*_Typing📲_*
*_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_*
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_ZAFAFA BIYAR 2K22_
_________________________
Chapter Three
...........Hafsat tai azamar ɗago kanta tana dubanta, duk da hawayen da ke sharara a kumatunta na azabar da take ji a ƙafarta, cikin ƙarfin halin ta ce, *_“Muhibbat!_* dan ALLAH karki sakamu a wahala da hatsabibancinki. Kwana huɗu kenan kacal da gama kashe wata wutar da kika kunno, indai dan nice karki damu, dama ALLAH ya ƙaddara sai naji ciwon nan koda bata sanadinsu ba, ina roƙonki kibarsu Ya Abubakar su huta da shegen tsokanarnan taki”.
Harara Muhibbat ta zubama Hafsat da murguɗa baki tana juya idanu, harta buɗe baki zatayi magana sai kuma tayi shiru saboda isowarsu cikin harabar asibitin.
Ko kaɗan jami'in nan baiso Muhibbat tayi shiru ba, amma kasancewar yasan aikinsa sai bai nuna hakanba, sai ma ƙoƙarin taimaka musu da yayi domin ganin an shiga da Hafsat taga likita akan lokaci.Da taimakon jami'in aka duba ƙafar Hafsat da ta samu tsagewar ƙashi, Zahidah sai godiya take masa saboda ƙoƙarin da yaketa musu, dan sunso su kira gida ya hanasu. Hanawar tasa kuma ta bama Muhibbat haushi, dan a ganinta ya cika shishshigin tsiyane kawai, musamman daya kasance duk wani motsinta sai ta ritsa idanunsa akanta.
Tun tana hararsa a ƙasan ido da masa ƙunƙuni har takai ta fito fili tana dalla masa harara. Ganin dai ba daina kallon nata zaiyi ba a tsiwace ta ce, “Wai malam kallon fa? Dan ALLAH karka cinyeni a tsaye mana”.
Sosai yanda tai maganar ya bashi dariya, dan tsaf ya gama fahimtar itaɗin matsiwaciyace ta gaske. Sannan babu tsoro sam a cikin idanunta kona sisin kwabo. Komai baice mata ba, sai ma ɗauke kansa da yayi kawai gefe tamkar bai jita ba. Taja tsoki tana murguɗa baki da miƙewa tabar wajen.
Can gefe ta koma tana ƙoƙarin sarrafa wayarta cike da ƙwarewa. Cikin ƙanƙanin lokaci kiran da tayi ya shiga, sai da aka ɗaga sannan takai kunne tana faɗin, “Assalamu alaika Yaya”.
Amsa mata akai da ga can, kafinma ya gama rufe baki cikin shagwaɓa taci gaba da magana. “Yah Uthman muna hospital ne”.
A tsananin tsorace muryarsa ta bayyana, “Hospital Auta?! Waye bai da lafiya?”.
“Oh Yaya calm dawn, Hafsat ce taji ciwo a ƙafa amma da sauƙi, dan yanzu haka ma an gama mata gyaran sunce tsagewan ƙashine”.
“Ya ALLAH! Auta wai sai yaushe ne zakuyi hankali ku kam? Yanzu haka a wajen shegen rawan kan nan naku hakan ta faru?”.
“Na rantse Yaya bafa da gangan bane, wasu marasa kirki ne suka kusan turemu a power bike”.
“What?!. Power bike fa? Ku miya kaiku kan titin da masu power bike kebi!!?”.
Yanda yay maganar a tsawace ne ya sata zabura, duk cikin yayun nata yafi kowa sauƙin hali bayan Yah Abubakar. Sai dai kuma idan ya rikice tafi tsoronsa fiye da kowa a cikinsu..... Cikin katse mata tunani yace, “Zan turo muku Ammar yanzun nan danni naje katsina ne..”
Yana gama faɗan hakan ya yanke wayar. Kasaƙe Muhibbat tayi tana kallon wayar, yayinda gefen zuciyarta ke ayyana mata neman mafita. A fili tace, “Tab Yah Ammar! Wlhy bazan bari ya samemu a asibitin nan ba wannan ɗan matsalar”. Da sauri tabar wajen zuwa inda jami'in nan mai amsa sunan driver-n taxi yake da Zahidah.
“Zahidah tunda sunce zasu iya sallamarmu gara mu wuce gida, dan na haɗa gurmi wlhy”.
Zahidah dake mata kallon mamaki tace, “Gurmi kuma! Nami to?”.
“Humm daga kiran Yah Uthman fa na faɗa masa shine wai zai turo mana Yah Ammar shi yana katsina. Ni kuma wlhy banason Yah Ammar yazo asibitin nan ya samemu saboda yafi gidan haya matsala kema kin sani”.
Kafin Zahidah dake dariya tace wani abu jami'in nan yay saurin cewa, “Ai sunma sallemu daman, inaga ku shiga ku fito da ita kawai mana”.
Harararsa Muhibbat tayi tana ɗaure fuska. “Ikon ALLAH sai kallo, wai ni kam bawan ALLAH ca'akai ka kula damu ne kokuwa? Taxi ɗinka muka hau ka kawomu inda muke buƙata, to sai mi kuma ya rage?”.
