_*SO DA ZUCIYA_*
*_FREE PAGE:3_*
_*NANA HAFSATU_*
*_ZAFAFA BIYAR PAID BOOKS_*
*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bankSaiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .___________
****Dai-dai lokacin da su sameerah, Farillatu da kuma guggun yaran mak’ota suka fara ife-ifen yiwa su Sailuba da Hajara oyo-yo. Sai yauk’i suke suna baje hanci. Su ga yan hutu da sukaje garin Suleja wajen kanwar mahaifiyar su (Mama Atuwa). Su Sameerah sai gudu suke suna tsallen murnar dawowar yayyun nasu. Dandazon sauran yara na biye dasu. Kayan su duk’un duk’un. Wasu ma pant ne kawai ajikin su ba riga. Sai dai fatan Allah ya kare kawai.
Murnar ife-ifen shelar dawowar su Sailuba ne yasan ya Mama Atuwa tsaida maganar da take na Jimmamman (Jim-Mam-man) amarya kuma bazawara ga Malam Ardo mijin su. Ta kwasa aguje tana rangad’a gud’a, Kai kace sabuwar amaria aka kawo. Nan duk murnar dawowar ‘yammatan yayan nata ne. Sailuba da Hajara.
“Ahayye biyu kyautar Allah, An buga daku anbar ku ya zasuyi daku? Sai kallo. Kaf Rimin kebe baya ku ‘yayan Atuwa. Allah dai ya kawo muku mazaje masu motoci mai nishi su aure ku...”
Su kuma sai hura hanci suke, Suka ajiye jakar ghana must go din da sukayi kama kama da hannun ta.
Kamar su d’aya da Atuwa, Yanayin fad’adden bajajjen hancin ta daya kama gam a fuskar ta. Hakan suma suka dakko kamannin nata. Sai hasken mahaifin su da sukayi suka kuma ‘kara dana bleaching. Saboda tsananin yadda fatar su ke shekin kyallin yellow yellow, Da kuma bak’i bak’i a kafafuwan su da hannayen su.
Kana ganin su kallo d’aya zakayi musu kasan yan biyu ne. Suna kama da junan su ainun. Sai dai tsayi daya bambamta. Hajara tafi Sailuba tsayi. Suka zube akan tabarmar Atuwa dake shimfide a dan tsukukun kofar dakin ta. Duk ta huhhuje taji jiki ainun tabarmar. Sai ‘daga kai take tana leka jakar kayan su.