🧕 UNAISA 🧕
*E*
Ayshatuuu
Nasan zuwa yanzun Kun kosa kusan asalin Labarina, zaku so kuji wacece Anna? Haka Mamaa Haka Dada? Su Ahmad da dukkan role dinsu cikin rayuwata. Sunana Unaisa Yahya, mutane da yawa sukance Wai a gurina Suka fara jin suna Unaisa, ni kaina Bayan ni me sunan baifi sau biyu na Kara jin me irin sunana ba.
Mahaifina Dan wani kauye ne ko Kuma nace gari a Masaya Dake karkashin Birnin kudun jihar jigawa. Mahaifina sunan shi Alhaji Yahya tun Yana saurayi sunan shi kenan, Dan bashida aikin da ya wuce yaje Saudi Arabia yayi shekara uku, hudu har ma biyar sannan ya dawo. Hakan yasa duk garin kowa Alhaji Yahai ake ce Masa memakon Yahya din. Mahaifiya ta sunan ta Hassana tace Mana ita Yan biyu ce Amma abokin tagwaita Kar tata shi ya rasu. Su biyu ne gurin iyayen su itada Baba Zulai a Wanda ta sani. Tace Mana dukkan Yan uwan ta idan aka haife su rasuwa suke, Amma akwai yayun su biyu Wanda Suma Basu San su ba, ba Kuma ta San inda suke ba, su biyu kadai Suka rage. Iyayen Anna Fulani ne Wanda ke yawo a duk inda Suka samu shanun su zasuyi grazing. Suna tafiya Allah ya kawo su Masaya lokacin Zulai Bata fi shekara goma Sha biyu ba, da suka zo sukai camping can bayan gari ita Kuma tana Dan shiga gari da sauran Yara a Haka dagaci ya ganta ya aure ta. Lokacin ana goyon Anna, da lokaci yayi suka kada shanu suka tafi Suka barta. Se bayan shekara hudu lokacin Yayanta biyu sannan suka dawo, sunzo wucewa, . Zasu tafi dagaci ya samu da kyar ya karbe Anna with the hope cewar idan Anna na nan zasu dinga zagayowa suna ganin su. Suna tafiya baa fi kwanaki uku ba Wanda dagaci ya aika ya gano hanyar da Suka dauka ya dawo yace iska akai sosae wadda tasa da yawa Suka rasu Kuma ciki harda kakkanin mu. Wani maganar ta girgiza kowa se Anna ta tashi hannu Inna Zulai ita ce uwarta da ubanta da komai nata. A Haka ta girma hannun su Babu makaranta da aka saka ta har ta shekara Sha biyar aka dinga zancen Bata samu miji ba, Anna kyakyawa ce ta gaske tana da gashi Haka Kuma karamin jiki me da ita kamar yadda Inna Zulai take. Kana kallonta kaga bafullatanar asali. Fara ce tas har yellow yellow take. A shekarar Alhaji Yahai ya dawo daga saudiyya Bayan ya shafe shekaru acan. Dagaci Baffa ne a gurin shi, da kakata da ta haifi Yahai da dagaci uwa daya uba daya suke, Kuma ita din uwar dakin Inna Zulai ce Dan Haka Yana neman auren Anna Babu wani ja aka hada su auren. Har muka girma nasan Anna Bata son Babana, ban taba ganin ta saki jiki idan tana tare dashi, gashi ni yarinya ce me bin kwakwaffi, I observed kamar spy Haka nake.
Akayi aure Anna da Baba, da farko se ya ajeta a masaya tayi wajen sati uku se ana hudu sannan ya tattara ta Suka dawo sauna. Anna Bata son shi yadda me karatu bazai dauka ba, a masaya sukance idan yazo zance se da itace me bakin wuta Inna Zulai ke korata, Kuma saboda sanin batada kowa se Inna yasa ta hakura ta aure shi. Bata fi watanni uku ba Sega ciki ya fito, gidan da take zaune gidan haya ne daki daya ya Kama ya biya kudin shekara biyu, cikin na wata biyar ya fara Shirin komawa saudia kamar yadda ya saba, da ya fada Mata se tace ita ta yadda ya maida ita masaya tunda nan Babu wani Dan uwa da take dashi. Yace shi baiyi niyya ba Kuma ita Bata Isa ta saka yayi hakan ba, Haka kuwan ya tafi ya barta anan, ko hanyar masaya ma Bata sani ba. Haka ya barta ya tafi wata uwa duniya. Guzurin da ya bar Mata Bai Kai lokacin haihuwa ta ba ya Kare, zuwa lokacin tayi sabo sosae da makwabta Dake Kuma ta iya sakar hannu se tunda tazo Bata zauna ba take saka, wannan kudin sakar take sakawa cikin banki a Haka har Allah yayi ta haihu. Wata makwabciyar dakinta dattijuwa ita ta zauna da ita har ta haifeni, kafin ya tafi ya fadawa makwabcin shi yadda zaayi a sanar a masaya cewar Anna ta haihu. Washegari kuwa se gasu sunzo yuya guda. Inna Zulai kamar ta Yi me saboda farin cikin haihuwata. Ranar suna aka saka min Unaisa kamar yadda yace Mata. Ragon suna da koami daga can Suka zo dashi. Kama nake sosae da Anna Amma Kuma fatata se tayi duhu irin ta mahaifina. Se ya kasance ni ce daban da sauran, Dan dukka kannena farare ne tas dasu. Bayan tayi arbain aka kaita Masaya ta kwana biyu sannan ta dawo, shiru Babu Baba Babu dalilin shi, kowa yasan kayan sanyi suna ci ne kawai lokacin sanyi sede idan kana da