3

34 1 0
                                    


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
(The hunch back girl)

#  _NoorEemaan_

The writer of
Rayuwar faheemah
Mijin Ammina ne sila
Papi ne
Kyautar koda
Abraham
And now👇
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)

*Free page*

Chapter5️⃣⏩6️⃣

D'ago fararren idanun ta masu d'auke da brown eye ball tayi, kana ta kalli wacce ta kira ta.

murmushin da za a kira shi na yake matar ta sakar wa hoorain, martani hoorain ta mayar mata har jerarrun hak'oranta suka bayyana, a hankali matar nan da a kalla zata yi shekaru talatin da tara ta karaso ta zauna a gefen ta, cikin kauna mai tsanani da take wa yarta tace

"Hoorain ga abinci a daki, na dauko miki?"

"A'a Mami.... na koshi" hoorain ta fada cikin sanyin muryar ta mai dad'in amon.

"Me kika ci da zaki ce kin koshi, ko bakya son wanna abinci wani kike so?" Mami ta tambaye ta with so much care.

Murmushi hoorain ta sakar wa Mami tana kokarin mayar da kwallar ta, abinda zasu kai baki wahala yake musu, amma domin farincikin ta Mami ke tambayar ta idan wani abu take so, hak'ik'a idan taci abincin nan bata kasance y'a mai jikin kai hadi da tausayin mahaifiyar ta ba.

"Allah Mami cikina a cushe yake, bana jin yunwa, yanzu ma da daga band'aki nake" ta karasa tana sakar wa Mami murmushi domin kwantar mata da hankali.

Jinjina kai mami tayi, kana ta mike ta shige daki...
Yamutsa fuska Hoorain tayi sak'amak'on wani murdawa da cikin ta yayi kamar y'a'yan hanjin ta zasu fito saboda yanda cikin ta yake wayam babu abinci, amma bazata iya ci ba, domin ta tabbatar Mami ta fita jin yunwa, domin a daren jiya dan guntun abinci daya rage musu ita ta cinye, Mami ta ce ta koshi saboda ita ta samu ta ci, cikin dare tana kallon Mami ba tare da sanin ta ba tana murkususu hadi da yin ruf da ciki, a jiya tayi kuka sosai mara sauti domin bata so mahaifiyar ta taji...

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

*HAMDAN*
Da misalin k'arfe uku da mintuna arba'in suka isa kogi kauyen Oguma. Sai dai ba cikin kauyen can ciki ba.
Tunda daga wajen kauyen Hamdan ya fahimci cewa tabbas kauyen nan ba lafiya, haka dai suka nufi inda aka tanadar musu, already an riga anyi musu abinci, nan mutanen da aka bawa contract din abincin suka shiga gabatar musu dashi.

Kallo daya hamadan yayi wa abincin ya dauke kansa, sam baya jin zai iya cin wanna abincin da ya tabbatar hannu da yawa ne ya dafa ta, sannan bai san yaya tsaftar mutanen yake ba.

Nannade hannu rigar shi yayi, sannan ya fara ciri bakin safa da Boot din kafar sa, inda take farar lafiyayyen kafar sa ta bayyana tamkar bai taba taka ƙasa ba.

Dan jan wandon sa yayi sama kad'an, ya cire  agogon hannun sa ya d'aura kan wani babban dutsen dake gefen wajen, cike da nutsuwa ya shiga yin alwala, bayan ya gama ya mayar da safar sa da takalmi, zai dauki agogon sa dake kan dutse karaf ya kama Godiya tana kallon sa, macen soja ce yar garin Jos, kara daure fuskar nan yayi tamau fiye da baya, sannan ya bude motar su ya dauki sallaya kana ya fuskanci gabas ya fara sallah cike da nutsuwa, sallar daya dauke shi mintuna goma kafin ya iddar, addu'a sosai yayi, kan Allah ya basu nasara a wannan aikin da suka zo yi, wayar sa ya ciro daga aljihun wandon sa, ya danna number'n Ammi.... Bayan ta daga yace

"first love ina wuni, nayi kewar ki"

Murmushi tayi kana tace
"Lafiya Lou Captain, ya hanya? Ina ta son kiran ka amma ban samu zama ba, iyalan baba Dalhat ne suka kawo min ziyara"

Lumshe rikitattun sky blue eyes din sa yayi kana yace
"Mun isa kauyen Ammi"

Ajiyar zuciya ya ji Ammi ta saki, ta shiga fadin alhamdulillah, daga nan suka ɗan yi hira, yana jin Muryar Ayiyah da su Omar suka hira, kafin su yi sallama Ammi ta jadadda masa lallai ya ci abinci k'ar ya zauna da yunwa, ya dai amsa mata, amma bazai iya cin wanna abincin ba, rather he prefer ya sha coffeen sa.

Bayan sallar Isha ne, duk sojas din sun kasance cikin shiri, dama yan ta'addan nan cikin dare  suke kawo farmaki kauyen, cike da k'warewa Hamdan yake basu umarni da nuna musu direction din da kowa zai bi cikin kauyen ba tare da yan ta'addan sun sani ba, sannan wasu sojas din ya basu umarnin zaga gidajen kauyen domin tabbatar da tsoro... haka dai ya rarraba su ta yanda za a samu komai ya tafi yanda suka tsara...

