🧕UNAISA🧕*A*
✍️Ayshatuuu
Na sauke wayar daga kunnena tareda sakin Murmushin jin dadi, bayan shekaru da na dauka Ina jiran wannan lokacin se gashi yazo, komai lokaci ne sede jiran se me karfin Imani. Na kalla gidan da komai na ciki Wanda nawa ne, na Kara kallon hoto Na sanye da Ash din Abaya ta idon duniya, fuskata dauke da Murmushin da ko kana bacin Rai ka kalla se kayi murmushi, Yana tsaye a bayana sanye da dakakiyyar shadda Ash sede nashi Ash din yafi nawa duhu, yayi kyau karshe Yana murmushi, na saki ajiyar zuciya Ina hamdalan cikar buri. Na aje wayar Jin ana kwankwasa kofa, cikin sauri na Nemo veil Dina dake ninke akan cushion gefe Dani na lulluba sannan na nufi kofa bayan na zura slippers a kafata, dama na aje ne saboda ko ta kwana. Seda na leka Amma banga ko waye ke knocking ba kawai se na bude, a take wata Mata da Kuma karamin yaron da Bai wuce shekara biyar ba Suka bayyana. Fuskar ta dauke da murmushi, matar ta girme ni sosae nesa ba kusa ba, kana kallonta kasan ta manyanta Kuma Yar gayu ce ta gani ta fada, nikam a rayuwata Ina son Yan gayu, take naji ta burgeni, ni din Yar gayu ce ta bugawa a jarida, ko lokacin da bamu da komai bamu da gata bamu da Mai taimako a hakan idan ka kalleni ba zaka taba kawowa a cikin wahala nake ba. I always mind how I look. Na Bata guri ta shigo tana fadin
" Amarya Bata laifi ko ta kashe Dan masu gida!"
Nayi murmushi tareda ayyana kada dai na kashe din. na karaso ciki na Mata tayi ta zauna tana fadin
" Ammar come and sit, baka gaida Anty ba"
Yaron ya zauna Nima na zauna Ina murmushi nace
" Zo nan boy"
Ya make kafada tayi dariya, na gaida ta ta amsa da faraar da tunda na bude take a fuskar ta, na Mike na shiga kitchen na dakko ruwa da juice, se su alkaki a karamin plate, na jera Kan tray sannan na kawo musu. Ta dubeni tace
"A'a harda wahala! Nagode sosae"
Nayi murmushi anxiously Ina jiran tayi min bayani
" Sunana A'isha, ni neighbor din ki ce ta baya, megidan ki yayi ma megidana maganar zuwan ki, shi ne na lallabo mu gaisa"
Na Kara fadada murmushi na ina shafa Kan Ammar da ya dawo gefena Yana Wasa da throw pillows din da na Gama jerawa, nace
" Naji dadi sosae Anty, sunana Unaisa. Nagode da ziyarar ki"
Tayi murmushi jin nace Mata ta ci abinda na kawo Mata, karshe tayi min bayanin yaranta uku bayan Ammar daya Tana karatu a Alqalam katsina, me bi Mata Yana UAE Yana karatu, se me bi Masa tana secondary ita anan cikin anguwar mu take yi.
" Amma Anty boarding Kuma? Na zata nan Bayan mu makarantar take"
Tayi murmushi tace
" Ai dukka boarding sukeyi, Kinga Ammar ma se yayi"
Nace
" Allah ya kaimu har na fara jin tausayin shi"
Kafin ta bani amsa se wayata dake Kan side table ta fara ringing, na saka hannu na dakko, jikin screen din kamar yadda nayi saving King, shi ya bayyana, saboda a duniyata shi din sarki ne, shi ke mulkin zuciyata. Na saki murmushi jin tace min
" Daga Kiran ki Mana"
Na Kara a kunne na Amma maimakon naji muryar shi se naji akasin hakan, naji wata muryar daban. A take yanayin fuskata ya canja nace
" Ina me wayan? Me ya same shi?"
" Hajiya idan Zaki iya zuwa kizo nan general hospital yayi accident ne"
Shi ne amsar, amsar data gigita ni, Bai jira me zance ba ya kashe wayar, already Anty Aisha ta iso inda nake saboda yadda hannuna ke rawa, kirjina Yana sama da kasa alamar Neman iska nake, ta riko hannuna tana fadin
YOU ARE READING
UNAISA
RandomA yanzun maza da yawa suna shunning daga responsibilities dinsu, kamar yadda mahaifina ya auri mahaifiyata ya barta take daukar dawainiyar mu. Idan ya dawo ta samu ciki se ya tafi yayi shekara biyar Bai dawo ba, mu din mun tashi a hannun mahaifiyar...