page 4

178 4 1
                                    

*_SO DA ZUCIYA_*

*_NA_*

*_NANA HAFSATU_*

*_ZAFAFA 5 (2022)_*
*_FREE PG:4_*

_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY💯💯🙌🏽❤️_

_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_

_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR’ANI MA GIRMA_

_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI💯🙌🏽❤️_

_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇🏾_

https://youtube.com/c/sudaiskura

_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._

_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan🙏🏻_

•••.        •••.     •••.    •••.

***Dadaa dake cikin dakin ta ita da yara, tana jiyo hayaniyar masu kawo amarya tai saurin kashe fitilar shekarau ya gaza din da ta kunna musu dan suga haske. Tayi haka ne dan mutane suyi zaton sunyi bacci dan gudun kar ayi mata habaici da yawa. Gwaggo Lami ce ta shigo gidan da gud’ar ayyirrrrrrriri tana cewa.

“Amarya ta shigo gidan masoyinta, Jimmamman tako kafarki da hannun dama saboda kore asirin kishiyoyi.”

Gabaki daya mutanan da suka yo rakiya suka kwashe da dariya tare da hada baki wajan furta.

“Ahayye!! Nanayeeee casss...!”

Mama Atuwa na daki sai faman kwafa take, ji take kamar ta harbe daga su har amaryar saboda kishin da yake damunta. Kai tsaye kuwa suka nufi dakin ta zasu kai amarya a hada su tare da yi musu nasiha. Sai da suka fara shiga ta mike a zabure tana wani irin nishi tace dasu tana nuna su da yatsa manuni.

“Aradun Allah duk wace ta kuskura ta shigo sai na balla mata kafar baya bakaken munafukai. Daga ku har Ardon a karkashin kafata kuke babu uban da nake tsoro billahillazi.”

“Heeee caras-cas! Ardo dai ya yi sabon zubi, kuma dole yadda ya dama haka za'a shanye a gidansa.” Cewar wata kanwar Jimmamman daga can bayan Gwaggo Lami.

“Aikin banza aikin wofi BZ din? Har bazawara tana da wani daraja da kima a gurin miji? Mune nan aka aure mu a yan mata yan shila ba wai ragowar wani ba.”

Mama Atuwa tai maganar cikin cusa musu haushi. Sai dai babu wanda yaji din sai ma wata gud’a da suka sake yi kamar sun zo gidan gala.

“Haba ke kuwa Hafsatuwa, wannan auren fa ba haramun bane. Annabi Muhammad S.A.W ya auri bazawara, dan me zaki dinga aibata makamancinsa? Kiyi istigifari dan kinyi sabo babba.”

Gwaggo Lami ta fada tana kamo hannun Jimmamman suka juya dan shiga wajan Dadaa, wacce tasa duk suka kwanta tare da yin kamar sunyi bacci. Duhun da suka gani ne yasa su haska fitilun dake hannuwansu, nan suka tarar da Dadaa kwance tayi ‘dai-dai tamkar mai baccin gaske. Gwaggo tace a rabu dasu a kai amarya dakinta. Jimmamman na yafe da mayafi cikin ranta tana ta sak’a yadda zata zauna a gidan, musamman zama da Atuwa dan taga itama ba wai mutunci gare ta ba.

Sai da suka gama habaice-habaicen su kafin su tattara kowa ya kama gabansa, aka bar amarya ita kadai a daki tana jiran shigowar angonta.

•••.   

ZAFAFA BIYAR NEW YEARWhere stories live. Discover now