wani da kake bawa, hakan yasa ciniki ya tsaya cak, ta fara tunanin da me zata zauna wannan dattijuwa Baba Rakiya Anna na fadar ta, tana yawan cewa ita din ba karamar taka rawa tayi a cikin rayuwar ta ba. Ita ta fara koyawa Anna yadda zata tashi a tsaye, tace Mata tunda mijin baya nan bazaiyi ba to ita Anna ya kamata tasan yadda zatayi ta nema na kanta. Shi ne ta fara wankau, ka kawo kayan ka ta wanke maka se ka biyata, dashi zata yi cefane ta Adana wani. Idan ka kalleta se kasa Baki ka hureta saboda Rama, wahala da talauci. Haka tayi rayuwa har na shekara da rabi, lokacin kudin haya ya Kare kwatsam Sega Baba ya dawo, ku kalla wajen shekaru biyu. Ya siya kayan abinci, ya Kara biyan kudin haya baiyi ko wata ba ya Kara komawa, a wañnan Karan Bai dawo ba se Dana cika shekara uku lokacin Anna Sanaa take iri iri Dan ta biya min kudin makaranta, a cewar ta yadda batayi karatu ba, Bata San dadin karatu ba to nidin bazan Yi Haka ba. Wata private school cikin unguwa ta sakani tana biyan kudin. A Haka ya dawo shima kamo shi akai aka dawo dashi, to wannan shine yayi shekara daya Bai koma ba Yana hada kudin da zaiyi igama idan yaje. Kafin ya tafi Anna ta haifa Firdausi Nuzla. Ko arbain ba tayi ba Baba ya shura takalman sa ya koma. Ko zaman da yayi na shekara bana yarda dashi kamar ma tsoron shi nakeji, komai nawa Anna ce, ko nazo zanyi Mata magana muka hada idanu dashi to tabbasa na fasa maganar.
Bayan ya shekara hudu ya sake dawowa, kuyi imagining duk wata wahala da bawa zai iya Sha, to Anna Tasha akan mu, ya maida ta tamkar Baby making machine, idan yazo Yana tafiya ciki zai bayyana. Bayan ya dawo min Kara girma ya Kara komawa ya Barta da ciki, shi ne aka Haifa Badi'a. Bai dawo ba seada ta shekara biyu lokacin Anna ta samu cikin Hunainah.
Wata safiyaKafin mu Gama shiryawa se gashi ya fito daga daki, Nuzla da Badi'a Suka gaishe shi Amma ni Kam ko kallon shi banyi ba seda Anna ta zungure ni hade da harara ta sannan nace
" Ina kwana?"
" Lafiya Lau Unaisa! Har Kun shirya zuwa makaranta?"
Nace
" Mhm!"
Yace
" To Allah ya bada saa, kafin ku dawo na koma no"
Nidai bance komai ba har muka gama na dakko jakunkunan mu zamu tafi, na kalla Anna nace
" Anna zamu tafi, jiya kin manta Baki bawa Badi'a kudin crayons din ba"
Ta mike da sauri tana fadin
" Mantawa nayi wallahi,Allah yasa baa dake ki ba?"
Ta gyada kanta, ta wuce daki Dan dakko min, Baba ya saka hannu a aljihu ya Ciro uban kudi Yan 500 notes da se Dana zare idanuna Dan mamakin yawan su. Ya zaro daya sannan ya maida sauran ya Miko min daya yace
" Gashi nan kuje ku saya sauran se ku saya Abu a Hanya"
Na girgiza Kai nace
" A'a"
Se ya tsaya sororo Yana kallona yace
" Amshi Mana!"
Na Kara girgiza Kai daidai fitowar Anna se ta tsaya tana kallon mu, Nuzla tace
" Anna tace kada mu dinga karbar Abu a gurin mutanen da bamu sani ba"
A take Naga fuskar shi ta canja, he looks embarrassed, yaa kalla Anna sannan ni se Nuzla se Badi'a, Anna ta Mika min tace
" Adda ku tafi kinji, ayi adduar fita daga gida sannan Dan Allah ana tashi ki dawo kunga yau laraba akwai hadda a islamiyyar"
Na gyada Kai na Ina fadin
" To Anna inshallah se mun dawo"
Ta bi bayan mu tana fadin Allah ya muku albarka. Haka kullum take ita din uwar arziki ce. Bayan ta dawo yayi Mata rashin mutunci sannan ya tattara kayan shi ya tafi. Ko da muka dawo se muka cigaba da harkar mu Babu Wanda ya tambaye ta inda yake a Haka rayuwa ta tafi, abin bakin ciki tafiyar shi da wata Tara ta Haifa Hunainah, wannan karon Babu Wanda yazo ko daga masaya ma, itama batayi taron suna ba, a cikin mu Babu wadda ta samu less kulawa ma irin Hunainah, duk yadda muka shaku da Badi'a to abin ya wuce tsakanina da Hunainah, ni ce komai nata, wanka goyo, feeding dinta da komai ni ce. so da ta fara magana ma da suna na ta fara fada, take cemin Amie. So akwai wayanda har muka girma Yar Amie suke ce Mata
Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 First Bank of Nigeria A'isha Hassan kwalam and send evidence of payment to 09063467258.
YOU ARE READING
UNAISA
RandomA yanzun maza da yawa suna shunning daga responsibilities dinsu, kamar yadda mahaifina ya auri mahaifiyata ya barta take daukar dawainiyar mu. Idan ya dawo ta samu ciki se ya tafi yayi shekara biyar Bai dawo ba, mu din mun tashi a hannun mahaifiyar...