PAGE 2

510 3 0
                                    

*_Typing📲_*


             *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_*

                *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

_ZAFAFA BIYAR 2K22_

*________________________________*

*Chapter two*

.........Idanu sosai na ware domin ƙare masa kallo, sai dai isowar mashinan power bike guda biyar cikin layin ya rabamin hankali biyu, tuni makaho shima ya yaye kayan dattin jikinsa ya fito a lafiyayyensa. Cikin girmamawa ɗaya daga cikin wanda suke a saman mashinan ya faka nasa gabansa, ya sakko tare da sauke jakkar bayansa dake goye ya ciro takalma masu azabar ƙyau da sauran kayan bada kariya daga haɗari na mashin ɗin.
       Cikin sauri wani ma ya sakko a nasa mashin ɗin ya warware kujera ya ajiye masa sai kace wani sarki.
      cikin wani salo na isa da ƙasaita yakai zaune tamkar wanda ya samu kujerar falonsa, yanda yake abu cikin izza da isa ya sani yin zuru ina kallonsu.
       Wanda yake riƙe da takalmin ya kai tsuggunne gabansa ya fara zare masa takalman robar dake ƙafar tasa irin na masu kiwo ɗin nan duk sun fashe saboda wahala. Takalman ya shiga saka masa, shi kuma ya amshi hular kwanon ya ɗaura a kansa tare da sauran kayan. Miƙe yay cike da ƙwarewar ƙasaita ya ɗare bisa mashin ɗin.
       Makaho da wanda ya kawo masa mashin ɗin suma duk suka haye sauran mashinan da ƴan uwansu suke..
       Kasancewar nashi mashin ɗinne a gaba ya sake daidaitashi. Cikin sallon ƙasaitarsa ya ɗaga hannunsa sama, ƙaramin yatsansa ya fara miƙarwa alamar (ɗaya), ya ɗaga na kusa da shi (biyu), yana ɗaga na ƙarshe alamar (uku) suka saki wata irin sautin ƙara data gigita kusan mafi yawan jama'ar layin. Tuni mata suka shiga gudun afkawa cikin ɗakuna, masu ƙarfin hali naɗan leƙowa suga mike faruwa?.
        Kasancewar layin da suke yana gab da bankin tuni saƙonsu ya isa kunnuwan jami'an tsaron dake zagaye da wajen. Har rige-rige jami'an tsaron keyi wajen hawa ababen hawansu, dan sunsan wannan singing ne na tabbatar da shiɗin na kusa da bankin.

        Daga ɓangarensu kuwa a wani irin mugun gudu suka harbo mashinan suka fito daga cikin layin, hakan yayi dai-dai da gabatowar motocin jami'an tsaron kwanar layin suma. Isowar jami'an tsaron ya sakasu danna wani abu a jikin mashinan nasu tuni hayaƙi ya gauraye titin baki ɗaya suka harba mashinansu tamkar walƙiya.

       ALLAH yaso a ƙaramin titi suke, da tabbas babu abinda zai hana haddasuwar gagarumin haɗari saboda yanda gaba ɗaya titin ya lulluɓe da hayaƙi, mai tahowa baya ganin mai tafiya.
      Sai dai duk da wannan hayaƙi hakan bai hana mota ɗaya cikin motocin jami'an tsaron bin bayansu ba a guje suma. Kusan mintuna uku cikakku hayaƙin ya ɗauka kafin ya baje, zuwa lokacin tuni mashinan nan sun ɓace ɓat daga yankin ma baki ɗaya tamkar na aljanu.
       Rai a ɓace sauran jami'an tsaron ke yarfar da hannaye, kowa yanajin takaici da ƙunar rai cikin zuciyarsa. Masu ƙarfin hali ne ke ƙoƙarin tsintar ƙananun takardun dake yashe a ƙasa alamar masu power bike ne suka sakesu tare da hayaƙin. Abinda ke a jiki ya ƙara harzuƙasu, dan kamar yanda ya saba barin sunansa idan ya aikata laifi a wannan karonma hakane. Sunan nasa ne a jikin takardar tare da zanen fuskarsa ta tsoffi raɗam.
      A zabure ɗaya daga cikin jami'an yace, “Kai! Wannan ai yana cikin al'amajiran dake a ƙofar bankin suna bara”.
     “What!!?”
C.P ya faɗa a matuƙar zabure.
       Manager da shima ɗaya daga cikin takardar ke hannunsa muryarsa a hargitse ya ce, “Tabbas wannan al'amajirin sati biyu da suka wuce na fara ganinsa a wajen nan. Amma dai wannan ya cika matsiyaci”.
         Zafi da ƙunar da zukatansu suke musu ya hana kowa ƙara magana. A kuma dai-dai lokacin matar gwamna da yaronta suka iso wajen suma. Dan sun gaji da jiran tsammani a cikin banki. Jin cewar basu kamashiba yasa ɗanta ya fara masifa tamkar zai haɗiye harshensa. Hakama mataimakin gwamna ya tabbatar musu karsu wuce awanni ashirin da huɗu basu kamo hegen ba.
    Daga haka kowa yabar wajen rai ɓace. Jami'an tsaron ma kowa ya koma inda ya fito domin ƙulla mai yuwuwa.

ZAFAFA BIYAR NEW YEARWhere stories live. Discover now