7

48 1 0
                                    


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
(The hunch back girl)

_NoorEemaan_✍️📚

Chapter 1️⃣3️⃣⏩1️⃣4️⃣

Mintuna arba'in ya dauke shi shiryawa, kana ya dauki hanyar cikin kauyen oguma. Yana zuwa kofar gidan ya hangeta daga dan nesa da shi tana tafiya da bokitin rike a hannun ta, nan ya fahimci rafi zata je, wani iri ba dadi haka ya ji a ransa. So yake ya kira ta amma ya rasa ta yanda zai fara bude murya..., hakan ya sa  cikin zafin nama irin na su  na soldiers ya shiga bin ta, taku biyar zuwa shida ya iske ta...

*HOORAIN*

Ji tayi an karbi bokitin hannu ta, a tsorace ta juyi, ganin Hamdan ya sa ta sauke ajiyar zuciya mai sauti kana tayi murmushi.

Hamdan so yake yace mata sorry ya razana ta amma ya kasa.

Cikin sanyi da dadin Muryar ta tace "ina kwana ya Hamdan" ta ji sunan shi ne a lokacin da Ammi ta tambaye sa.

Wani yanayi na musamman yaji a zuciyar sa, kannen sa ya tuno, domin haka suke kiran shi, amma nata dabanne, domin tamkar da wani salo daya kawata sunan ta yi amfanin wurin kiran shi, wanda ya ji ya tsaru sosai a kunnuwan sa.

"Lafiya"

shine abinda yace cikin maganar sa da yafi kama da rada, domin idan baka da kunnen ji bazaka ji abinda yace ba.

Hoorain bata kara magana ba suka cigaba da tafiya, duk wanda suka hadu da shi a hanya su dinga bin su da ido kenan cikin mamaki, wasu har tuntube suke garin kallo, babban mamakin su shine ganin lafiyayyen namiji handsome uwa uba dan gayu a tare da Hoorain mai kusumbi.
ashe duk iya wakan Taheer dan mai gari da suke gani wasa ne, domin Hamdan ya dama ya shanye shi... Hamdan kuwa kara dinke fuskar nan yayi tsaf ganin kallon yayi yawa.

Bayan sun zo rafin Hoorain ta kalle shi, tace "ya hamdan kawo bucket din na debo ruwan"

Wani kallo ya jefa mata, shi ba harara ba gashi nan dai, kasa da tayi da kanta, domin k'wayar idanunsa mai kalar sararin samaniya yana matuƙar tasari a gareta tare da saukar mata da kasala, sam bata jurar kallon cikin su.

Kan wani babban dutse ya nuna mata yace "sit!" Ba musu ta zauna.

Kamar ruwa ya cinye Yammatan dake rafin nan, mutuwar tsaye suka yi ganin Hoorain da Hamdan, hassada k'arara ya bayyana a fuskar su, tsanar Hoorain ya kara cika zuciyar su.

Hamdan kuwa bakin rafin ya nufa, ba tare da ya kalli fuskar kowa ba, kamar kullum macijin 🐍 nan mai gadin ruwa na nan bakin ruwan...kallo daya yayiwa macijin ya dauke kansa, bucket din ya sa cikin ruwan ya diba kana ya nufi wajen da  Hoorain ze zauna, alama yayi mata da ido kan su tafi ba musu ta tashi ta bishi, a ranta tana mamakin yau yammatan basu tsokaneta ba... Yau karon farko a kauyen oguma da bata yi kuka ba, sak'amak'on babu wanda ya nemi tsokanar ta.

Sun dan yi nisa da tafiya Hoorain taji an kwala kiran sunan ta.
A tare da suka tsaya, amma shi Hamdan bai juyo ba, murmushi Hoorain ta sakarwa Aramani daya taho hannun sa rike da kayan aikin gona.

Bayan ya karaso suka gaisa cikin yanayin su na shakuwa, sannan ya gaishe da Hamdan, gogan bai amsa ba, sai hannu daya bashi suka yi musabaha, wani dadi Aramani yaji ganin classic handsome guy ya bashi hannu sun gaisa ba kyama.

Kallon Hoorain yayi da yare yace
"waye wanna kyakkyawan?"

Murmushi tayi, cikin yaren ita ma tace "sabon yaya ne" ta fadi hakan domin bata san matsayin daya bata a zuciya ba kar ta zafafa da yawa.

"Gaskiya ya hadu, kuma wallahi kunyi kama fa"

Dan kwabe fuska tayi tace "dan'uwa Aramani haka zamu yi da kai, kai ma kasan ba gaskiya bane"

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now