*10:00pm*
Duk da tsoron dake lullub'e  a zukatan jama'ar kauyen Oguma, amma hakan bai hana wasu kwantar da hak'ark'arin su domin bacci ba musamman yara marasa wayo  cikinsu, Manyan kuma na zaune cikin zullumi da tsoro mai tsanani.

Karan bindigan da kauyen suka ji yayi sanadiyar karin tashin hankalin su, hakan kuma ya sanar musu cewa azzaluman sun shigo...

Masu tsananin tsoro har fitsari suka saki saboda tashin hankali, wasu kuwa cikin su ne ya shiga murd'awa suna shiga ba haya, domin rage ciki, wanda tashin hankali ya haifar musu da shi, masu buyo har a k'ark'ashin gado na yi, wasu na neman hanyar guguwa, wasu kuma sun fito waje, gaba-daya kukan su ya cika kauyen, ga yan ta'addan da suka fara cinna wuta a wasu gidajen...

Ta bangaren Hoorain da mami kuwa suna cikin gidan su basu fito ba, bama zasu iya gudu ba saboda lalurar hoorain bazai bari su tsira da ran su ba tare da an kama su ba, sai dai wani ikon Allah.
Mami baiwar Allah na zaune kan kod'ad'iyyar sallayar su tana rokon Allah ya kawo musu dauki, hoorain dake gefe hawaye na zuba daga idanun ta ma addu'a sosai take a ranta tana fatan Allah ya kawo musu karshen wannan kashe-kashe rayukan da ake a duniya, tana mamaki mutane marasa imani da zasu iya kashe rai da bai yi maka komai ba saboda son duniya, me suka tanada da zasu kare kan su da shi idan Allah ya tambaye su ranar gobe kiyama?

Daga ɓangaren yan ta'addan nan kuwa, harbi kawai suka fara ji from no where, wanna hakan ya tabbatar musu da cewa sojoji ne, maimakon su yarda makaman yakin su sai ma kara sakin harbin da suke, nan fa zugan soldiers dinnan suka bayyana kansu kana suka cigaba da sakar musu ruwan alburushi... suma yan ta'addan na sakar musu, yan kauyen Oguma suke dawo yan kallo, tsoron daya lullube zukatan su na raguwa, wasu sojas dake tsaye a kofar ko wani gida suka umarci wadanda suka fito waje kan su koma cikin gida gudun kada harbi ya same su, ai kuwa da gudu duk suka shiga har da saka sakata, dama tsananin tsoro, rudu, da rashin sanin abin yi ne ya fito da su.

Nan fada ya dawo tsakanin SOLDIERS da yan TA'ADDA, sai musayar wuta harbi suke cike da kwarewa...
yan ta'addan nan kamar kara tunkudo su ake, ana kashe su suna kara fitowa, abu fa yaki karewa har karfen dayan dare, inda a lokacin shugaban su da wasu zugan suka kara cika kauyen, suna cigaba da harbi.

Al'amarin fa ya girmama tunanin sojas dinnan, domin basu dauka haka abin yayi muni ba.
Godiya soja da itama take cikin masu harbin ta  koma gefe ta yanda ba za a ganta ba, wayarta ta fito dashi,  number'n Hamdan ta yi dialing wanda Allah kadai ya san ina ta samu...

*******

Safa da marwa yake, cikin farfajiyar gidan da suke, ya kira number'n wasu sojas din da yake da shi, amma basa dagawa, ya tabbata har yanzu basu kamalla bane, gashi manyan sa sun bashi umarnin cewa kada ya shiga yakin, na shi bada umarni ne da jagorantan su kawai. Amma ya fada a ransa cewa dole idan fadan ya ɓaci zai shiga cikin su... yana cikin wannan tunanin yaji wayar sa na ringing, bakuwar number'n ya gani, latsa kore yayi ya ƙara a kunne sa ba tare da yace komai ba

Cikin muryar ta mai amon sauti da jarumta kamar ba mace ba tace
"sir! Godiya ce, yan ta'addan nan kara yawa suke, domin har sun kashe mana mutane biyar...."

Bai jira ta gama maganar ba ya kashe wayar ya jefa a aljihun wandon kakin sa, cikin zafin nama ya dauki bindigogi bayan ya cika musu bullet, tsakanin cikin kauyen Oguma da gidan da aka tanadar musu tafiyar mintuna talatin ne, ba kuma yaso yayi amfani da abin hawa, saboda hakan zai sanar wa yan ta'addan zuwan sa, so yake yayi musu dirar ba zata, da direction da aka basu ya dinga bi, cikin sauri-sauri gudu-gudu cike da taka tsantsan domin isa wajen...✍️

*Hoorain Mai Kusumbi is not for free, it's 300 via, if you are willing to pay, here is the account details... 2261488155 Rukayya haruna zenith bank*.
*Then send  evidence of payment to this number 07082281566*

NoorEemaan
07082281566

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JxzoG62bUENBfExeNPbRSu

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now