8

47 0 1
                                    


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
(The hunch back girl


#sacrifice
#hotlove
#heart touching
#hatred
#betrayal

_written by NoorEemaan_📚✍️

Chapter 1️⃣5️⃣⏩1️⃣6️⃣

Safiyar alhamsin ne, jama'ar kauyen Oguma sai fitowa suke sak'amak'on jin Muryar dan baiwa Ashimi, domin su san matuƙar ya fito yana magana, toh fa yayi mafarki ne, kowa fargaban sa Kada a kira daya daga cikin sunan ahalin sa.

*TAKAITACCEN TARIHIN DAN BAIWA ASHIMI*

Asalin sa dan kauyen oguma ne, ya samo inkinyan sunan dan baiwa ne sakamakon idan yayi mafarki yana kasancewa gaskiya, tarin baiwa da ilimin sa ya sa ake ganin shi kamar wani sha takwas, wanda azahiri ba haka bane, tarin baiwa da ilimi ne ya sashi kasance hakan, farko idan yana sanar yayi mafarki, Zai kuma ce ayi sadaka mutane domin Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi, sai ana daukar abin wasa, har ya zama  abin dariya ga yan kauyen.

Ranar da yayi wata mafarki basu ɗauke shi da Muhammanci ba, har abinda ba a so ya hafku, domin exactly munanan mafarkin da yayi ya faru a zahiri.

hakan yasa tun daga wannan ranar idan Allah ya sa yayi mafarkin mutum mara kyau, sai yace ayi sadaka, ko kuma yace a dage da   tashi sallan dare, in Sha Allah sai mutum ya ga komai lafiya sakamakon addu'a da sadaka da ya yi, hakan yasa da yayi mafarki ya bayyana suna daukar shi da gaske...

*BACK TO STORY*

**********

Sai daya zo daidai kofar gidan su Hoorain ya ja ya tsaya, kana yace "Hoorain Yusuf a yau Allah ya bani ikon ganin maganin lurar ki a mafarki"

ya maimaita hakan sau uku abinka da yan kauye gaba-daya sun zagaye shi, ana ta kallon sa.

Ta bangaren Hoorain kuwa zaune suke ita da Hamdan da kullum sai yazo ya ganta yake samun nutsuwar zuciya.

Mami tana daki a zaune, yayinda Hamdan ke bare mata cashew nut da Aramani ya kawo mata soyayye tana ci, kawai kallon dan tsut din bakin ta yake with much admiring on his face, komai nata na burge shi, kamar ya hadiye ta ɗan so amma sam ba za ka taba gane hakan ta fuskar shi ba.

A lokacin da suka ji Ashimi dan baiwa ya kira sunan Hoorain gaban Mami da ita Hoorain yayi mummunan fad'uwa, cikin rashin fahimta Hamdan ke kallon hanyar soro ta inda yake hango kafafun mutane, gashi hayaniyar su ta cika wajen...

Mami ce ta fito daga daki, sannan ta mikawa Hoorain hannu  domin  taimaka mata wurin tashi, cikin mugun sanyi da jikin ta yayi ta kama hannu Mami ta mike...

cikin tafiyarta ta masu kusumbi ta bi bayan Mami, Hamdan ma mikewa yayi ya rufa musu baya, nan fa idanun yan k'auyen ya bisu Mami da suka fito zuuuuuuuuu

Cak Ashimi ya sayar da idanun sa masu kwarjini sosai ga fuskar Hoorain, kasa tayi da kanta domin idanun sa tsoro suke bata sakamakon tarin baiwa daya cika cikin su.

"A yau Allah ya nuna min ke Hoorain a mafarki"

Sai ya kalli Mami da idanun ta ke dauke da hawaye yace

"wannan kusumbi ba da shi kika haife ta ba, tana da Shekara daya a duniya aljanin daya yi sha'awar surar ta ya sanya mata sakamakon wata rana kin kwantar da ita tana bacci babu wando a jikin ta, kina band'aki, shi kuma ya bayyana gareta, surar Hoorain ya burge shi kana ya bashi sha'awa duk da karama ce, hakan yasa ya mika hannunsa daidai bayanta wani koren haske ya bayyana ya shiga ratsa bayanta, bayan wasu Mintuna ya bace bat.

Manufar sa ta yin hakan shine saboda kada wani da namiji ya aure ta ko ya so ta, shi kadai ne zai mallake ta. Kamar wasa a  hankali kusumbi ya fara tsiro wa har yayi wanna girman, a ko wacce rana wannan Aljani mai suna mushkaf sai ya zo ya kara mata girman sa, shiyasa kullum kusumbin ke cigaba da mamaye bayan ta, idan kuma aka cigaba a haka watarana zai rinjaye ta ta yanda ko tashi zai gagare ta..."

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now