🧕 UNAISA 🧕*F*
Ayshatuuu
Kafin ya tafi ya canja Mana gida, sede saboda tsadar gidan Bai bar Mata kudin abinci ba yace ai an fada Masa tana Yan buge buge Dan haka ta samu ta ciyar damu. Wannan abubuwan su Suka Kara harzuka Anna akan tsanar Baba, Bai taba sauke nauyij shi da Allah ya daura Masa ba, shi ya kasance kawai head figure ne a wañnan gidan. Anna kullum cikin Neman abin da zatayi da zai kawo Mata kudi take, ita ba gata ba balle ace wani zai kawo Mata dauki, duk duniya Inna Zulai kadai ke gareta, ita dinma Kam tana ta kanta. Kwatsam ana haka ta samu kwangilar yin rigunnan sanyi zuwa wata makaranta, Dake tunda na fara wayo inhar zata aje kwarashi to se na dauka na gwada tun tana hanani har ta kyaleni, ta siya min idan na Gama assignment dina se na dauka inayi. Wannan sanaar ma Bata ishe ta ba se take siyarda seasonings da spices Haka. A Haka nayi wayo Nuzla ma Haka, se ta saka ta a makaranta, idan muka dawo se mu tafi makaranar islamiyya. Dake na fara wayo idan na dawo se na dinga tambayar ta
" Anna Ina Babana? Anty tace zaayi PTA meeting kowa Baban shi yazo"
Se tace min nayi hakuri zaizo. Ana Haka Baba ya dawo da mummunan labarin rasuwar Baba Zulai. Anna kamar zata haukace saboda tashin hankali har yau Ina iya tuno kukan da ta dinga yi, a wañnan karon mukaje Masaya to zuwan ma ba me dadi ba mukai, seda muka kwana bakwai kafin muka dawo, ban manta ta taba Danni inada wayo sosae Kuma inada rike Abu ba nida mantuwa, of all my life lokacin na dauka ita ta Haifa Anna, kowa ya bude Baki zaice Hassana ce abar tausayi, ko Yayanta baa tausaya musu ba kamar Anna, dama su biyar ta Haifa dukka Masa Kuma duk sun girma, har da me zuwa Lagos. Tunda muka dawo Anna ta kwanta jinya shi Kam Alhaji Yahai dama can muka barsa, a wañnan jinuar da tayi min Sha wuya, da rokon Allah aka samu ta dawo Kan dugadugan ta ta daura daga inda ta tsaya.
A islamiyyar da Anna ke zuwa tayi wata kawa Anty Nana, wannan Anty Nana kusan kullum tana gidan mu saboda Allah ya Mata yawo, danma ita Anna ba Zama take ba Dan ta koma harkar Saida gwanjo, Amma Kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen ganar da Anna hanyar da zata bi, ta Kuma nausar da ita yadda rayuwa take a wañnan zamanin. haihuwar Hunainah wadda ta kasance auta Kuma ta hudu a gurin Anna, Wambai take zuwa tayi tsince tsince ta dawo gida ta siyar daga baya Kuma da likafa ta cigaba se ta siyo Kaya sosae ta jibge a gida, a shekarar da Hunainah ta cika biyu Ina Anna ta Zama wata daban Dan kuwa dealer Kaya take budewa ta siyar ta hada kudin ta. Ga saka da muke Mata, wadda makarantu da dama a kusa damu mu muke musu saka ni da Nuzla, Allah ya albarkaci kasuwancin matar nan se gashi ta hada kudi ta siyar da wani fili da ta taba siya acan bayan mu ta saya gida ta saka Yan haya. Wannan Anty Nana tace Mata ta Kara hada kudi ta saya gida idan ba Haka ba watarana zata rasa inda zamu zauna, kamar Wasa Anna ta hada komai da take dashi ta siyar tabi shawarar Anty Nana ta saya gida Amma a wañnan watan abinci ma se da kyar take iya siya Mana, dole ta samu wani gida take musu girki, idan zata dawo zata taho Mana da abinci muci. Mun Sha wahala sosae ba da Wasa ba, bana mantawa da weekend idan ta tafi gidan aikin ni Kuma se na karbo wankin mutane na zauna nayi na Kai can gidan na shanya su bani kudi, Wanda nake amfani dashi na siyawa Badi'a da Hunainah abinci da rana, mu Kuma se mu hakura har se ta kawo, ga Badi'a da son Madara yadda Bata San Babu ba, Duk abinnan Bata sani ba se watarana ta dawo unexpected ta sameni nida Nuzla min zage muna wankau, ranar seda ta fasa min jikina saboda dukan, a cewar ta ita zatayi Fadi tashi ta samo Mana Abu Amma mu we don't have that right, tun daga ranar ban sake wannan gigin ba. A wañnan shekarar komai yayi tsanani, sau da dama Zan ganta tana kuka idan Hunainah na kukan Yunwa a Haka a daddafe wata ya cika kudin aikin ta Suka iso ta siya Mana kayan abinci, da aka Bata kudin hayar gidan ta se ta koma sanaar ta ta gwanjo, rayuwa ta Dan Zama a bit stable.
