6

53 1 0
                                    


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
(The hunch back girl)



*Korafi ya karbu, zan kara yawan typing. Ina godiya sosai masoya da yanda kuka karbi littafin Hoorain, ku cigaba da bin alkamina domin jin yadda labarin zai kaya, wannan littafin ya sha bambam da duk wani Novel nawa, sosai na jima da son yin book din nan tun a Novel din papi, Amma Allah bai nufa ba sai yanzu, Muje zuwa... Noor na muku sahihiyyar kauna*💕😘

_written by NoorEemaan_✍️

Chapter 1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣

_________Mintuna goma masu kyau ya dauka a tsaye yana murza hannun sa cikin na juna, duk wani tunanin sa ya tsaya cak, zuciya da idanun sa ke son ganin ta, duk yanda ya kai ga son bijirewa zuciyar sa ya kasa... Kamar wanda ake bawa umarnin haka ya ga yana jefa kafar sa cikin gidan, sautin bugun zuciyar sa na sauyawa...

Sai daya tsinci kansa a dan soron gidan su kana hankalin sa ya dawo jikin sa, a ransa ya furta
"Hamdan me hakan kake yi akan mace? Please come back to your normal self, this is not you"...

Cikin sauri ya juya domin barin gidan... saura bai fi taku uku ba yace an ce

"waye nan?"

Runtse rikitattun idanun sa yayi, kana ya ware su ya juyo ga Mami dake tsaye, duk da yanayin mai wuyar fassaruwa da yake ciki ba zaka taba fuskantar hakan a saman fuskar sa ba.

"Me zaka ce kazo yi cikin gidan su?"
Wata zuciyar ta tambaye sa.

A hankali ya tako ya zo gabanta, cikin girmamawa ya dan dukar da kan sa yace

"Good morning ma" domin a lokacin sha biyu saura.

" Good Morning, lafiya dai ko?"  Mami ta fada Cikin sakin fuska, a ranta tana mamakin Meye kawo shi gidan su?

Ta bangaren hamdan ma ya dan yi mamakin jin Mami tayi Hausa, kasancewar kallo daya mutum zai mata ya gane cewa ita din ƙabilar igala ce,  amma bai nuna ko alama ba.

Kamar yadda ya saba yake kuma dabi'a a gareshi ya buɗe bakin sa kamar bayason magana yace "nazo ganin ta ne" 
ya ji ya fadi maganar da bai san ta ina ya fito ba.
A ransa yana fatan kada ta kara masa wata tambayar, domin wanna karon bai da wata sauran amsa.

Dariya ya bawa Mami, amma bata yi ba, ta maimaita abinda ya fada  " nazo ganin ta ne"  ta lura kamar bai da son yawan magana, 
"shigo daga ciki" Mami tace yana yin gaba, ta san cewa bazai cuce su ba, domin yanayin sa bai yi kama dana mugu ba, duk da ance mugu bai da kama. ga agogon soja dake hannunsa wanda ya tabbatar mata da cewa yana daga cikin sojojin da  Allah ya aiko suka kawo musu karshen azzaluman yan ta'addan nan.

****

Da kallo Hoorain dake zaune kan yagagiyyar tabarman su ta bi su da kallo,  hannunta cikin sakin masara da man ja Sai yaji... Kasa hadiye na bakin ta yi sakamakon ganin Mami da wani Balarabe a tunanin ta sun shigo...
Da kallo ta bisu, mamaki fal fuskar ta,  cikin Yaren Igala tace Mami tace "Hoorain wajen ki yazo"
Duk da tayi mamakin abinda Mami tace amma bata nuna ba, cikin ladabi tace

"toh Mami".

Daga  haka Mami ta shige daki abun ta.

Sauke idanun ta kasa tayi, cikin rashin sanin abinyi ta cigaba da taunan abincin ta a hankali...

*HAMDAN*
Tsurawa k'ananan labb'an ta masu kala biyu yayi, wanda ya kasance pink sai zagayen baki kamar ta zana da eye- pencil sai dai ba haka bane, naturally haka lips din ta yake...

Yanda take taunan yafi komai tafiya da shi,  idanunsa ya kai kan sakin masara  da yayi fari kamar ma ba a sa masa manja ba, alamun bai ji ba.

Ya kasa yarda cewa mutum ke cin irin wanna abincin da a wajen shi sai dai ya kira shi guba, domin a tunanin sa zai iya sa mutum rashin lafiya, saboda ganin da yake wa abincin yanzu wani tashi zuciyar sa ke yi, dauke idanun sa daga kan abincin yayi, a fakaice ya kalli tsakar gidan su, a rayuwa bai taba ganin gida daya lalace irin wannan bare har ya shiga, amma saboda bawa abinda zuciyar sa ke so yau gashi a cikin gidan da a wajen shi gwara kwalta a kan sa.

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now