*_SO DA ZUCIYA!!!💞_*
*_NA_*
*_NANA HAFSAT_*
*_(MX)_**_ZAFAFA BIYAR 2022_*
*_SHAFI NA DAYA_*
*_FREE PG: 1_*___________
*RIMIN KEB’E*
*GADA MAI ‘DOYI**GIDAN ARDO BORKINDO*
(AURE-AURE)“Wahidi...! Sadaka..! Almajiri bara iya, Iya dan Allah dan annabi, Iya yunwa batada hankali, Iya ko ‘kanzo ne ba miya. Ko gaya ne ba miya...Iyaa...wahidin wahidiya..!”
Almajirin nata rera baitin barar sa. Dadaa nata ce masa yayi hak’uri, yaki tafiya, Ya rike robar barar sa ahannun hagu, Dayan hannun kuma ya sakashi a hanci yana sakato daskararren tasono yana gogewa a kodaddiyar rigar shaddar jikin sa ruwan bula, Kayan sun fattatake.
**Fatimah-Zahrah (Zaarah) Yar bafulatanar budurwar na kwance akan shamilalliyar katifar kwanciyar ta irin ta boarding school dinnan. ‘Kulaficin nacacciyar baitin rera barar almajirin ce ta tashe ta daga baccin yunwar dole data dauke ta. Ta ja tsaki tana sosa manyan gashin idanun ta da suka jike da ruwan hawayen ta. Ta juya kanta gefe, Ta sauke idanunta akan mahaifiyar ta dake zaune tana yanke faratan hannun ta.
“Dadaa..”
Ta ‘karasa tana rufe bakin ta, Bayan bahaguwar hammar data taho mata.
“Kin tashi?”
“Na tashi Dadaa! Bansan bacci ya dauke ni ba ma.”
“Ai wannan wanki da kika tula dole ki baccin gajiya, Allah ya yi albarka.”
“Aamin Dadaa”
“Ga abinci can cikin kwanon ki. Tun da zafin sa yanzu nasan ya huce.”
Da azama ta janyo kwanon ta bude shi, Dauke yake da danwake da man ‘k’uli da jan yaji.
“Wayyo Allah na! Danwaken Iya fatsuma. Dadaa ina su Hamma Modibbo Da Na'eelah da Raheelah?”
“Su Raheelah sun tafi Islamiyya, Hamman ku kuma bai jima da barin nan dinba. Shi ya kawo danwaken nan ma.”
“Allah sarki Hamma, Allah ya kara budi.”
Cikin haka mahaifin su Malam Ardo borkindo ya shigo cikin gidan bakin sa dauke da sallama.
“Atuwaa,Dadaa ku fito”Ya zunduma musu kira yana daidaita zaman da yayi akan wata ‘ballalliyar kujera da ta gaji da lalacewa.
Mama Atuwa ta fito daga cikin d’akinta tana susar kunne da gashin kaza. Ta tsaya ‘kerere akan sa sanye cikin riga da zani kowanne kalar sa daban. Yaja tsaki yana girgiza kai.
Atare Dadaa da Zaraah suka fita tsakar gidan nasu,
“Bappah Barka da dawowa”
Zara ta tsugunna har kasa tana yiwa mahaifin nasu sannu da zuwa. Ya amsa fuskar sa a daure. A ‘darare ta koma cikin da’ki. Don inda sabo ta saba da tsangwama da kyarar mahaifin nasu.
“Sannu da zuwa...” Dadaa ta masa sannu ta rakube a gefe ta zauna.
“Ayau yau, Nakeso a share dakin abincin can. Jibi i war haka amarya zata tare.”
Gaba d’aya Dadaa da Mama Atuwa sai suka zube masa idanun su. Kowannen su kallan sa yake cikin tsantsar mamakin kalaman sa. Dai dai lokacin da almajirin nan ya sake dawowa zaure yana kurma barar da yake. Hade da bubbuga ‘kafar sa a kasan fashasshen dab’en da akayi wa zauren.
“Wahidi...! Sadaka..! Almajiri bara iya, Iya dan Allah dan annabi, Iya yunwa batada hankali, Iya ko ‘kanzo ne ba miya. Ko gaya ne ba miya...Iyaa...wahidin wahidiya..!”