SADIQ (ƊAN DAKO NE).

113 9 0
                                    

*"SADIQ"*
      ( _ƊAN DAKO NE_ )

     NA

SHAMSIYYA USMAN MANGA.

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION.

Dasunan Allah Mai rahama Mai jin qai.
       
            GODIYA
Godiya ga Allah maɗaukakin sarki da yabani ikon fara wannan littafi Allah kabani ikon gamasa lafiya🤲.

     SADAUKARWA
Wannan page in gaba ɗayansa SADAUKARWA NE Gareki MENERT A YANDOMA Marubuciyar ( BAƘAR TAFIYA)Alkhairin Allah yakaimi a duk inda kike Allah ya ƙaro basira sosai inayinki Tawan♥️🙏😇

.https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
__________________________
*GARGAƊI*
_Labari na banyi shi dan cin mutumcin wani  ko wata ba, in ya cika karo da rayuwar ki arashi ne_


    Page 1&2
     

    .......... Saurayine matashi Wanda aƙalla shekarunsa bazasu haura 26-27 years ba haka,sanye yake cikin wasu Riga da wando Wanda na kasa tantance waɗan ne kalane saboda yadda suka koɗe suka jeme.

      Tafe suke da wata mata wacce aƙalla baxata haura shekaru arba'in zuwa arba'in da biyar ba tana gaba yana biye da ita. Kayane a kansa Wanda yawan kayan da na kalla sai da nadan razana a zuciya na "nace yanzun duk yawan kayannan akan mutum shi daya""

      A dai_dai wannan lokacin suka iso wani titi zasu tsallaka already ita matar har ma ta tsallaka tana ta masa masifa akan baya sauri shidai bai kulataba lura da yayi matar kaman tanada mita.

       Mota qirar Marced Benz ce ta sheƙo da gudu Wanda sai ka rantse da Allah mai tuƙin motar ba a hankalinsa yake ba.

wani mahaukacin burki taja Wanda yayi daidai da zubewar kayan da suke kan wannan saurayin gabadaya a tsakiyar titin Allah ma yaso titin ba irin babban titi bane ba motoci da yawa akai.

      Cike da bala'i wannan matar da suke a tare ta juyo ta daukesa da wani mahaukacin mari Wanda ni kai na sani da na tsora ta  cikin masifa tafara magana.

       " kai wane kalan shasha ne eyee, wane kalan wawan ƊAN DAKO NE wanda bai san mai yakeyiba, wallahi da nasan haka kake da ban fara daurama kayana ba kagodewa Allah da yasa kayana basu samu matsala ba wallahi da sai ka biya"

      Cikin tsananin mamaki yake binta da wani kallo a xuciyanshi "yaace wato ita bama ta lafiyana take ba ta kayanta take Allah ya kyauta."

    Amma a fili sai yace

"hajiya kiyi haƙuri wallahi ba'a San raina hakan ta faru ba bakiga yadda Mai motan yake gudu ba kaman zai tashi sama."?

         " Dallah malam rufamin baki ka kwashe kayan kazo mutafi ba dogon zance nakeso ba."

          Duk abun da yake faruwa har a yanzun mamallakin motar bai fitoba,kuma yana kallonsu duk abun da yake faruwa amma su basu ga Waye a motan ba kasancewan glass in Mae duhu ne.

          Sai yanzun aka bude murfin motar cikin nutsuwa aka zuro qafa waje daga yanayin qafar danagani nafahimci mace ce mamallakiyar motar a hankali ta fito gaba ɗayanta daga cikin motar Masha Allah shine abun da na iya furtawa yarinyace matashiya wacce bazata wuce shekaru ashirin zuwa ashirin da ɗayaba sanye take cikin doguwan Riga maroon colour ta yafa mayafin rigar a kanta amma ba rolling tayi ba.

          Farace doguwa farin nata irin Wanda ya sirka da ja haka watau irin farin turawa tana da hanci amma ba dogo ba da bakinta matsakaici tana da ido amma ba manya ba komae nata de ɗan daidai irin matannan ce wadanda ake cewa musu masu qananan kyau watau sai ka kallesu da kyau zaka fahimci tsantsar kyan da Allah ya musu.

SADIQ (ƊAN DAKO NE).Where stories live. Discover now