Murmushi yayi idanunsa a kanta, “Sai ku bani kuɗina ya rage ƙanwata”.
“Ya salam! Dan ALLAH kayi haƙuri bawan ALLAH. Wlhy gaba ɗaya mun shafa'a ne”. Zahidah ta faɗa tana laluben bag ɗinta.
“Karki damu ƴammata babu damuwa. Nasan kuna a rikicene ai. Amma ƙawar nan taki ya kamata ta rage tsiwa”.
Zahidah dake miƙa masa ɗari biyar tai dariya, “Kaga fita batunta ga kuɗinka mun gode sosai”.
“Ai karki damu riƙe kawai sai na kaiku inda zaku yanzu sai na amsa”.
“Malam gara dai ka amshi kudinka kai gaba, dan bazamu sake shiga motarkaba ɗan sarkin shiga sharo ba shanu”. Muhibbat ta faɗa tana hararsa.
Saurin toshe bakinta Zahidah tayi itama tana hararta, “Wai nikam Hibbat kodai wadda tai miki wankan jego bata gasa bakin nan bane da baya barin kowa. Ina laifin bawan ALLAHn nan, kigafa ƙoƙarin da yay mana akan Hafsat”.
Hibbat ta buge hannun Zahidah da haushi, “To dan kuma ya taimakemu sai ya ishemu da shishshigin jaraba. ALLAH ni banason shishshigi da ƙwala kai a faranti irin na wasu mazan”.
Tana gama faɗa tai shigewarta ɗakin da Hafsat take. Duk binta sukai da kallo, kafin Zahidah ta maido kallonta ga jami'in. “Ayya dan ALLAH kai haƙuri. Ita haka take sam ba'a gane kanta tamkar mai aljanu”.
Ƙaramar dariya yayi yana sosa tsakkiyar kansa da key ɗin taxi ɗin. Yace, “Kinga karki damu ni salon natama birgeni yakeyi, irin waɗanan sam ba'a cutarsu a duk inda suka shiga. Je kawai ki fito dasu na kaiku kafin a sake kirana ɗan shishshigi”.
A yanda ya ƙare maganar cikin langaɓe kai kalar tausayi yasa Zahidah ƙyalƙyalewa da dariya tana shiga ɗakin domin su fiddo da Hafsat..Da ƙyar Muhibbat ta amince jami'in nan mai taxi ya ɗaukesu zai maida gida. Dan ko sai kumbura take a motar tana ƙananun ƙunƙuni alamar bataso hakan ba. Shi dai yakanyi murmushi lokaci-lokaci idan ya ɗago ya dubeta ta mirror yaga yanda take cika baki da iska tana harare-harare........
★.★.★.★.★.★
Kamar yanda aka saba yau ɗinma tuni media ta ɗauka. Gidajen redio dana televisions harma da yanar gizo mutane sai tofa albarkacin bakinsu suke. Dan lamarin wannan gagarumin ɓarawo ya daina bama mutane tsoro sai al'ajabi da mamaki. Kullum ji suke jami'an tsaro na farautarsa, mai makon ya tsorata ya ɓuya sai ƙarama gawurta yake a al'amuransa. Gashi babban abinda zai baka mamaki manya-manyan ƙusoshin ƙasar masu lasisin iya ɗaukar mataki yake bi yana yashewa da saka rayuwansu cikin tarkuna. Dan da wahala ya kafa maka ƙahon zuƙa daga ƙarshe baka koma ƙarƙashin binciken hukumar *EFCC🐦* ba, ko ka ƙare rayuwarka da ciwon paralysis saboda barazanarsa idan yay dirar mikiya aka kaddarorinka da kuɗaɗenka. Yanzu dai yanda ya yashe asusun matar gwamna bawai ya barta bane kenan. Duk da neman da ake masa ruwa a jallo cikin kwanaki ƙanƙani zai sake silalowa ya danƙara mata wani harbin mai zafi har sai ya kai rayuwarta ƙasa kwance zai barta.
Duk yanda ƴan jarida sukaso jin ta bakin jami'an tsaro da gidan gwamnati akan wannan al'amari abin ya gagara. Sun haƙura dole suna bada labarin iya abinda idanunsu suka gani da ɓarnar da wannan mutumi ya tafka a baya kafin wannan ɗin.
Yayinda a gefe kuma jama'ar gari suketa tofa nasu. Wasu najin daɗin abinda yakeyi ɗin dan bawai a satar kuɗin manyan ƙasar kawai ya tsaya ba, har ƴan fashi da suka addabi mutane da ƴan ta'adda yakan kama waɗanda har yanzu babu wanda zai iya cewa ga inda yake kaisu ya ɓoye. duk da kuwa shima ɗin mai laifi ne a bayyane, wasu ko na jifansa da ALLAH wadai saboda suna ganin bashi da maraba da ƴan ta'addar da yake kamawa ai. Yayinda ƴan kanzagi ke zaman rubuta shaci faɗi su yaɗa a kafafen yanar gizo game da shi da ayyukansa..............✍*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI......_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bankSaiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k)*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR
*_ALLAH ka gafartama iyayen mu😭🙏🏻_*