DEEN MARSHALL NA MAMUHGHEE

547 9 0
                                    

_*DEEN MARSHALL*_
_Mamuhgee_

*_ZAFAFA BIYAR_* 🔥🔥
_*So Da Zuciya*_
Miss xoxo
_*Halin Girma*_
Hafsat Rano
_*Dabi'ar Zuciya*_
Safiyya huguma
_*Takun Saka*_
Billyn Abdul
_*Deen Marshal*_
Mamuhgee

_Pay @08184017082 Or 09134848107_

*1*

*_BismillahirRahmanir-Raheem_*

Ahankali ta dago kanta dake 'dan Sara Mata ta kalli kofar office din nata da aka kwankwasa batareda ta motsaba ta dauke idonta akan kofar tana sake boyayyan numfashin dake bayyanarda qosawarta da halin ABBAS LAMIDO sbd ko ba'a fada ba tasan koba shi bane to koma waye to al'amarine daya shafi sunan Abaas aciki.
Turo kofar akai tareda shigowa ko Bata dagoba Jin takun takalma yasa ta fahimci Sarah ce Dan Haka ta sake lumshe ido tana dago Kai ahankali tareda dauke hannunta daga kan aikin datakeyi a laptop ta aje gefe tareda gyara zama ta Kai hannu ta dauki ruwan data fitar a fridge tun dazu sbd su huce daga sanyi ta bude robar ruwan Tasha kusan rabi ta ajiye sauran tana cewa"

Sarah akwai wani abune?

Sai alokacin Sarah ta matso ta zauna kan kejerar hutawar dake kallon wadda  *_NAJMA_*  ke zaune tana jiran abinda zata fada,
Saidata Dan sauke numfashi itama kafin Kai tsaye tace"

Naj dazu kafin isowarki zuwan chairman Abaas biyu office dinnan Kuma Banga alamar lafiyaba a yanayinsa
Zan iya cewa dai yanayin da aka Sabane.

Sai alokacin _*NAJMA ABDULLAHI BELA*_ ta dago da fararen idanuwanta dasukai laushi da gajiya tareda damuwar Jin abinda aka fada din ta kalli Sarah tsawon lokaci kafin ta sauke nata numfashin itama ta bude Baki da muryarta me taushi dake kokarin boye damuwarta tace"

Meyene matsalar Abaas Kuma yanzu?

Cikeda kulawa Sarah tana kallonta tace"

A yanda nakega inaga bazai wuce akan maganar jiya bace da Dr Sa'id yazo gurinki sbd zuwansa biyu Ana cewa kunfita tareda Dr Sa'id din.

Sai alokacin ta tuno da zuwan Dr din jiya da fitar da sukai zuwa taron makarantar yaronsa a wata private school dake kusa bama nesa ba.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana daukan wayarta Dan kiransa Dan kuwa ma wannan karon yayi kokarin rashin binta gida tun Daren jiyan yayi abinda ya Saba.

Ringing wayar ta ringa yi harta katse Bai daga ba ta sake saka Kiran Bai dagaba har lokacin
kusan Kira uku Tai Masa baya dagawa ta kashe wayar tareda ajewa gefenta ta waiwayo ta kalli Sarah tace"

Bai dagaba
Baya office dinsa ne?

Banajin yafita Dan ko kafin nashigo Naga wucewar secretary dinsa hanyar zuwa office dinsa.

Juyar da fararen idanuwanta tayi ta maidasu kan wayarta da tadau ringing taga sunan Hanifa ne akai ta lumshe idanu ahankali tana sauke ajiyar zuciya tareda Jin sanyi aranta sbd Hanifa Marshal Alfa Bata Bata lokaci komai kankantarsa batareda takirata ba idan taji wani Abu yafaru da ita.
Kallon Sarah tayi da alamar tambayar cewa"
Kinfada Mata yawon da Abaas yayi na nemana yanzu da safe kenan?

'yar dariya Sarah tasaki tana miqewa ta nufi hanyar fita tana cewa"

Sorry ma'am itace takirani da kanta ta tambaya.

Ficewa tayi tareda rufo kofar office din har lokacin da sauran dariya akan fuskarta saidai ta baro jikin kofar sukai kusan Karo da Abaas daya qaraso office din sanye cikin suits ash dasukai Masa kyau matuka kasancewarsa kalar ruwan tarwada Kuma cikakken kyakkyawan namiji meji da lokaci da kuruciya da nera.

Da sauri Sarah ta matsa gefe tana sake sake fuska da tace"

Barka chairman.

Ko kallonta beyiba ya bude kofar office din dake daukeda sunan NAJMA BELA ajiki ya shige tareda rufo kofar.

ZAFAFA BIYAR NEW YEARWhere stories live. Discover now