I

220 38 1
                                    


🧕 UNAISA 🧕

*I*

Ayshatuuu

Lokuta da dama mukan dauka cewar choice din mu ne haduwa da mutane, Amma idan muka nutsu mukai tsam da ranmu zamu gane cewar komai a rayuwar Dan Adam is destined, it's written. Kuma dukkan Wanda aka hadu dashi akwai manufa da Kuma hikimar hakan. Haduwata da Zuhra na dauka kawai choice Dina ne da na kulata har ta Zama kawata,  Amma Bayan lokaci me tsawo se na fahimci through her akwai abubuwa da Allah ya tsara Wanda ni ban sani ba. Zuhra mutuniyar arziki ce. Bayan Anna ita ce mutum ta farko da na fara bude Baki na Kira da kawata, duk da halayen mu by far sun banbanta nesa ba kusa ba, ita din mutum ce carefree and friendly yayinda nake akasin hakan, ni mutum ce me wahalar sabo kamar inada kin yarda, ko Kuma Ina tsoron been attached to someone Kuma ya tafi ya barni. Kullum Rana idan na tashi to se Zuhra ta kirani Wai kawai taji yadda nake, sede nayi dariya kawai nace ai lafiyata kalau, wani lokacin Kuma idan ta Kira se ta ce min wai banji komai ba Akan exams dinmu, har ranar nace ta jira Zan Kira Yaya Yusuf na tambaye shi, ko Dana Kira shi se yace min ai Yana Hanya zai zo gidan. Dan Haka na fito na fadawa Anna, ta dubeni tace

" Ni Wai meye ne tsakanin ki da Yusuf din Anty Nanah ne?"

Na bude Baki da mamaki nace

" Anna menene tsakanin mu kuwa? Kawai na Kira shi naji maganar makaranta ne saboda Zuhra ta takura"

Ta nuna min gefenta alamar na zauna, na samu guri na zauna gabana nata faduwa, tace

" Unaisa ba takura muku nake ba, Amma kinsan yadda komai ya kasance a rayuwar ku, Ina son ki manta da zancen wasu samari ki maida hankalin ki kiyi karatu, lokacin aure zaizo, lokacin da zakiyi samari Yana nan zuwa. Ni ki kalleni shekara ta Sha biyar akai min aure ko yadda zanyi sallah daidai ban Gama sani ba, ki kalla irin abinda na tsinta a aure me naci riba, Dan haka kudinnan komai da nake jurewa saboda kune, ki daure kuyi karatu kinji Adda?"

Na gyada Kai na Ina goge hawayen fuskata da tuni na fara kuka nace

" Allah Anna ki yadda Dani Babu wani Abu tsakanina dashi, ban taba tsayawa da wani..."

Tayi saurin katse min rantse rantsen da nakeyi tace

" Na sani Adda, kawai dai Ina tuna miki ne. Kin gama girkim?"

Na girgiza Kai tace to naje na karasa, na Mike da sauri na fita kamar Zan kifa, na shiga kitchen na karasa stew din sannan na jujjuye na gyara kitchen din. Ina gamawa Badi'a da Hunainah na shigowa, na dube su duk sun gaji nace

" Sannun ku, kuje ku cire uniform kuzo kuci abinci"

Badi'a ta saki murmushi tace

" Kai wallahi Adda kamar kinsan Yunwa nakeji"

Hunainah ta tsaya tana hura hanci tana tambayata abinda aka dafa, nace ta wuce ta bani guri, ta tafi tana bubbuga kafar ta. Babu jimawa se gasu sun fito daidai shigowar Nuzla, Dake Shirin fara waec, shiyasa take dawowa daban da kowa. Ta dubeni

" Adda an Gama abinci"

Anna dake fitowa daga bedroom tace

" Haka dai kullum kamar kamun Yunwa"

Tayi dariya ta wuce ciki, tray na dakko na hada Mana dukka Dan yawanci tare muke cin abinci, dukka tare muka zauna muka fara cin abinci, Bayan mun Gama Anna ta zauna tana bamu labarin yarintar Nuzla dukda wani abun na sani, tunda Zan iya tuna yarintarmu tare, Muna ta Mata dariya ita Kuma ta hade Rai tana fadin

" Allah Anna so kike Badi'a ta dinga tsokanata ko"

Anna ta dubi Badi'a wadda har ciki take rikewa saboda dariya tace

UNAISAWhere stories live. Discover now