H

197 37 1
                                    


🧕 UNAISA 🧕

*H*

Ayshatuuu

*Have you paid for Unaisa? If no then hurry and do so as we only have two pages to take down the free pages. Thank you for the patronage.*


Bayan sati biyu ranar asabar na shirya tafiya zuwa hadejia, Dan yin exams dina. Tun dare Anna ta sallameni da komai Nima na hada komai da zanyi amfani dashi. Hatta kayan da Zan saka seda na dakko Dan Haka da sassafe Ina tashi nayi wanka sannan na dakko atamfa red me adon spring sea green da purple. Seda na shafa powder nasa khol fuskar nan tawa smooth saboda yadda nake kula da ita bana son ko Abu daya ya taba ta, kurji daya idan ya fito min se na tadawa kowa hankali da korafi, shiaysa nake maintaining jikina musamman fuskata. Na shafa balm Wanda yasa lebena kyalli na yafa veil na zura flat shoes Dina na dauka folder se jaka. Anna na kokarin fito damu Koda kayan mu basuda tsada Amma tana iyakar kokarin ta akan mu, shiyasa ba zaka taba ganin alamar ko muna cikin wahala ba, balle yanzun ma Babu wata wahala da muke Sha, Anna na samu sosae se godiyar Allah. Seda ta rakani Tasha na hau mota sannan na ta koma gida, shi ne lokacin farko da nayi tafiya me tsawo ni daya Dan Haka duk bayan mintina ashirin se ta Kira taji Ina Ina, gashi ni bansan hanya ba se tace na tambayi driver din mana, tun Yana fada min har yace Wai na ishe shi Haka. Wani Dake gefena yasha kufta ya kafa hula zanna bukar ya dubeni Yana murmushi yace

" Alama baki taba tafiya ke kadai ba ko?"

Na Dan Bata fuska tare da gyada Kai na, yayi murmushi yace

" Dama kyawawa irin ku ai treasure ne"

Wannan karon ban kula shi ba, na saukar da kaina Ina Kara haddace formulas din physics. Muna zuwa hadejia aka sauke ni a Tasha, shima gayen ya sauka ya dubeni Ina kokarin matsawa gefe yace

" Ina zakije?"

Na Dan yi shiru se Kuma nace

" School of nursing zanje"

Ya gyada kan shi sannan ya samar min napep, bayan na Shiga ciki shima ya shigo ya zauna gefena, duk surutun da yakeyi ko uffan bance Masa ba Amma shi din Bai gajiya, he's so annoying na ayyana a raina. Har gate din school Suka kaini, na sauka Ina Nemo Masa kudi yace ai na bayan ya biya, na kalleshi nace

" Nagode Allah ya saka da alkhairi!"

Ya gyada Kai ya min waving tareda bani card yace na kirashi. Na gyada Kai Suka wuce ni Kuma na nufi cikin makaranta, banma tsaya wani duba card din ba na wullar dashi cikin katon drum din shara. Screening aka farayi se venue aka bani na exams din, ana bani questions dina na fara Babu Wasa. Tun Ina cikin exams din Naga alamar hadari ya hado, sede is More of iska than hadarin ruwa, gashi duka garin ya daure yayi dum Babu dadi yanayin. Se na fara attishawa da Dan karamin tari, a Haka na Gama nayi submitting sannan na fito, Amma se naji kirjina yayi min nauyi har numfashina suna ciccikowa, ga gajiya ga Kuma Yunwa, ga fargaban hadarin dake hadowa, kafin wani lokaci duk na gaji Amma a Haka na cigaba da tafiya zuwa gate, Ina zuwa mutane anata tafiya ga motoci na lodin garuruwa, na nufi inda naji ta Kano Dan shiga na tafi se naji an dafa ni, nayi saurin juyowa se Naga wannan Zahra din, tana min murmushi tace

" Yayar Hunainah!"

Nayi murmushi Nima nace

" Zahra ko?"

Ta Dan Bata Rai tace

" Gaskiya I'm hurt! Kin manta sunana?"

Na rufe fuskata da hannayena nace

" I'm sorry! Tuna min Dan Allah"

Taja hannuna tace

" Sunana Zuhra Ismail, nazo nan pre test. I just hope kema Haka?"

UNAISAWhere stories live. Discover now