Inada shekara Sha biyar, Nuzla nada Sha biyu, Badi'a na da tara ita Kuma Hunainah nada bakwai Haka muke. Wani safiya ta asabar anyi hutu both islamiyya da Boko. Tunda muka tashi Anna ta bar min sallahun ta tafi gidan aikin ta muyi abinci muci, duk Wanda yazo nemanta muce ta tafi ungiwa Dan ba kowa yasan tana aikatau ba, an dai San tana fita tun safe se yamma take dawowa. Hakan yasa muka dakko holiday homework din mu, na fara koyawa Hunainah tracing kafin na koma Kan Badi'a, na Gama da ita na dawo Kan Nuzla da tace min ta kasa composing poem da aka saka ta tayi, na zauna da kyar na Mata sannan na koma Kan nawa, Haka abin yake kullum, Allah ma yasa dukkan mu kokari ne damu shiyasa wahalar take raguwa. Bayan mun Gama Nuzla ta hado kayan da mukai amfani dashi kanana ta wanke mana tas ni Kuma na daura Mana danwake da zamuci for breakfast, kawai se muka ji sallamar Baba, dukka muka amsa ya dawo bayan shekara da shekaru. Muka Masa sannu da zuwa ya shige daki abin shi ya barmu. Nuzla ta dubeni tace
" Adda ya zamuyi Anna Bata nan"
Nayi shiru Ina tunani nace
" Kawai muce ta je suna ko?"
Se muak gyada Kai, seda na sauke abinci sannan na bawa Badi'a ta Kai masa, se yace tace min nazo, na saka hijabi na Dake Kan igiya na Shiga dakin Yana zaune Yana ta jefa danwake a bakin shi, a raina nace kamar ya bada kudin flour se wani ci yake.
" Ke Baki San kice min sannu da zuwa ba? Yara duk Babu tarbiyya"
Nayi kasa da kaina Ina jin Babu dadin yace min bamuda tarbiyya, a ganina duk kokarin da Anna keyi ganin ta tarbiyantar damu daidai Amma shi da ko kadan Bai bada gudunmawa ba zaice Haka, se hawaye ya fara zubo min, Bai ma lura ba yace
" Ina iyar ku?"
Na dan diririce Ina share hawayen fuskata nace
" Ta...taje suna can Brigade"
.
Ya gyada Kai yace na tafi, Babu musu kuwa na fice Ina sakin ajiyar zuciya. Seda muka Gama cin abinci sannan Badi'a tayi wanke wanke a hankali kamar marar laka, Haka take ita din ajebo ce of highest order! Shiru shiru Anna Bata dawo ba har shida shi Kuma se tambaya ta yake Yi se yaushe zata dawo nace ai bansan me yasa Bata dawo ba. Hankalina ya tashi ganin har Bayan ishai, har Hunainah da Badi'a sukai bacci Bata dawo ba se wajen Tara naji sallamar ta, nayi wuf na tafi zaure , a matukar gajiye Haka fuskarta ta nuna nace"Anna me ya faru yau kin dade?"
Ta danyi tsaki tana Mika min kayan hannun ta tace
" Wallahi aikin ne se a hankali, me gidan ne yayi Baki Dole seda muka Kara daura wani abincin"
A hankali nace
" Anna wannan mutumin ya dawo"
Tace
" Waye?"
Nace
" Baba fa"
Se ta dafe kirjinta nace
" Amma nace Masa suna kikaje, mu shiga Kar yaga na Dade"
Mun jiyowa se muaki kicibis da bawan Allah ya nade hannun sa Yana kallon mu, ya saka hannu ya kwada min marin da shi ne karon farko Kuma Karo na karshe da aka marenu, kafin nakai hannuna, Anna ta riko ni tana fadin
" Me yasa zaka mare ta? Laifin me tayi maka"
Ya Mata wani bansan kallo yace
" Ke kin Isa kice wani Abu, mayaudariya Maci Amana. Dama ance fita kike Yi idan bana nan. Ga Yara nan dukka sunyi wata irin Kama.."
" Yahai! Ka tsaya da duk abinka akai na Amma karka Bata min nasabar Yara na, me yasa bazan fita ba? Ka bar Mana abinda zamu ci ne? Ka tafi uwa duniya ka barni da Yara da auren ka. Wallahi Yahai ko zaka Fadi ka mutu a gabana bazan taba yafe maka ba"
Ya daga hannun sa ya dauke ta da Marin da seda ta sake ni, na saki kuka Ina rike hannun ta ji nayi duk duniyar tana juya min,
" Na fada Yahai, bazan yafe maka ba Koda shi kadai ne abinda zaka je aljanna wallahi se de kaje wuta, idan kana ganin banida gata banida kowa ka sani Allah shi ne gata na, Kuma zakI daka sanin abinda ka Mana"
" Tunda har kinsan na fada ki fada to se ki je na sake ki saki daya, saki biyu!! Babu ni Babu ke, ki tafi can da Yayanki"
Wannan shi ne mafarin komai, shi ne silar bunkasar mu yayinda ta Zama ta rushewar sa!
Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
YOU ARE READING
UNAISA
RandomA yanzun maza da yawa suna shunning daga responsibilities dinsu, kamar yadda mahaifina ya auri mahaifiyata ya barta take daukar dawainiyar mu. Idan ya dawo ta samu ciki se ya tafi yayi shekara biyar Bai dawo ba, mu din mun tashi a hannun mahaifiyar...