*SADIQ*
( _ƊAN DAKO NE_ )
NASHAMSIYYA USMAN MANGA.
*MANAZARTA* *WRITER'S* *ASSOCIATION.*
*_BISIMILLAHIR_* *_RAHMANI RAHIM*_
Page 13-14
..............Napep MUFEEDA ta sake tara inda ta faɗama shi inda zai kaita cikin mintina ƙalilan suka iso cikin unguwartasu.
Tun daga bakin gate ɗin gidansu MUFEEDA jikin ta ya bata ba ƙalao ba dalilin ganin mai gadi da tayi da sauran ma'aikatan gidannasu sunyi cirko-cirko a bakin gate ɗin.
Cikin sauri ta ƙarasa wajen su tana tambayar lafiya.
Maganar tace ta katse ganin Dad ɗinta da tayi ya fito daga gidan fuskar shi babu alamun annuri yana cewa
"Wallahi gaba ɗayanku na baku nan da awa ɗaya kuje ku nemomin inda ƴata ta shiga idan ba haka sai na koreku a aiki kuma sai nasa an kulleku tunda ku baku san aikin ku,ya za'ayi ace har ƴata ta fita a gidannan ko nace har a shigo cikin gidana a ɗauke mun ƴata amma a rasa wanda zai dakatar da faruwan hakan to wallahi na lura............
Bai ƙarasa maganar ba idanuwan shi suka sauƙa masa akan MUFEEDAN da take tsaye a gefe ta kafe shi da ido.
Cikin sauri ya ƙarasa wajenta har yana shirin faɗuwa kallonta yake alamar yana son ya tabattar da cewar tana cikin ƙoshin lafiya.
Sai da ya gama ƙare mata kallo kafin ya fara magana.
"Doughter ina kikaje da safiyar Allah nnan ba tare da kin sanar mun ba fatan dai ba wasu bane suka zo suka ɗauke ki ba kimun magana ko hankalina zai kwanta duk kinsa nida mahaifiyar ki hankalinmu ya tashi".
Kallon mahaifin nata tayi itama tanajin wata soyayyar sa tana ƙara ratsa duk wasu gabobi da suke cikin jikinta har ga Allah tasani cewar mahaifinta yana bala'in sonta sai dai ita halin sa na ƙi da kuma ƙyamar TALAKA shine ba ta so.
"Dad meyasa zaka sa kanka cikin damuwa akan abun da kaima kasan bazai yiwu ba ya za'a yi ace a shigo har cikin gidanka kamar kai Dad ace a ɗauke maka ƴarka ai abun da mamaki gaskiya"MUFEEDA ta faɗa tana so ta sharar da maganar.
"Naji hakane maganar ki Doughter to amma ina kikaje kuma me yasa da zaki fita baki ce Driver ya kaiki ba tunda kinsa banason kina fita haka?".
"Dad yanzu dai mu ƙarasa cikin gida idan yaso sai muyi maganar a ciki kamar zai fi".
Juyawa yayi ya kalli ma'aikatan dasuke tsaye ya daka musu wata uwar tsawa yace su bace masa da gani.
* * *
SADIQ nagani zaune a gaban wasu uban tilin kwanuka ya duƙufa sai wankesu yakeyi.
Ita kuwa Hajiya hakima mai gidan abinci tana zaune a gefe sai kallon shi take ko ƙifta ido batayi a zuciyata nace ita kuwa wannan lafiya kamar wata mayya ta kafeshi da ido haka.
Ya ɗau tsawon lokaci yana wanke kwanukan kafin ya gama.
Tashi yayi ya ɗakko tsintsiya ya share wajen tas ya shigar da kwanukan ciki.
Fitowa yayi ya zo gaban Hajiyan ya tsuguna yace.
"Hajiya nagama idan ba wani abun zan tafi saboda inason naje naga ya jikin mahaifin nawa yake"
Murmushi ta sakar masa wanda saida gaban shi ya faɗi yayi saurin kawar da kanshi.
"Shikennan SADIQ sai kadawo kaje kawai babu wani abu bara in baka kuɗin idan yaso gobe kadawo".
YOU ARE READING
SADIQ (ƊAN DAKO NE).
Ficción GeneralLabarine mai cike da abun tausayi,tsantsar Sadaukarwa,fa'idar biyayyar iyaye da kuma tsantsar zalunci.