" *SADIQ* "
( _ƊAN DAKO NE)_NA
SHAMSIYYA USMAN MANGA.
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION.
Page 3-4
..............Parking space MUFEEDA Ta nufa samu tayi driver har ya fitomata da motar dazata hau wata farar motace ƙirar BMW Sai sheƙi takeyi dagudu driver in yazo zai buɗemata dakatar dashi tayi tana cewa.
"Audu basai kabuɗe ba na hutar dakai zan buɗema dakaina " tafaɗi tana ƙarasawa jikin motar Inda tabuɗe tashiga mazaunin driver.
Key tayiwa motar inda mai gadi ya buɗemata gate in gidan nasu cikin gudunta data saba dashi tafice acikin gidan baba mai gadi yana ɗaga mata hannu.
Cikin abun da baifi minti huɗu zuwa biyar ba takai kanta cikin makarantarsu ta *YOBE* *STATE UNIVERSTY* ( *YSU)* Dakennan cikin garin DAMATURU duk da kasancewar da ɗan tazara tsakaninsu.
*FACULTY OF SCIENCE* Shine abun da naga an rubuta a wajen da ta nufa ciki naga tashiga inda naga an rubuta *DEPERTMENT* *OF* *MEDICINE* anan na fahimci me take karanta.
Hall in tashiga inda tasamu ba wasu mutane dayawa aciki ajiyar zuciya tasauƙe ganin batayi latti ba.
Seat ta nema a gaba-gaba tazauna taciro littafinta tana dubawa inda jiya bata samu damar dubawa ba kafin malamin yashigo.
* * *
Yau dai Alhamdulillah ba laifi SADIQ yasamu kuɗi dalilin kayan daya ɗaukarwa wani Alhaji yakai masa mota Alhajin mai kirki ya zari dubu uku ya basa.
Kamar kullum yau kam da wuri ya baro kasuwar ya kama hanyar gida.
MUFEEDA Ce suka fito daga hall in da suka zana test masha Allah kowa kagansa cike da murna sakamakon test ɗin yazo musu ba yadda suka ɗauka ba saboda da yawansu sun ɗauka zatayi wahala amma sai akasin hakan.
Motarta tanufa tashiga tanufi gida.
Yau ma kamar jiya adaidai titin jiya tagansa saidai yau ba kaya a kansa,parking in motarta tayi a gafen titi ta sauke glass Ɗin motar tana binsa da kallo har sai da ya ƙulewa ganinta.
Motar ta tayar tanufi gida zuciyarta cike da tausayinsa saidai ba abin mamaki bane ba idan kayi la'akari da halinta daman can ita mai tausayice.
Da murna ya ƙarasa shiga layin gidansu saboda yasan koba komai yau zasuci susha saboda ya ɗan samu kuɗi.Saidai mai turus yayi ya tsaya inda ya hango mahaifiyarsa a tsaye a ƙofar gida hawaye sharkaf a idonta cikin sauri ya ƙarasa inda take har yana ƙoƙarin faɗuwa.
" Umma meyafaru naganki a tsaye kina hawaye."?
Cikin shesheƙar kuka tasa hijab ɗin ta fyace majina tace.
"SADIQ Mahaifinka ba lafiya jikinsa ya tashi yanzu haka Fitowar da kaga nayi AISHA nakejira taje ta nemo mana abun hawan daza'a sakasa mu tafi asibiti"
Adaidai wannan lokacin AISHAN suka ƙaraso da mai adaidaita.
Cikin sauri SADIQ suka shiga gidan dashi da mai Adaidaitan inda suka ɗakko baban wanda baisan waye a kansa ba suka nufi asibiti.
*GENERAL HOSPITAL* Dake cikin garin DAMATURU Suka nufa.
A Bakin wani gini naga ya ajiyesu saida na ɗaga kaina sama tukun na iya karanta sunan.
*GOPD COMPLEX* Shine abun da naga an rubuta a jikin ginin fita yayi daga adaidaita in dubu yazaro a aljihunsa yabawa mai adaidaita amma Allah sarki duba da yanayin daya gansu aciki kamar marasa ƙarfi sai yaƙi karban kuɗin.
Godiya SADIQ Yamasa inda cikin sauri yanufi cikin GOPD In don samo kujerar da'ake ɗaukan marrasa lafiya da ita( wheelchair).
Ganinsu nayi sun fito tare da wani mai kaya purple da alama uniform ne yana turo kujerar SADIQ Kuma yana biye dashi.
Ɗaukar sa sukayi a kujerar inda suka nufi cikin GOPD In dashi domin ganin likitan.
Suna zuwa likitan yana ganin yanayin jikin yace kawai a wuce dashi *ACCIDENT AND* *EMERGENCY(A&E)* Saboda he's in critical condition.
Cikin sauri aka nufi A&E ɗin dashi inda likitan yabawa patient in da suke zaune a wurin haquri zaije ya gansa tunda shi Emergency ne.
Nurse ɗin datake on duty ne takalli SADIQ tace.
"Bawan Allah muna buƙatar folder kaje yanzu kayanko ka kawo mana saboda ba'a ganin patient ba folder"
Dasauri SADIQ Yafita yanufi inda ake sayar da folder duk da saida yayi tambaya aka nuna masa dari biyu akace masa nan yazaro dubun aljihunsa ya basu tambayarsa sukayi duk wani information akan patient yafaɗa musu suka cika suka bashi.
Juyawa yayi yanufi A&E Ɗin yaje yakaimusu folder in ta window ya hango likitan akan mahaifin nasa yanataso yayi yadda zaiyi dan ganin ya ceci rayuwar patient in.
Likitanne yafito yana goge gumi cewa yayi amasa magana da ɗan uwan marar lafiyar yasamesa a office ɗinshi.
*COMMENT SHARE*and VOTE *FISABILILLAH* 🙏
_SHAMSIYYA MANGA CE✍️_ ✍️.
YOU ARE READING
SADIQ (ƊAN DAKO NE).
General FictionLabarine mai cike da abun tausayi,tsantsar Sadaukarwa,fa'idar biyayyar iyaye da kuma tsantsar zalunci.