25

2K 53 5
                                    

💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫

Chat me up directly by clicking on this link wa.me/+2347012181461
      ✍️ M SHAKUR

Free page
EPISODE 2️⃣5️⃣
Ko karasa maganan baiyiba katon bodyguard dinshi yataho hakan yasa Razika tawani ja hannun Du'a da duka karfinta, fashewa da kuka sosai Du'a tayi Guard din nabinsu Razika najanta da sauri tana kuka mutanen wajen namata dariya suka fita daga wajen sukai hanyar staircase suka farabi, sai alokacin bodyguard din ya tsaya ata gaban stairs din yace "idan kuka dawo cikin wajen nan saina bindigeku" dasauri Razika kejanta suna sauka sai alokacin tasan ashe kafafunta sun gaji, sosai take kuka Razika tace "waike bakida wayaune Du'a saikace wata karaman yarinya, jibi yanda kikasa akai embarrassing namu" da kyar ta iya karasa sauka daga stairs din kaman kafafunta zasu cire daga cinyanta suka fito waje, wani Alhaji ne suka gani tsaye awajen yana gyara zaman malum malum dinshi yana kallonsu, hannu Du'a tasa tai wiping hawayen dake kan fuskanta tass, wani irin murmushi mutumin yasakin mata yace "common pretty girls basa kuka, daina kuka" dasauri Razika tacigaba da janta da sauri dan magrib yayi, da dan gudinshi ko kunyan mutanen dake wuce su baiyiba yasha gabansu yakalli Razika yace "I guess ke kawarta ce ko dan Allah sakin mata hannu kibani minti daya nai magana da ita" yakalli Du'a data dauke kai yace "Pretty dance mata tasakin mata hannu" cigaba da tafita sukayi yana binsu har sukakai mota, bude motan Razika tayi Du'a tafara sawa aciki sanan tashiga itama taja kofa mutumin na bubbuga kofa takalli driver Hajiya tace "muje wanan mutumin na binmu" kunna motar yayi yaja shikuma mutumin yadaga hannunshi sama kaman mai kiran mutane saiga wata hadaddiyar jeep yazo baya yabude yashiga yace "mubi wanchan motan Auwallu amman ahankali zamubi motan sabida karsu sani suboye inaso nasan mahaifin yarinyar nan"   yana biyedasu har suka shigo estate dinsu, nesa dasu yasa aka kashe motan ya gyara zama yana kallonsu, gate aka bude musu suka shiga ciki sanan aka maida gate din aka rufe, dasauri yace "tada motan kaga Auwallu" tasa motar driver shi yayi zuwa gidan da Du'a ta shiga, parking yayi akofar gidan sanan yabude bayan motan yafito yana gyara zaman malum malum yana leken gefen gate din kaman wanda yasami matsalan tabin hankali, ahankali yakai hannunshi zaiyi knocking gate din aka bude gate din aka fito, Sharif ne yafito daure da alwala dan masallaci zaije sallan isha'i, tsayawa yayi yabi mutumin da kallo, dasauri mutumin  ya shiga leka gidan kaman zaiga Du'a ta gefen Sharif, ganin haka yasa Sharif yarufo gate din ahankali yace "lpy" wani irin murmushi Alhaji yayi tareda shafa kanshi saikuma yace "wai mugaisa wlh duk na rude ne naga abinda raina ke matukar so" yamikama Sharif hannu, kin bashi hannu Sharif yayi yana kallonshi still yace "lpy maikazo nema? Kokuma nace wakake nema?" sake sosa meya Alhajin yayi yace "wlh naje ba wata yarinya yar fara haka nabiyo naga tashiga gidan nan, inataso namata magana tun achan amman dayan datake tareda ita taja hannunta tahanata magana dani wlh, dan Allah ko zan iya ganinta kokuma zaka hadani da mahaifinku dan naga kaman kai yayanta ne naganka fari kaman ita dudda tafika fari da kyau" yay maganan yana lashe baki yace "Allah yayi mace awurin nan wlh" wani irin daure fuska Sharif yayi ganin tsohon banza ne, hakan yasa yace "sunana Sharif, kuma yarinyar dakake magana matata ce, ka kama girmanka ka tattara inaka inaka kabarmin kofar gida kafin nahadaka da hukuma" wani irin kwalalo idanu yayi saikuma yadaura hannu akan saman bakinshi yace "assha ai bansan matarka bace, bansan matan aure bace wlh nagayamaka bata kulani ba inda ace takulani tagayamin tanada aure daban biyota ba wlh, amin afuwa nabarka lafiya" yajuya yashiga mota dasauri sukabar wajen wani irin tsaki Sharif yaja yabi motan da kallo yace "tsohon banza kawai" saida yaga su fita daga estate din sanan yawuce yatafi masallaci.

Sharif na tsakar gida yana alwala yaga shigowansu itada Razika tana goge fuskanta da gyalen abayan dake kanta idanunta sunyi ja sosai, bama su luradashi ba suka wuce ciki, falo suka shiga kallo daya Hajiya dake zaune akan kujera tana magana awaya tamata tagano wani abu dasauri tacire wayan daga kunnenta tace "zan kiraki Hajara" katse wayan tayi takalli Du'a da Razikan da duk suke atsaye sun kasa karasowa gani suke kaman tana ganinsu zata gane abinda yafaru, yunkurowa tayi tana kallonta still tace "why did you cry Du'a? Maiya sameki?" Dan zaro ido tayi this is the first time datasan tama Grandma dinta laifi sosai, Grandma data taimaketa tabata freedom shine daga fara fita ta hartaje hotel ita maiyama kaita taje, duk ta tsaya tana tunanin nan zuciyanta fall da tsoro batare databama Grandma dinta amsaba, juyakai Grandma tayi takalli Razika tace "maiya sameta take kuka"? Baki Razika tabude zatai maganan da sauri ta tattaro duka karfinta ta tari numfashin Razika ahankali tace "Grandma hannun matan zafi sosai kuma gashi tadade kaina ke ciwo" sosai Grandma ke kallonta, ga idanun nan nata sundan kumbura alamun tasha kukan tace "to dan kanki na ciwon kitso sai kiyita kuka banace kidena all this abubuwan ba keba yarinya bace"? Gyadama Grandma kai tayi hawaye nasake taruwa a idanunta tace "sorry" ganin tana neman sake kuka yasa taidan murmushi dan she looks damn cute tace "zonaga kitson" tahowa tayi ahankali gabanta nafaduwa sosai ko kadan bataso tama Grandma dinta karya ba, zama tayi gefenta, Grandma tabude kan tana kallon kalaban dayay bala'in kyau tace "wow daman abu mai kyau yafi bada wahala, kinga yanda yay kyau kuwa, wow oya jekiyi salla kiyi wanka kizo nabaki abinci da paracetamol kisha" gyadamata kai tayi ta tashi ahankali sama, Grandma takalli Razika dake tsaye itama tace "sannu kinji Razika, Du'a dukta wahalar dake, jeki daki kiyi salla kihuta" ahankali tace "to" tawuce, tashi tayi itama dayake hijabinta nakusada ita dan tariga tai salla yasa ta tashi ta shimfida dadduma danyin salla.

KYAWUNA JARABTA TA Where stories live. Discover now