9

48 1 0
                                    


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
(The hunch back girl)

_written by NoorEemaan_📚✍️



Chapter 1️⃣7️⃣⏩1️⃣8️⃣

Daga can bangaren Ammi kuwa a zafafe ta daga wayar domin sauke masu tsananin fushin da take dashi, saboda kullum cikin damuwa take, musamman data daina samun sa k'watak'wata a waya... Sabanin fadan da take da niyyar masa, sai jikin ta yayi laushi sak'amak'on muryar sa da ta ji yayi kasa sosai ya furta

"my first love".

Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana jin fushin da take da shi na raguwa, sosai take son Hamdan, amma ta rasa meka damun sa gaba-daya ya sauya mata, kamar ba zakin sojan ta ba, duk da babu gazawa a muryar sa amma ta66as akwai canje-canje a tare da shi.

"Captain dina, ka ɗauke ni matsayin ammin ka kuma first love dinka kamar yadda kake fada?"

"Of course yes Ammi" ya fada yana mikewa zaune, domin da kamar bacin rai Hadi da damuwa a tattare da Muryar ta.

"Then why kake boye mun damuwar ka, ko ban cancanci sani ba?".

"A'a Ammi, kin fi kowa dacewa ki sani" ya fada cikin wata murya daya kashewa Ammi jiki.

Amma ta daure tace "in hakane then tell me, me kake a kogi bayan ba dangi uwa bare na uba a can, meyasa bazaka dawo ba, na kasa gane maka fa, You re behaving strange these days, ko so kake ka samun damuwa a zuciya, baka bani ciwon kai kana yaro ba sai yanzu daka mallaki hankalin ka Hamdan? answer me am taking to you" wanna karon a dan tsawace tayi maganar domin she can't take it anymore.

A Zuciyar sa yaji wani daci sosai, idanun sa ya runtse da karfi, abu ne wanda kowa na gidan su ya sani, matuƙar Ammi ta kira real name dinsa toh lallai fushi take da shi, boyayyen ajiyar zuciya ya sauke kana cikin Muryar sa da yayi bala'in yin kasa yace "Am sorry Ammi, please karki yi fushi dani, You know I have you first love, bana kaunar ganin fushin ki..."

Numfashi ya dan sauke yana datse jajayen labb'an sa da jerarrun hak'oransa sannan ya cigaba da cewa "as soon as na dawo zan baki labari mai dadi wanda kika jima da muradin jin shi daga bakina"

Sanyin sosai Ammi taji a ranta, fuskar ta dauke da murmushi.

Hamdan ya dan yi gyaran murya yace " pray for me, ki sa ni a addu'ar ki, Allah ya bani ikon yin abinda ke raina, kinji first love?"

"My handsome son, a kullum ina maka, sannan zan dage da tashin dare domin yi maka addu'a, Allah ya tsare mun kai a duk inda kake, ya baka Sa'a, Please do take care of yourself for Ammi ok, i love You"

"I love you too first love" yayi mata reply.

"Yawwa nace yaushe zaka dawo ne?"

Shiru yayi na yan Mintuna sannan yace
"Ammi ban sani ba, but a kodayaushe zaki iya gani na, just pray for your son"

Jikin Ammi ya fara sanyi da lamarin Hamdan. Definitely something is fishy somewhere, amma bata matsa masa ba, addu'a ta k'ara masa, da haka suka yi sallama.

Ya jima zaune idanun sa a lumshe yana tunani.. can hoton fuskar Hoorain ya mamaye idanunsa, ajiyar zuciya ya sauke kamar ita din ya gani a gabansa, tuno halin daya barta a ciki ne yasa shi mikewa, yayi kewar ta ba kaɗan ba, musamman zazzak'ar Muryar ta da murmushin ta dake sanya zuciyar sa yin sanyi, mikewa yayi ya shirya, kana ya nufi cikin kauyen nasu....

*******

Kansa tsaye cikin gidan bakin sa dauke da sallama kasa kasa kamar yadda ya saba, dan tsakar gidan nasu shiru, babu motsin kowa.

Mami data ji Muryar sa kasa_kasa ta fito tana amsa sallamar, cikin girmamawa ya dukar da kansa ya gaishe ta, Mami ta amsa fuskar ta a sake, kana ta warware masa matacciyar tabarman su dake nannad'e sakamakon hakan k'urar jar dake jikin tabarman ya tashi, kawar da kansa gefe yayi, juyowa Mami tayi ta ce "zauna ko, bari na taso Hoorain, tun jiya taki bacci sai dazu na samu baccin ya d'auke ta"

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now