G

184 29 1
                                    


🧕 UNAISA 🧕

*G*

Ayshatuuu


Se lokacin ta gane abinda Anty Nana je nufi da maganar ta, ta Kama hannuna muka shiga ciki Ina kuka, tana Yi Nuzla nayi, ta kwashe kayan mu Ina Taya ta, a Daren bamu runtsa ba ta kwashe kayan ta, ta Jirge gado da komai nata asuba nayi Muna sallah ta dauki mayafin ta ta fice, kafin bakwai ta dawo da me mota da Kuma Anty Nana se makwabciyar mu umma da suek shiri ta shigo, munata baccin gajiya a parlor, seda ta kwashe komai nata tas sannan ta kwashe mu muka tafi, Allah ya rufa Mana asiri ta saya wannan gidan da sede muje karkashin gada mu zauna. Muka koma sabuwar unguwa anan cikin Kano, gidan karami ne me dakuna biyu se bandaki da Kuma kitchen kwaya daya, se shago Wanda kofar shi take a waje. Anna tasa aka rufe kofa aka dawo da kofar ciki, tsakar gidan karami ne da rijiya ta ruwa. Haka Suka Taya ta ta shirya komai da se yamma lis sannan aka Gama Suka tafi. Daki daya tasa kayan gadon ta da wardrobe, dayan shagon tasa kujerun ta, se dayan tasa Mana katifar mu da jakunkunan makarantar mu. Da daddare muka kwanta, duk farkawar da nake tana zaune a sallayya tana kuka, seda mukai wajen kwana uku sannan ta hada kanmu muka tafi Masaya bisa shawarar Anty Nana. Muna zuwa ko karasawa gidan dagaci bamuyi ba, aka dinga Mata Ihu tsintacciyar mage Bata mage,Ashe dama mu din ba yayan Yahai bane yawo takeyi, Haka ta dinga kuka muna Taya ta ta juyo muka dawo Kano. Ka guji macen da akai wa laifi. Kafin mu koma makaranta ta rage damuwar ta, ta samo Mana makaranta sabuwa kusa damu, kullum ta zauna se tace Mana

" Unaisa, Nuzla, Badi'a da Hunainah.."

Wadda ba lallai tana fahimtar maganar da Anna keyi ba.

"...Duk wannan abinda nakeyi Dan ku nakeyi, Ina son kuyi karatu ku fitar Dani kunya, Ina son yadda mahaifin ku ya wulakanta ku, dangin shi Suka ki karbar ku, kusa su zo da kansu su roki gafarar ku Yayana, ku wanke min bakin cikin shekara goma Sha shida na kunsa a wajen mahaifin ku. Daga yau ni kawar ku ce, ko menene kuzo ku fada min"

Wannan kalaman nata seda muka haddace shi a kwakwalwar mu, se ya zamana rayuwata gani nake Dan ita nake, komai nake se na tuna wannan maganar tata. Ance zafin nema baya kawo samu inji BAHAUSHE, gaskiya ba Haka bane Dan kuwa kafin shekara ta rufa Anna tayi gaba se de ka tada Kai kallo, mussamman kasancewar mu farkon tarewa a unguwar ya zamana kusna ta kafa kanta a Sanaa. Kayan gwanjo har daga saudiyya ake Aiko Mata ta Zama babbar mace mu kanmu se rayuwa tayi afuwa sosae, Amma kullum tana tuna Mana kada mu manta wahalar da muka Sha, kada Kuma mu manta kanmu.

Bayan shekara uku

Na cika shekara goma Sha takwas, na zama young adult which always wanted to, kullum so nake ace min ai shekara ta Sha takwas. Na Gama secondary school Dina tsaf na Kuma fita da flying colors dan kuwa kaf set din mu Babu Wanda ya samu grades din da na samu a waec. Dama banyi neco ba. Saboda Anna tace tana da yakinin zanci neco. Sede inda aka samu mistake banyi jamb ba, seda Dan Anty Nana Yaya Yusuf yazo sannan yake tambayata nace ai banyi ba, bana mantawa shi ya siyo min form din school of nursing hadejia da Kuma form din school of midwifery Kano. Yace naje nayi pretest da interview duk inda naci kawai se naje nayi.

Na girma sosae, na Zama yanmata wadda dauke idanu akaina se Wanda yayi da gaske, banida tsayi sosae Amma tsawona is average, no macece chubby saboda ni ba a rame nake ba, hips dina tamkar Wanda aka hura shi Haka yake abinda ke daukar hankalin maza da yawa suke nuna suna Sona, and I hate that fact. Ba laifi I'm busty dukda ba sosae ba Amma ba zaka ce bani dashi ba, ni din macece cikakkiya. Fuskata nada tsawo, inada gashi me yawan gaske sede tauri ne dashi sosae, banida goshi Dan ta gefen gira ta gashin kaina a hade suke, gashi ne kwance a forehead Dina Wanda ko Yaya na daura dankwali se ya fito, gashin baya rufuwa, inada asalin kamanni na Fulani, dogon hanci, matsakaitan idanu farare tas, bakina bashida girma Kuma ba karami bane, hakorana farare ne tas a jere kanana, a jiki inada wushirya siririya. Ina da sanyin Hali, banida hayaniya ko tashin hankali, duk wani Abu Dana ga zai bani matsala Ina koakrin ganin na kauce Masa. Bana fada zaiyi wahala kaga ance anyi fada Dani Amma Kuma inada ruko na gaske, I forgive but I don't forget, inada saurin kuka Wanda ake cewa it's a sign of Innocence, hakane indai nai kuka to inada gaskiya Amma idan nayi shiru to gaskiya nayi laifi, ni mutum ce me sallah, a ibada sallah na daya daga cikin abinda nake finding joy and peace a yinta, Amma azumi da kyar nake sitta shawwal bayan Ramadan. Wannan gaba daya itace Unaisa.

