4

29 1 0
                                    


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
(The hunch back girl)

# _NoorEemaan_

*DEAR LOVELY FANS DA MA MAKARANTAN HOORAIN PLEASE KU KARANTA WANNAN BAYANIN NAWA IT'S VERY IMPORTANT*

_Zan yi wanna dan tsokacin ne  idan ma akwai mai irin wanna tunanin a ransa_.
_Kila wasunku zaku ce meyasa Noor ta rubuta cewa HAMDAN yana da gashi, bayan ba a san sojojin da gashi ba_.

_Yeah it's possible soldiers su tara gashi, amma mafi yawa na nan Najeriya basa yi_...
_Abin da ya saba dokar soja shine askin banza ne ba a so_... _Amma  bawai basa tara gashi bane, sai dai mafi yawan su basa tara mai yawa_...

_Dan haka Habibte's ina sane da abinda na rubuta, domin ina da experience a akan soldiers, ina da friends da yan'uwa sojas,  and also tun Ina pre-nursery har na gama secondary school a barrack din sojoji nayi karatu na, to Cut it short_...
_Haka nake son HAMDAN ya kasance a littafin HOORAIN, shiyasa na rubuta cewa yana da suma_.
_Abu mafi muhimmanci a novel shine sakon da marubuciya take son isar wa yaje inda ake so_.

_A karshe dai makaranta na da suke bibiyata tun daga farkon book dina sun san cewa duka book dina fictional story's ne, ban taba rubuta true live story ba, Dan haka a Novel ba komai ne dake faruwa a gaske  za a  rubuta ba, dole akwai nishadantarwa domin kawata Labarin_.

*Thank you all da yanda kuka karbi littafin HOORAIN MAI KUSUMBI wandanda suka siyi book dina ina godiya sosai Allah ya bar kauna, son so nake muku*.

*Free page*

Chapter 7️⃣ ⏩ 8️⃣

Tafiyar da ya kamata yayi a Mintuna talatin, a 20 minutes yayi shi.
A lokacin daya isa wajen yayi mamakin yadda  abu ya ɓaci haka, ba tare da  bata lokaci ba ya shiga cikin sauran soldiers  aka cigaba da fafatawa cike da kwarewa wanda hakan ya nuna cewa sun  sha  training mai zafi...

A takaice dai sai karfe hudu saura aka samu komai ya lafa, inda yan ta'addan nan da suke rage takwas har da shugaban su suka yi kokarin guduwa, domin bullet din su ya kare.

Cikin sa a hamdan ya samu nasarar sakarwa biyar arbi a kafafun su biyu, sauran ukun ma wasu soldiers din suka karbe su, hakan yasa suka zube a kasa suna ihu azaba...

Umarnin Hamdan ya bayar cewa a kamo su duka. Sannan ya ce wa wasu soldiers din su tsaya a kauyen har safiya domin tabbatar da tsoro, cikin girmamawa suka amsa da "yes sir!" 
Bayan sun isa gidan da suka sauka nan aka kulle yan ta'addan nan a wani daki.

*WASHEGARI*
Kusan ko wani kafa da sadarwa sun samu labarin abinda ya faruwa, sun kuma bayyana wa jama'a, zuciyar mutane cike da farin ciki nasarar da Allah ya bawa wadanda jaruman sojas din masu kishin kasar su.

Field marshal wanda shine mai 5 star rank general, haka kuma shine highest rank a Nigerian army, Ya kira Hamdan ya yaba masa.

Ammin ma ta gani a news din karfe shida da ta kalla, ta kira hamdan tayi masa murna sosai da addu'ar Allah ya dawo da su lafiya.

Da misalin k'arfe taran safe yan jaridu sun cika k'auyen oguma domin cigaba da daukar rahoto, Sannan an kai yan ta'addan nan babban kotun Abuja kasancewar daga kogi zuwa Abuja babu wani mugun nisan, an saka su a prison zuwa ranar da za a yanke musu hukunci...

*BAYAN KWANA ƊAYA*.

Ta bangaren yan k'auyen oguma kuwa sosai suka tashi da nishadi a safiyar yau, tsoron da fargaban su ya kau, sun dawo hada-hadar su kamar yadda suka saba cikin walwala.

********

Tafe take cikin tafiyar ta irin na masu kusumbi, hanyar rafin kauyen su ta nufi, duk da yanda mami ta hanata zuwa, amma bazata iya kallon Mami da girman ta na zuwa diban ruwa yayinda ita ke zaune ba.

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now