🧕 UNAISA 🧕
*B*
✍️ Ayshatuuu
Mijin Anty Aisha yazo, aka Kuma sanar da Governor se gasu an aiko daga fadar shi, aka dauki gawar da taimakon masu zaman jinya harda staff din da securities, sannan aka rike hannuna muka fita, na jingina kaina da headboard din kujera motar Ina jin wani irin abu na bin jikina, I was scared, I was hoping ya tashi yace min April fool! Wasa yake Babu abinda ya sameshi, how I wish a movies ne ace ya shiga cardiac arrest ne! But wannan da gaske ne na rasa shi, shi din ya mutu. Wayar shi Dake hannuna ta fara Kara se Naga " Daughter" nasan Aseey ce hakan yasa na dauka na Kara a kunnena, cikin kuka take fadin
" Unaisa a wani asibitin kuke zamu taho?"
Hawaye ya cigaba da gangaro min nace cikin dashewar murya Dan ta riga da ta Jima da dashewar saboda kuka nace
" Ya rasu!!"
Seda tayi shiru na kusan mintina daya, either she's in shock ko Kuma kokarin digesting abinda na fada take, se kuwa ta saki kuka tana fadin
" That can't be Unaisa! Ki duba carotid artery din shi. He can't die just like that"
Allah sarki ita ta fini sakin layi, Jin bance komai ba se ta Kara sautin kukan Wanda ya Kara dagula min lissafi na jiyo ta tana fadin
" Mamaaa wallahi Abiey ya rasu! Unaisa tace ya rasu. Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!!"
Na kashe wayar Ina Kara sakin kukan rashin sanin halin da nake ciki, rashin sanin madafa. Kafin wani lokaci Kira ya dinga shigowa Amma bazan iya dauka ba, se Kuma Wanda suke da number ta Suka ta Kira na Amma na mutum daya na dauka wato mahaifiya ta
" Unaisa me ya faru da me gidan ki?"
" Ya rasu!"
Na fada Mata a hankali, ban Kuma Jin me tace ba, na rutse idanuna se Kuma ga Kiran Dada, uwata wadda ta kasance tare dani a dukkan halin da nake ciki, na dauka Amma banyi magana ba se sheshekar kuka da nake, hakan yasa ta saki salati tana fadin
" Yallabai da gaske ya rasu, ku Kira zuhra mu tafi"
Anty Aisha ta karbe wayoyin a hannuna, duk Wanda ya Kira se ta dauka ta bada amsa, a wañnan halin muka karaso Kano. Allah yasa nasan gidan shi Haka na kwatanta muka Isa, an taru sosae abinka da Dan siyasa da yake akan mulki. Aka shiga Dani ciki shima Haka gawar tashi. A makeken parlon kasa Mata ne a zazzaune kowanne da carbi a hannunsa, I began to think Ina Suka samu ko dama sunsan zai mutu ne, already Dada da Zuhra da Badi'a har da Yaya khulthum sun karaso, Zuhra na ganina ta mike ta nufo ni ta rungume ni, Haka kukan mu ya tsananta, seda Dada ta janye ni ta rungume ni tana buga bayana a kunnena tana fadin
" Sabr Unaisa"
Na kankame ta inajin kamar zuciyata zatai bindiga Dan abinda nakeji yafi gaban misali. zaunar Dani tayi aka dakko min hijab na yaye mayafin Dake jikina, Allah kadai yasan tururin da zuciayata take. Babu jimawa har an Gama shirya shi, aka shigo dashi akan muyi masa addua, kafata har sarkewa takeyi saboda jiri da nake ji. Na tsugunna gefen shi, ga Mamaa wato First Lady, Asiya, Muhammad da Kuma Ahmad se ni, mune ahalin nashi. Banda kuka Babu abinda nake Yi seda Mamaa ta dubeni tace
" Kiyi Masa addua Unaisa ita yake bukata"
Na kalleta, she sure is a strong woman, na saukar da kaina Kan gawar shi Sannan na fara nema Masa gafara, ina saka ran zai huta a kabarin shi saboda shi din mutumin kirki ne. Muna kallo Haka aka fita dashi zuwa makwanci, na saka kaina cikin hijab kamar Raina zai fita, ban taba sanin Haka zafin ka rasa wani yake ba, ko lokacin da mahaifina ya rasu naji Babu dadi nayi kuka Amma Bai Kai ko kwatan abinda nake ji yanzun ba. Ana Kiran sallar maghrib Anna ta karaso hankali a tashe, suka shigo Muna hada idanu da ita na Kara sakin kuka, ta janyo ni jikinta tana fadin
YOU ARE READING
UNAISA
RandomA yanzun maza da yawa suna shunning daga responsibilities dinsu, kamar yadda mahaifina ya auri mahaifiyata ya barta take daukar dawainiyar mu. Idan ya dawo ta samu ciki se ya tafi yayi shekara biyar Bai dawo ba, mu din mun tashi a hannun mahaifiyar...