri harda dan gudun ta tai falonsu tana budewa taga su Rahima Mariya da Aneesa duk sunci gayu sosai suna zaune afalon Hajiya atare sukace. "surprise" suka tashi suna rungumeta, wani irin murmushi tayi ta kallesu tace "yaushe kukazo sorry" dasauri Aneesa tace "bakomi Hajiya da Ammi daman sun gayamana kinji aiki, jekiyi wanka kizo kici abinci mutafi" gyadama musu kai tayi takalli Grandma dinta dake zaune tana kallonsu tana murmushi, wajenta taje ahankali tace "Grandma ina yini" fuskanta tashafa tace "Du'a dina sannu da zuwa, yi sauri kije ki shirya kunga tuntuni su Aneesa ke jiranki" wucewa sama tayi da saurinta dakinta ta shiga, wanka tayo tafito, tunawa da abinda Grandma tafadi mata yasa tasake dauko wata gown wanan is simple dan ba designers bane irin na dazu data sakaba milk color, saka shi tayi sanan tadauki mayafinshi ta feffesa turare tafito kasa, duk juyowa sukayi suna kallonta Aneesa tace "mena rike dankwali a hannu kiyafa mana" karasowa falon tayi tace "ban iya bane grandma zatamin" tabama grandma dan kwalin, dasauri Mari tace "Hajiya bari mu mata sabida ta iya" tana maganan ta karbi veil din daga hannun Hajiya sanan ta wani irin yafama Du'a akai gaban kanta daya cika da kwantaccen gashi yawani fito, Rahima tace "wow wlh kinyi kyau Du'a mutafi to, Aneesa ina kudinta da Ya Sharif yace mubata" dasauri Aneesa tashiga bude handbag dinta wani kudi taciro a envelope sanan tamikama Du'a din tace "ga kudinki, tundazu dasafe kafin yatafi office yabamu mubaki" dasauri Du'a takalli Hajiya danharga Allah batasan mezatayi ba, murmushi Hajiya tayi tace "karba Allah ne ya ciyar dake kafin aci kudin Sharif saidai idan Allah ya tsaga da rabonki ne" kwashewa da dariya yaran dukansu sukayi sukace "wlh kuwa Hajiya Ya Sharif kare bayacin kashinshi, karba muje" Ahankali tasa hannu takarba tace "thank u" sanan tasa ajaka, sallama sukama Hajiya sukai tafi direba ya kwashe su, sosai sukema Du'a hira a mota ita abin mamaki yake bata yanda suke sonta daga ganinta jiya dan har labarin samarin su suke bata, Aneesa data zauna agaban mota ne tajuyo ta leko takalli Du'a tace "ke baki bamu labarin saurayinki ba" Dan zaro idanu tayi tanuna kanta tace "ni"? dasauri Mariya dake gefenta tadan bugi kafadanta tace "common on don't be shy, tell us about the lucky guy" dan murmushi tayi saikuma tadauke kai dan tambayan tabata kunya ahankali tace "ni banda saurayi ko daya wlh" wani irin bude baki sukayi suna kallonta sabida mamaki, Rahima dake gefen Mariya tace "Du'a wasa kike ko" girgixa kai tayi tace "wlh ba wasa nake ba" shiru duk sukayi yanda yarinyar nan keda kyau ace bata da saurayi basu wani karyata ta sosai ba sabida sunga ko wayama batada shi, share maganan sukayi suka shiga wata hiran har sukakai mango dazasu, nan Du'a taga yanda ake shopping ita bama tasan mezata dauka ba hakan yasa kome suka dauka itama saisun daukan mata anata cart din, tundaga kan Bra da tuni suka gwadata suka shiga zakulo mata sizes dinta zuwa pants, pads kayan makeup, duk suna tura cart dinsu kowa na diban abinda akeso TV super market din dake makale asama na aiki Channels television news inda ake program REINVENTING THE NIGERIAN YOUTH....

Suna tsaye bangaren English wears Rahima ta amshi tape tana kokarin ana waist din Du'a dan asan size din jeans dinta itama ta dauka kaman daga sama wani kyakkyawan eloquent voice yadaki dodon kunnuwan Du'a da hakanan taji kaman tasan muryan, dawani irin sauri tadaga kanta sama takalli TV, chak ta tsaya ko motsi kirki tasaka, idanunta ne suka sauka kan fuskan da kusan kullum saitaga fuskan, wanda yacetota daga rijiya, yana sanye cikin wasu classic suit dark blue, ga necktie awuyanshi, yana zaune kan wata hadaddiyar kujera yayi crossing legs dinshi in a stylish way, yadaura hannunshi biyu kan cinyanshi wrist dinshi na daure da agogon Rolex, idanunshi fari kalll wanan karan babu bakin glasses akan su, lips dinshi sunyi wani masifaffen pink kaman ya shafa janbaki pin akai, gashin kanshi dake da yawa sunyi wani kalan extraordinary coils, yana magana da english da accent dinshi na bristish, kaman acikin mafarki taji ana Du'a, Du'a, Du'a, tabatan da akayi yasa tai firgigit tafarka ta kallesu da sauri dan sai alokacin ma tasan ashe tayi nizan tunani ne, neck dinta Rahima takai hannunta ta taba tace "baki da lafiya ne? Tunanin me kike haka kin tsare TV da ido eh harmun gama siyan kaya" binsu tayida kallo ganin yanda suke kallonta kaman sun damu yasa takakalo murmushi tace "tunanin abubuwan dazan saya fa nake" murmushi dukansu suka mata, Rahima tace "mungama da wanan shop din next stop is abaya store, mutafi mubiya mufice yamma nayi" gyadamusu kai tayi tabisu zuwa wajen cashier tana kara waigowa tana satan kallon TV da Asad har lokacin ke magana, kowa kudinshi yabiya sanan aka musu parking kayan a leda sanan suka wuce suka fita still saida takara waigowa takalli TV, sanan suka fice, ranan basu suka dawo gida ba sai 8 nadare kasa bude kayan tayi salla ta lallaba tayi sai bacci tashinta grandma tayi saida ta tasa ta agaba taci abinci sanan tabarta takara komawa bacci da tagaji bata saba fita ko wahala hakaba, all abinda tasani is wanka kwanciya da cin abinci shikenan saisa tai bacci awahale.

DAN MAGANA DANI M SHAKUR CHAT ME UP BY CLICKING ON THIS LINK wa.me/+2347012181461

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now