💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️M SHAKUR
Free page
EPISODE 1️⃣ 9️⃣
Gyadamai kai Ammi tayi cikeda jin dadi tace "Allah maka albarka Asad dina" murmushi yayi yace "Ameen Ammi, but who is the girl"? kaman bazata fadamai ba tace "jikan Hajiya ce, she's 21" yatsine fuska yayi yace "Ammi ni all those children banson raini fa" hararanshi Ammi tayi tace "to Uncle Asad, ya za'ayi ma tamaka raini, jikan Hajiya ai she's just like ur sister su Mariya idan tayi badaidai ba ka gyaramata, kuma batada raini ko kadan that I know" yatsine fuska yayi irin baimasan maganan nan ahankali yace "Ammi I want coffee" tashi Ammi tayi tace "bari nahado ma tunda yaran nan duka sun gudu gidan Hajiya sun barni nikadai" kitchen tawuce tashiga....Yau idan kaga bakin Du'a har kunne, har Rahima dake feeling tagirme su bazata iya zama friend din Du'a ba jitayi tanason Du'a sabida yarinyar akwai kyau dudda sun lura duk sun fita wayewa basu wani damuba kafin kice me cika falon Hajiya sukayi da hayaniya, suka tasa Hajiya agaba sai tabama Du'a itama kudin shopping gobe duk suka tafi tare, itama 200k tadauko tabata daman tanason takai yarinyar shopping but bata sami lokaci ba waya ma tace "gobe idan zata dawo zata taho mata da waya" duk suna cikin uban hanayinan Sharif yay sallama, dasauri Rahima tace "kinga Du'a we have two brothers, wicked and harsh, yanzu zakiga weekend one din shike mana murmushi da wasa amman shine ba'acin kwandalan shi" Hajiya dake kallonsu tace "Au haka kikace Sharif shigo kaji yanda kannenka kebata maka suna" turo kofan yayi yashigo hakan yasa Du'a itama tadaga kanta dantaga wanda ake batawa, wani kyakkyawan gayene dogo mai tsayi gashinan fari fat kaman su Rahima, tana ganinshi taga kamanninshi da Rahima da Mariya, baida kiba ko kadan, sai uban kyau ga sajenshi baki sidik dasuke nan akwance, gashin baida tarin gashi irin na Asad amman akwai gashi kadan da lowcut yakeyi ko kadan bata ganeshi ba hakan yasa kawai ta tsaya tana kallonshi daga inda take zaune kusada Hajiya dasu Rahima.
Dauke kai yayi daga kallon Du'a ganin kannenshi da kowa na wajen yace "Hajiya yanzu har gidanki suka tattaro sukazo suna gulmana yaran nan, aiko wlh zan baku kashi" yay maganan yana dunfaro su, ihu sukayi duk suka tashi suka kankame Hajiya Du'a ko sai dariya dasauri Hajiya tace "jama'a na shiga uku, wani yamikomin wayata yaga wlh Ammin ku zan kira tazo ta kwashi yaranta kutafi gida tunda neman kasheni kuke kai kuma wlh bazaka taba yaran nan agidan nan na ko kazo kazauna kokuma kawice katafi idan mugunta kazo yi nagayamaka kukuma ku dagani" Da sauri suka dagata shikuma yazo gefenta yazauna kusa da ita yay folding hannu yace "Hajiya jikanki batada kunya ita batasan yayanta yazo tagaidani ba wlh idan tace zata biyema marasa kunyan yaran nan nida ita bazamu shirya ba" yay maganan yana hararan Du'a, sosai Du'a ke murmushi ganin yanda Sharif keda ban dariya, ahankali cikin yar muryanta tace "Ya Sharif ina yini" hararanta yayi yace "lpy lau" Mariya dake gefenta tace "Ya Sharif kaga harda ita zamuje shopping din gobe tunda Ya Asad yabamu namu kai kabata nata ai itama kanwarka ne yanzu" dasauri Hajiya tace "ohh ni yasu Mari ke Mariya yaushe kika dawo scammer eh, Sharif yaran nan damfaran ka zasuyi ba yanzun nan nabama Du'a nata 200k dinba" dan sosakai Sharif yayi yace "Hajiya ni bansan ko yaran nan basuso nai aure bane, kudin aure fa nake tarawa" saikuma ya kalli Du'a yace "nasan sun riga sunce miki banda kirki I will prove them wrong, kinga ban shigo da kudi ba, but zanbama Mari gobe tabaki okay" gyadamai kai tayi tana kallonshi irin kaman bata yarda ba dinan dan ita Grandma tariga tabata kudin ta, kaman Hajiya ta lurada hakan ne yasa tace "baki cema Yayanki kingode ba" murmushi tayi ahankali tace "nagode Ya Sharif" nan fa dakin ya kachame da hira, shi Sharif baida girman kai yana shiga kannenshi yayi hira dasu sosai iyayensu dasuka rasu yasa yafara haka dan he is all dasuke dashi couple with the fact Asad baida wasa, saisa yake hira dasu yasasu dariya yasasu bakin ciki komi ba, daga karshema zamewa Du'a tayi tai bacci shoulder ta nakan jikin Rahima, sai wuraren 11 Sharif ya tarkatasu sukama Hajiya sallama suka tafi kaman karsu tafi, itakuma ta tada Du'a tawuce taje ta kwanta.
YOU ARE READING
KYAWUNA JARABTA TA
General FictionSTORY OF A GIRL THAT STRUGGLE WITH HER BEUTY, she believed that her beauty is her curse.