5

26 3 4
                                    


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
(The hunch back girl)


_NoorEemaan_


*The love and affection he has for her totally made him a changed person. Labarin da yazo da wani salo wanda baku taba ganin irin shi ba, fadakarwa, zafaffan soyayya, tsantsar kiyayya, sadaukarwa mai girma and a lot of more*

Chapter 9️⃣⏩🔟

🎻🎻 _I wanna come home to roses_🌹 _And dirty little notes on post-it's_📝 _And when my hair star turning grey_...🧑🏽‍🦳🎻🎻

🎻🎻 _He will say I'm like a fine wine better than age_🍷
_I guess i learned it from my parents, that true love starts With friendship_♥️

_A kiss on the forehead_💋 _a date night_🌃🍝
_Fake an apology after a fight..._🤫

_i need a man who's patient & kind gets out of the car and hold the door_🚗

_i wanna slow dance in the living room like_... _we're 18 at senior prom_.
_And grow old with someone🧑🏽‍🦳👨🏼‍🦳who makes me feel young_💃🕺
_i need a man who loves me likeee... My father loves my mom_♥️🎻🎻

ta kai ƙarshen wakar nan da wani slow tone mai tsayawa a rai.

*HAMDAN*
Ji yayi Kamar ruwan kan shi ya kone, wani yanayi mai wuyar fassaruwa ya dinga ratsa shi, ba tare da ya shirya wa hakan ba, kasan makoshi ya furta " ya rabb! what a melody voice"

Hoorain kuwa sam bata san da tsayuwar sa ba, domin ita kanta dake wakar ratsa zuciyar ta yake, sosai take matukar son wakar nan, wanda a wayar Aramani ta fara ji har ta haddace ta saboda kaunar da take wa wakar...

Idanun sa ya kai kan fatar hannun sa...kofofin gashin jikin sa sun bubud'e wanda hakan baya rasa nasaba da yanda wakar ta yi tasiri har jinin jikin sa, bai kara bari ya kalle inda take ba ya fara takawa cikin tafiya mai kama da sassarfa ya bar wajen.

Bayan ya isa gidan da suka sauka kan gado ya fada, yayi matashi da karfafa hannun sa, yana sauke tagwayen ajiyar zuciya tamkar wanda yayi gudun tsere, ya rasa yadda zai fassara wannan yanayin da ya shiga yanzu...

**********

*HOORAIN*
Zaune suke a karamar tsakar gidan su, kafar ta na cinyar mami tana gyara mata farcen ta abin so adorable. Mafi yawan mutane na mamakin yadda Hoorain ke fara sol, yayinda Mami baka ce.

Shakuwa da soyayyar da suke wa juna abin burgewa ne, tamkar ya da kanwa haka suke.

"Mami mie" Hoorain ta kira Mami da taushin murya.

"Na'am" Mami ta amsa cikin kulawa tana kallon ta.

A karo na uku take son furta Abinda ke ranta amma ta rasa yanda zata fara tambayar Mami amsar da ta dade tana son ji.

Numfashi ta sauke kana tace "Abbi! Mami Please ina yake?"

Kod'add'iyar rezar dake hannun ta Mami ta ajiye, damuwa mai yawan gaske ya bayyana a fuskar ta, hannun Hoorain ta rike da har ta fara hawaye tace

"Hoorain! Sau nawa nace Miki kada ki kara min maganar Abbin ki? Shin akwai abinda na gaza Miki a matsayin uwa? Akwai? Na sani cewa muna cikin matsin rayuwa wanda nake fatan ya zama tarihi watarana, ko kin gaji da zama da ni bana miki yadda kike so?".

Cikin sauri ta rungume Mami tana sakin kuka mai taba zuciya, kan kusumbin ta da kamar kullum kara masa girma ake Mami take shafawa... cikin so, kauna, da tausayin tilon yarta.
Hak'ik'a tana ganin rayuwa wanda babu wanda zai kawo mata sauyi face Ubangiji, bata damu da kanta ba, kullum addu'ar ta shine Allah ya kawo sauyi Na alkhairi a rayuwar Hoorain...
Sam bata son jin Maganar mahaifin Hoorain wanda ya wofintar da su, ko yar sa bai kara waiwaya ba yau shekaru sha biyar kenan, Meye laifin su da suka cancanci wannan sakamakon daga gareshi?...

HOORAIN MAI KUSUMBI (the hunch back girl)Where stories live. Discover now