*DABI'AR ZUCIYA*
03
*Free page**_GARABASA DAGA ZAFAFA BIYAR_*🔥🔥🔥🔥🔥
*_Bononza kashi na hudu !!!_**Mun saurara koken masoya,mun kuma amsa,domin farincikinku shine namu!!!*
*Daga yau zuwa TALATA zuwa gobe LARABA,zaki iya samun litattafan zafafa biyar bisa farashin ragi wato 700 kacal*
*MAZA GARZAYA KAFIN RAHUSAR TA QARE,KI TURA 700 DINKI ZUWA WANNAN LAMBAR ACCOUNT DIN*
6019473875
MUSAA SAFIYA ABDULLAHI
keystone Bank*Saiki tura shaidar biya ta nan*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
08184017082*Ga masu tura katin waya ko kuma VTU,saiku tura ta nan,kudi da shaidar biya*👇🏾👇🏾👇🏾
09134848107*_ALLAH YA BAWA ME RABO SA'A_*
Dai dai sanda take kalmashe jela ta qarshe daga kitson data yiwa ummansu yaran sukayi sallama,umman tasu ta janye kanta daga tsakanin qafafun kaltum din tana amsa sallamar kana ta qarashe mitar ta data fara dazu
"Daga yau ba zaki sakemin kitson dare ba" ta fada tana janyo dankwalinta me santsi ta daure kanta dashi.Hannun kowanne cikin yaran uku riqe yake da littafi exercise da kuma pencil,idanunta a kansu,tana binsu da kallon mamaki,mamakin yadda akayi suka sake dawowa gurinta bayan tataburzar da aka gama yi wancan satin,wanda ya tilast ummanta tayi magana akai,duk da kasancewarta mai matuqar kara da kawaici,ba kasafai akejin bakinta ba kan al'amura da dama ba,wannan yana daya daga cikin dalilin da ya sanya azzaluman mutanen dake tare da ita suke amfani da wannan damar suna cin karensu babu babbaka a kanta,daya daga cikin tarin abubuwan dake ciwa kaltum tuwo a qwarya.
Dukkansu suka haye saman tabarmar suna rige rigen miqa mata littafin hannunsu suna fadin
"Ni zaki fara yiwa,dabbobin dake cikin gidansu kowa akace kowa ya zana,yasa kala" a hankali ta maida dubanta ga ummanta dake zaune daga gefan tabarmar,wanda ta matsa ne ta basu waje ta yadda sararin wajen zai ishesu,a duniya babu abinda take qauna kamar zane,duk da cewar batayi karatun boko ba,amma Allah yayi mata baiwa ta iya zane,wanda dukkaninsu basu isa suce ga daga inda ta samota ba,idan ta zana maka abu zaka rantse da Allah an zanashi ne bisa ilimi da kuma qwarewa,wannan dalilin ya sanya duk sanda aka baiwa yaran zane a makarantar boko basu da wanda suke kawowa sai ita,kusan mafi yawan yaran maqotansu ita ke musu,kota kwatanta musu yadda zasuyi.Kallon da ta yiwa umman tasu a yanzu ta yishi ne cike da kwadayin ta bata umarni kan tayi musun,saidai ko kallo inda take umman batayi ba,hakan ya sanyayar mata da jiki,ya kuma bata amsar hukuncin daya kamata ta yanke,don haka murya a sanyaye ta dubesu
"Kuje ku kaiwa asiya,ta iya zata zana muku" sak dukkansu sukayi,sai daya daga cikin yaran ne yayi qarfin halin yin magana
"Nidai ki zana min don Allah,Allah wancan karon data zana mana babu wanda yaci,malamin ma sai daya zanemu" ajiyar zuciya ta sauke,cikin sigae lallama tace
"Habibu....kuje,wannan ba mai wuy....." Kafin ta qarasa taji muryar umman nata sanda take miqewa tana barin tabarmar tana fadin
"Zana musu" wani dadi taji ya sauka har qasan ranta,ba bata lokaci ta miqa hannu don amsar littafin daya daga cikinsu nan fa rigima ta kaure,da qyar ta sasanta su akayi quri a,wanda yaci ta karba nasa,ta qwalawa habiba kira ta basu aron wata fitilar aci bal bal din,ta ajjiyeta a tsakiyarsu,sannan ta duqufa ya fara zanen cike da nishadi.Boyayyar ajiyar zuciya umma ta saki,daga nan inda take zaune tana iya hango komai yadda yake faruwa,tana iya hangen zallar nishadi a fuskar kaltume din da yadda take zanen cike da karsashi suna hira da yaran,batasan me takeji ba,batasan meye a zane ba har haka da take qaunarsa,saita kuma sakin wata ajiyar zuciyar karo na biyu,zuciyar tata na cika da fata na alheri ga iyalan nata.