Anna ta dawo na nuna Mata forms din da na riga nayi filling na Kuma Yi attaching dukkan credentials din daake bukata a ciki. Ta karba ta jujjuya sannan ta dauki wayar ta ta Kira Yaya Yusuf tayi Masa godiya sosae. Washegari ni da Anna da Hunainah muka je Danbatta mukai submitting da sati ya zagayo mukaje hadejia muka Kai. Mun fito daga school din muka wuce tasha, muna zaune cikin tashan Hunainah Tasha guava t Bata min veil dina, tunda Anna ta kalleni ta gimtse fuska, na Bata Rai nace

" Saboda Allah Anna kiga abinda yarki ta yimin?"

Hunainah ta saka hannun ta tana goge min Bata San Kara Bata min take ba, na saki karamar Kara nace

" Anna kiyiwa Allah ki ce yarinyar nan ta Bari Mana"

Ta dubemu tana dariya tace

" Hunainah daina kina batawa Adda mayafinta"

Ta kalleni da idanun ta irin nawa tace

" Sorry Adda!".

Na shafa kanta nace

" It's ok Darl"

Anna ta dubeni tace

" Wacce kike so a ciki makarantar?"

Na danyi murmushi nace

" Idan Zaki yarda nafi son hadejia, nayi nursing kawai"

Se tayi murmushi tace

" Nasan a duk inda kike Zaki kula da kanki Dan Haka Babu damuwa Allah ya sa ki samu wadda kike so din"

Nayi murmushi nace Amin. Se hirar mu ta katse saboda shigowar passengers guda uku, babban mutum Haka shekarunsa sunfi arbain se wani guy da yake a late 20s dinsa, da Kuma Yar budurwa da Bata fi saa ta ba. Sukai sallama suka shiga, seat din dake gaban mu na mutum hudu yace ya siya Dan Haka akace mota ta cika Dan muma Anna seat din baya ta siya, ga dama akwai passengers biyu a gaban motar. Budurwar ta fara juyowa ta gaida Anna hakan yasa nima na gaida Wanda nake tunanin mahaifinta ne da Yayanta. Sunata Hira har muka Isa Kano, tun kafin mu Isa guy din ke waya Yana fadin

" Ahmad kazo park mu wuce, wallahi motar mu ce ta samu matsala tun a hadejia"

So ana aje mu duka muka sauka, tazo ta taba Hunainah tana murmushi tace

" Ya sunan ki baby?"

Ta kalleni tace.

" Yar Amie"

Nayi dariya nace

" Sunanta Hunainah"

Se ta shafa kanta daidai lokacin Baban kece Mata

" Zuhra Ahmad yazo"

Ta Mana waving hannunta Suka shiga katuwar mota baka wuluk Suka wuce, na lumshe idanuna na tare Mana napep sannan muka wuce gida. Muna zuwa Nuzla tayi girki ta Gama Amma gidannan gaba daya upside down. Tunda muka shiga Anna ta hade fuska, Badi'a tana zaune da wayata Dana bar musu Koda zasu kira mu ko mu Kira su. Tana ta danne danne ga Waka ta Kure volume tana ji. Tana jin sallamar mu ta mike Dake Anna ce a gaba tayi kanta zata rungume ta, wata harara data sakar Mata yasa ta tsaya, se ta sunkuyar da Kai

" Anna sannu da zuwa!"

Bata amsa ta ba ta wuce ciki,na dubeta nace

" Badi'a ya gidan"

Ta Bata fuska tace

" Kuma Anna se Bata Rai takeyi"

Na kalli tsakar gidan nace

" Ki kalla yadda kukai da gidan Dole ranta ya baci"

Daga Haka na tsaya nayi alwala Ina Shiga naji tana ma Nuzla fadan sun Bata Mata gida,su kamar ba Mata ba Basu San yadda zasu gyara gida ba. Nidai na tada sallah sannan na idar na fita tsakar gida muka hadu da Nuzla muka gyara gidan tas sannan ta zubo Mana abinci, Anna na daki na bita nace

" Anna kizo kici abinci, kiyi hakuri an gyara gidan"

Ta Gama saka top din dake hannunta tace

" Yanzun fisabillilahi Adda ya kamata ace sun bar gidannan kacakaca Haka Kamar bola?"

Nace

" Kiyi hakuri ba zata Kara ba"

" Wannan me kunnen kashin zata ji ne"

Haka na lallaba ta mukaje muka ci abinci sannan muka zauna Hira. Haka rayuwan yake tafiya har aka Kira mu zuwa pretest a danbatta. Wannan karon ni kadai naje nayi sannan na dawo.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.

UNAISAWhere stories live. Discover now