2

38 1 0
                                    

 
🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
            (The hunch back girl)

#NoorEemaan

*Hoorain Mai Kusumbi is not for free, it's 300 via, if you are willing to pay, here is the account details... 2261488155 Rukayya haruna zenith bank*.
*Then send  evidence of payment to this number 07082281566*

*Free page*

Chapter 3️⃣⏩4️⃣

"FIELD MARSHAL"

Shine sunan daya gani a rubuce baro-baro kan screen din wayar sa.

Latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunne sa, cikin girmamawa wa marshal yace

"Good evening sir!"

"Evening captain, hope you are good?"

Hamdan yace "very well sir"

"That's nice, am... kan maganar da zaka jagoranci wasu sojas zuwa yaki ya tashi daga sati mai zuwa, domin mun samu labarin yan ta'addan nan sun sake kai farmaki wa kauyen, suna cikin wani hali matuƙa, dan haka jibi ne tafiyar ku in Sha Allah, domin gobe za a kamalla muku komai na tafiyar, all the Best captain Hamdan"

"Thank you sir" ya amsa yana taune jajayen labban'sa masu daukar hankali.

Ya jima yana tunane-tunane kana bacci ya dauke sa, kasancewar a matukar gajiye yake.

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

*WASHEGARI*
Misalin karfe goman safiya ce, zaune yake cikin motar sa yana sharara gudu kan lafiyayyen kwaltan, sanye yake da three quater wando na soja, sai singlet shi ma na sojas daya bayyana karfafan kafadun sa masu fadi, babu hula a kan shi yayi parking gashin sa as usually, kafar sa sanye da sandal fari mai igiyoyi,  hannunsa dake murza sitiyarin cike da kwarewa sanye yake da tsad'add'en agogo, yayi mugun yin kyau...
Karatun Alqur'ani ke tashi cikin surutal Al-furqan, a nutse yake bi cikin zuciyar sa, wayar sa dake kan kujerar mai zaman banza ya dauka ya yi danne-danne kana ya kara a kunne sa,  bayan seconds hamsin aka daga kiran daya ɗayan bangaren.
Kasa-kasa kamar mai tsoron kar a ji shi yace
"Assalamu alaikum, ina kwana first love, am on my way coming"
Abinda yace kenan ya katse kiran, bayan mintuna goma ya shigo unguwar su Nasarawa GRA, horn ya danna aka bude masa ya shiga,  a tsakiyar gidan ya yi parking motar kana ya nufi part ɗin Ammi.

A bakin kofar glass ya tsaya, kofar ta buɗe ya shiga, runtse ido yayi sak'amak'on ganin Ayiyah a Zaune, a ransa yace

"damn it!  Meyasa matar nan ta dawo" domin idan akwai abinda yake gudu toh Ayiyah ce, duk da kasancewar ta kakar sa, amma mugun ciwon kai take bashi.

Ware rikitattun idanun sa yayi, kamar yadda ya saba ciki-ciki haka yayi sallama, yana k'ara daure fuskar sa tamau, gudun kada Ayiyah ta kawo masa wargi amma bai tsira ba...
Cikin muryar ta mai cike da k'arsashi duk da ta tsufa tace
"fuska Fara, zuciyar ka baka, idan ka ga dama ka dawo da fuskar ka ta shanu bai dame ni ba, wallahi sai nayi magana, domin ni idan nayi shiru ban yi magana ba bakina wari yake, wanna gantalewa da bakin halin har ina, a cewa kullum mutum fuska a murtuke kamar na kashin asuba "

Ammi dake jin su kuwa matse dariyarta tayi, Hamdan kuwa kara bata rai yayi ya nufi wajen Ammi ya zauna kusa da ita, Cikin kaunar mahaifiyar sa ya kalle ta kana yace "Ammi hope you are Fine?"

"Am very fine Dan albarka, ya aiki?"

"Fine first love"

ya amsa yana ɗora kansa kan kafadar ta.

Wani tabe baki Ayiyah tayi tace " haka fa, sai karyar turanci, yanzu fisabilillahi ko kunya baka ji, katoto da kai ka wani zo ka manne wa uwar ka, ko su Abbas da suke kannen ka basa wanna iyayin, ko da yaƙe laifin uwar ka nake gani, domin ita ke shagwaba ba"  ta bantali goro tana tauna, jikake karas karas ta kuma baza kunne domin jin yayi magana amma bai kula ta ba,  hakan ya dame ta, domin ita kam bata iya shiru ba, ba kuma ta so a yi shiru, "nayi magana kayi shiru kamar baka ji ba, gaskiya dai sai na fada, kuma bari ka ji ka yi ka nemo matar aure domin mun gaji da ganin ka haka, ko kuma na je kauyen su wata kawata na samo maka mata a can...."

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now