SHAFI NA HUDU

828 16 1
                                    

*ƊABI'AR ZUCIYA*
*Free page*
04

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar


      A daren ranar idan tace tayi isashen bacci to tayi qarya,haka ta dinga baccin rabi da rabi,abunda ya faru ne kawai yake dawo mata daya bayan daya,ta fuskanci kaf rayuwarsu qalubale ne a cikinta kala kala,tako wacce fuska akwai kalar jarrabawar dake fuskantosu,ko sai yaushe al'amura zasu daidaitan musu kamar kowanne mutum?,amsar data kasa lalubowa kenan,har xuwa wayewar gari,sanda ta tsinci muryar ummansun saman kanta tana kiran sunanta.

       A kasalance ta miqe,cikin yanayin barcin da bai ishi mutum ba,ta zauna sosai tana murza idanu,tana kuma duban umman nasu,ganinta sanye da hijabin da takan sanya idan zata je wata unguwar
"Ki tashi hakanan.....matar malam ta aiko kije kiyi mata kitso,nizan fita,zanje dubo inna"
"Inna kuma ummanmu?" Ta tambaya cikin mamaki tana duban fuskarta,don ta sani cewa ita dinma aiba isashshiyar lafita gareta ba,ciwo ne a qafarta wanda kullum yake ci gaba,take kuma neman kudin maganin da zatayi,saboda lokitocin cikin gari da suka ja kunnenta kan ta gaggauta yin maganinsa,yin jinkiri ko wasa dashi zai iya haifar mata da komai,ciki harda rasa qafar tata ma gaba daya,to amma ko a mafarki,koda wasa basu taba ganin gilmawar inna cikin gidan da sunan tazo dubata ba,hasalima a kafatanin rayuwarsu xasu iya lissafa sau nawa suka taba ganinta tazo gidan nasu,kallonta umman tayi sosai tana karantar yanayin fuskarta
"Eh ita,ashe kwana biyu bata jin dadi,sai dazu Allah ya kawo yaron nan salisu na kusa dasu yake gayamin" sosai ran kaltum din ya baci,wato kwata kwata mahaifiyar tasu ma bata da darajar da za'a aiko a shaida mata bata da lafiya,sabida bata da abun duniyar da zata bata,tana da yaqinin inda rahama ko zaliha ce koda babu aike innar zata je da jan gindi da kanta ta sanar musu,qoqarin miqewa kawai kaltum tasoma yi,don ba zata bar umman tasu ta tafi ita kadai ba,gwara suje tare,duk da wanzuwarsu a wajen babu abinda xai hana na daga abinda inna tayi niyyar aikatawa akan umman tasu,amma dai biyu tafi daya
"Umma don Allah jirani ja watsa ruwa kawai muje tare"
"A'ah....to kitson fa da ake jiranki kiyi?" Umman ta fada tana binta da kallo,a lokacin har takai bakin qofa
"Zan aika habiba ta basu haquri,idan muka dawo naje nayi musu" saita qara wuta ta fita da sauri don ma kada umman ta sake tsaidata.

ZAFAFA BIYAR NEW YEARWhere stories live. Discover now