1

99 5 0
                                    


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
             (The hunch back girl)

*WATTPAD*
@NoorEemaan

*Hoorain Mai Kusumbi is not for free, it's 300 via, if you are willing to pay, here is the account details... 2261488155 Rukayya haruna zenith bank*.
*Then send evidence of payment to this number 07082281566*

_*hoorain zai zo da wani salo na daban wanda baku taba gani ba, novel din na daban, ya sha bambam da duk wani Novel nawa, ban ce alkamina yafi na kowa ba, amma alkalamina na daban ne, just follow my pen, and i assure you that you Will never regret*_

In the name of Allah, most gracious, most merciful.

*Free page*

Chapter 1️⃣⏩2️⃣

*BUKAVU BARRACKS KANO*

Babban barikin sojoji ne mai matukar girma, yana ɗauke da waje je daban-daban, yayinda kabilu mabambamta hadi da addinin ne a cikin barikin, sosai suke zaman lafiya ga hadin kai gwanin sha'awa.

Ko wani soja da iyalan sa da area da suke zama, ya danganta da ranka(muƙamin) Mutum.

Misali akwai officers mess, batcher, White House, da sauran su, haka ma akwai asibiti da suke kira MRS duk a cikin barikin.

Zaune yake a officer dinsa, in da aka kawata office din da kayan k'awa irin na sojas...
fuskar sa a murtuke yake amma hakan bai hana kyawun sa buya ba.

Kyakkyawan matashi ne mai shekaru talatin da biyu a duniya, sanye yake da kakin soldier da yayi matuƙar yi wa farar fatar sa kyau, duk da a zaune yake amma hakan bai hana mutum ya gane cewa shi din dogo ne ba, mai fadaddar kirjin, a takaice dai giant wanda ya sha training sosai.
Gashin kansa mai tsayi ne, har parking yake, domin yazo masa har saman kafadun sa, sai dai bai barin shi a baje, always Yana parking gashin.

Sajen sa mara yawa kwantacce ne daya kara masa wani sirrin kyau, zagayayyen fuska ne dashi mai dauke da cikakken gira hadi da eyelashes masu yalwa, hacin sa dogo ne mai tsari, idanun sa madaidaita ne masu ɗauke da eyeball sky blue, sai bakin sa madaidaici red color, a takaice dai he's damn handsome!

System ce a gaban sa yake operating da hannu biyu at the same time cike da kwarewa, yayinda lokaci zuwa lokaci yana ɗan sipping coffee dake kan table din shi, sam bai damu da abinci ba, mafi yawan lokuta yafi gane wa coffe.

Alamun sako ya gani an Turo ta Gmail din shi, hakan yasa bayan ya gama abinda yake ya shiga.
sunan field marshal ya gani, wanda hakan ya nuna cewa shine ya Turo masa sakon, a nutse ya karanta komai in less than five minutes duk da yawan rubutun...

Hannu ya sa ya shafa kwantaciyyar sumar sa, sanan ya furzar da iska daga bakin sa hadi da lumshe rikitattun idanun sa.

Amsa ya rubutawa marshal da cewa ya gan sakon, sannan ya kashe system din gaba daya

mikewa yayi tsaye... Masha Allah dogo ne sosai wanda ya dace da tsarin halittar jikinsa, hular sa ta sojas ya saka wanda ya ƙara masa kyau sannan ya saka wani brown sunscreen (gilashi) ya dauki wayar sa ya nufi hanyar barin officer ɗin cikin tafiyar sa mai cike da izza, takama, hadi da burgewa...

Jefi-jefi yana haduwa da sojas daya girma a rank suna gaishe shi cike da girmamawa, hannu kawai yake daga musu ba kuma ɗan wulakanci ba, sun san halin shi na rashin son magana shiyasa basa damuwa.

Haraban office din na da matukar kyau an kawata shi da flowers masu ban sha'awa green sai kamshi furanni suke ga Nigerian flag da wasu tambari na sojas da aka kawata Haraban da shi...

Wajen hadaddiyar motar sa kirari Bugatti ya nufa, ya buɗe murfin ya fada ciki, har ya ta da motar ya ji an K'wank'waso glass din motar.

Zuge Glass din motar ƙasa yayi, kasancewar ya rufe kuma tinted ne...

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now