🧕 UNAISA 🧕
*C*
✍️ Ayshatuuu
Haka na cigaba da Zama da Mamaa a gidan, yanayin zaman ya banbanta da abinda nayi tunanin ganin, na dauka baza mu taba maganar arziki da ita ba, yadda ta dinga fadawa Dada ta tabbatar idan Zan shigo na shigo da wasiyya ta Dan kuwa se ta min azabar dazan bar gidan da kaina, Amma ko kadan ko kallon banza Bata taba min ba, hasalima kallon da take min me dauke da tausayi ne. Har mamakin yadda muke zaune lafiya nake, last time da na sani balai take akan zaa auro ni, to gashi Kuma ta karbe ni hannu bibbiyu, ta hakura ta saduda, Amma akwai abubuwan da bazan manta ba. Ranar da aka Yi kwana bakwai akai addua a karkade, aka cire tampons Dake waje, wasu Suka gyara Mana gida sannan aka baje, Anna, Dada da Zuhra Wanda suka kasance tare dani duk ranar suka tafi, har mutanen hadejia ma, Anty Aisha ta tafi tun ranar uku Amma ana bakwai dinma tazo. Wannan tafiyar tasu yasa nayi ta kuka mussamman da Abba yace anan Zan zauna ba se na koma gida ba, Haka na yini a daki Ina kuka, har Anna ranar se da tayi kuka, Ina ganin rayuwata a garari take, musamman da nazo kwanciya Naga Babu Zuhra da zata raba dare tana lallashi na, da Kuma min Hira Koda bazan amsa ba. Abokan shi Wanda ya kasance Senate president, da sauran senators tunda shima elected senator ne in office. Seda suka saka aka cika Mana store da duk wani nau'in kayan abinci sannan suka shigo suka Kara gaida mu ya aje kudi ya juya ya tafi su Muhammad Suka raka su. Washegari gidan Babu kowa, Jin shirun da gidan yayi yasa na kasa fitowa Bayan na idar da sallah na zauna Ina jin kewar shi a dukkan sassan jikina, kwana uku kawai mukai dashi Amma kwanakin bazan manta dasu ba, sun kasance masu dadin gaske, ya sakani farin cikin da nake mamakin yadda mutum zai iya hakan, Na lumshe idanuna hawaye sun wanke min fuska ta, na saka kaina tsakanin cinyoyina Ina kuka tun karfina, Ina cikin kukan se wayata ta fara ringing, na saki ajiyar zuciya tare da janyo wayar Naga Anna ce me Kiran, cikin sauri na goge hawayena na dauka Ina fadin
" Anna Ina kwana?"
" Lafiya Lau Unaisa! Ya kike Ina fatan bakya kuka"
Na saka hannu na dauke hawayen dake cascading a kuncina, na danyi sniffing nace
" Na daina Anna"
Ta Jima tana min nasiha sannan tace nayi wanka na fita na taya Mamaa aiki. Daga Haka mukai sallama na Mike jikina ba karfi nayi wanka sannan na shirya cikin wata bakar riga wadda Babu ado ko kadan a jiki. Hulata na cire Dan saka sabuwa anan naji yadda kaina ya damkare guri daya. Comb na dauka na taje shi Ina runtse Idanuna saboda yayi tsamu. Na zauna a nutse nayi kitso biyu na hade jelar na saka a hula sannan na dauki katon veil na yafa a jikina na fito parlor. Ba kowa se masu aiki sunata fama, muka gaisa suna kara min gaisuwa, Ina tunanin murya ta Mamaa taji ta fito, idanun ta sunyi jawur Wanda ya tabbatar min kuka tayi, na gaishe ta, ta saki fuskarta tace
" Ya Kika tashi Unaisa?"
Nace
" Alhamdulillah Mamaa"
Muna zaune shiru, tunda ba sabawa muaki ba balle muyi magana, plus Ina Kama kaina, Ahmad ya shigo ya shirya zai tafi aiki, muka gaisa sannan ya nufi kofa zai fita se na dubi Mamaa nace
" Bazai ci abinci ba"
Tace
" Ahmad abinci fa?"
Ya girgiza Kai, ta dubeni sanann tace
" No dawo ka zauna, Bari kasha ko tea ne"
Haka ya zauna aka kawo tea din yasha sannan ya tafi ita dama Aseey ta wuce gidan ta tun Daren jiya, Haka Muhammad ma da Bilkisu matar shi sun koma Gombe tun jiya. Se ya rage daga ni se ita, aka hado abinci Wanda naci kadan se naji zuciyata na tashi kawai se na Bari, ta dubeni
" Ko akwai abinda kike so ne?"
Na girgiza Kai Ina Dan murmushi nace
" Kawai bakina daci nake ji"
YOU ARE READING
UNAISA
RandomA yanzun maza da yawa suna shunning daga responsibilities dinsu, kamar yadda mahaifina ya auri mahaifiyata ya barta take daukar dawainiyar mu. Idan ya dawo ta samu ciki se ya tafi yayi shekara biyar Bai dawo ba, mu din mun tashi a hannun mahaifiyar...