10

87 2 1
                                    


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
    (The hunch back girl)

_written by NoorEemaan_ 📚✍️

Chapter 1️⃣9️⃣⏩2️⃣0️⃣

Hannun Mami ta rungume gam tana cigaba da kukan, ga muryar ta ya fara dashewa... haka ta cigaba da kallon su har ta daina ganin su.

Mami ta kamata da k'yar domin ita ma babu karfi a jikin ta suka nufi dan gidan su.

Mami ta shigar da ita daki, Hoorain ta sulale kan yoluluwar kafitar su ta kwanta, babu jimawa wani zafaffan zazzab'i ya rufe ta, jikinta ya dau zafi, hak'oranta na had'ewa dana juna yayinda jikinta ke rawa kamar mazari...

Hankali tashe Mami ta dauko yan jike-jike irin na su na kauyen ta bata ta sha, sannan ta dauki zanin ta ta rufa mata, bayan Mintuna talatin wani bacci mara dadi ya dauke ta cike da mafarkin su Hamdan.

*********

*NASARAWA GRA SULTAN ROAD*
_10:00am_

A dai-dai lokacin Ammi ta tashi daga bacci, domin raba dare tayi tana ibada, bayan tayi sallar asuba kuma bacci ya dauke ta, sai yanzu ta tashi.

Mikewa tayi tana dan yamutsa fuska abinka da jikin tsufa, toilet ta nufa tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin had'add'e kuma tsad'add'en atamfar  *English gold*  ta shafa humra da wasu turaren ta masu  dadin k'amshi.
Ammi macece mai son gayu, tsafta, hadi da k'amshi, a takaice dai a wurin ta y'ay'an ta suka gado hakan.

Bakin gado ta zauna, ta latsa wayar ta, inbox dinta ta gani ya nuna an turo message, hakan yasa ta shiga, ganin number'n Hamdan ne yasa ta danna da sauri...

Sau uku ta maimaita abinda ya rubuto mata, jikin ta yayi sanyi sosai kalaman sa sun ratsa zuciyar ta, tausayin sa da son sa sosai taji ya kara shigar ta har hakan yasa wasu hawaye Masu dumi suka biyo kuncin ta, hannun ta daga sama a fili tace "ya Allah ka fini sanin abinda yarona ke yi, ya Allah ka bashi Sa'a, ka zaba masa abinda yake mafi alkhairi, ka tsare shi da tsarewar ka ya Allah, ka kiyaye shi  da  kiyayewar ka, mugun ji, mugun gani ya Allah ka raba shi da su, sharrin mutum sharrin Aljani ya Allah ya kiyaye shi, Allah ka dawo min dashi cikin koshin lafiya" ta shafa addu'ar wasu hawayen na kara zubo mata.

"Falmata! Falmata!! Wai baccin ne yar yanzu? inci dai Lafiya ko?" Ayiyah data zo bakin kofar yanzu ta fada.

Cikin gaggawa Ammi ta share hawayenta, sannan ta dai-dai ta Muryar ta ce
"gani nan Ayiyah" ta fada tana nufar bakin kofar, ta bude, ta wani dogon corridor ta bi sai ga ta a babban falon  ta wanda ya kasance kamar general falo domin duk a nan suke jin abincin.

Ayiyah ta gani zaune ta kurawa tv ido, kamar idanun ta zasu fado ciki, jin takun tafiyar Ammi yasa ta waiwayo, ta zubawa Ammi idanunta da ta rambada musu kwalli har yaso yayi yawa, tace "Falmata! wanna wani irin Bacci mai nauyi kika yi haka? Hankalina ya tashi ba shiri na kwashi kafafuna nace bari na dubo ko lafiya, yo Allah na tuba kana zaune da mutum yanzu, daya shiga daki babu jimawa sai dai ka ji ya zarce lahira, su Anas ma sun tambaya nace baki tashi ba, har sun wuce aiki domin sun ce basa son tashin ki"

Murmushin k'arfin hali Ammi tayi a ranta tana jinjina surutun Ayiyah ko full stop babu, rissinawa tayi kamar yadda ta saba ta gaishe da Ayiyah, cikin kulawa Ayiyah ta amsa tana sa mata albarka, domin ta kasance mace mai son a girmama ta, sannan tana yawan yabon Ammi a ranta domin duk da danta Wanda shine mijin Ammi  ya rasu, amma hakan bai sa ta fasa girmama ta ba.

"Kiyi karin kumallo ko? yau kin makara... Nace wai ya wanna dan fadin rai da miskilancin tsiya, ince kun yi waya mara kirki ko neman kakar sa baya yi"

Danne damuwarta Ammi tayi sannan tace "eh Ayiyah yana lafiya, yace ma ce na gaishe ki" ta karasa domin faranta ran Ayiyah.

Ta kuwa washe hakoran ta tace "Masha Allah, dan k'wal uba yau ya ga daman tambayata kenan" ta karasa tana sakin dariya irin nasu na tsofaffi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 22, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now