*SADIQ*
( _ƊAN DAKO NE)._NA
SHAMSIYYA USMAN MANGA.
MWA
Page 7-8
..............Kamar yadda ma'aikatan lab ɗin suka faɗawa SADIQ after two hour's ɗin kuwa sai gashi sun ƙirasa sun bashi result ɗin.
Office ɗin likitan ya nufa don kai masa sakamakon gwajin cikin wani irin sauri kaman zai tashi sama.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya isa office ɗin yayi sa'a kuwa marar lafiya mutum ɗaya ya tarar likitan yana gani.
Zama yayi a bakin office ɗin yana jira mutumin ya fito shikuma ya shiga.
Bai wani ɗau dogon lokaci ba mutumin ya fito yace masa yashiga inji likitan daman already securityn da yake bakin ƙofan ya faɗawa likitan zuwan shi.
Ƙofar office ɗin ya tura a hankali da sallama a bakin sa.
Likitanne ya amsa yace masa ga kujera ya zauna.
Zama yayi yana mai miƙa mashi sakamakon gwajin.
Karbar gwajin yayi yana mai gyara glass ɗin da yake idonsa,bayan ya gama duba sakamakon dagowa yayi yana mai duban SADIQ ɗin sannan ya fara magana.
"SADIQ ina son kabani hankalinka gaba ɗaya domin ka nutsu ka kalla abun da zan faɗa da idon basira,kasan dai cewar cuta ba mutuwa bace ba ko sannan da jinya da lafiya duk Allah ke bayarwa to kardai nacika ka da surutu watau a zahirin gaskiya SADIQ zamu turaku zuwa babban asibiti saboda gaskiya jinyar mahaifinka tana buƙatar kuje ku babban asibiti wanda suke da kayan aiki".
Cikin tashin hankali SADIQ ya ɗago yana kallon likitan sannan yace.
"Yalla'bai don Allah kayi saurin sanar dani abun da yake damun mahaifina"
Gyaran murya likitan yayi sannan ya cigaba da magana.
"A zahirin gaskiya mahaifinka yana fama da ciwon ƙoda wanda a turance ko nace a yaren likitanci muke ƙiransa da CHRONIC KIDNEY DISEASE(CKD)wanda yana buƙatar a masa aiki zamu iya kiransa kamar wankin ƙoda a hausance watau(DIALYSIS) kuma gaskiya mu bamu da kayan aikin yi saidai kuje irin TERTIARY FACILITIES ɗinnan su suke da kayan aikin.
Jikin SADIQ ne ya ƙara yin sanyi domin yasan gaskiya idan yace suna da kuɗin tafiya wani babban asibiti a yanzu yayi ƙarya to amma bakomai Allah zai yi.
Maganar likitan ce tadawo dashi daga tunanin da ya tafi.
"Yanzu zakaje ka karbo mana wata takarda(REFERRAL FORM) wacce zan rubuta muku tafiya wancan asibitin a jiki.
Tashi yayi jikinsa duk babu ƙwari ya nufi hanyar fita daga office ɗin don zuwa karbowa abun da likitan yace.
Bayan ya fito daga office ɗin tamabayar securityn da yake bakin office ɗin likitan yayi inda zaeje ya karbo referral form ɗin.
Nunamasa yayi ashe ma bawani nisa sosai.
Hanyar wajen ya nufa inda ya isa cikin ƙanƙanin lokaci,wani ɗan saurayi ya tarar a wajen inda ya faɗamasa abun da yake buƙata,cewa yayi ya bada naira ɗari,ɗarin ya zaro ya miƙa masa inda ya karbo form ɗin ya nufi office ɗin likitan.
* * *
4:00pm daidai jirgin su Dadyn MUFEEDA ya sauƙa a Airport a daidai wannan lokacin kuma suma motocin su suka iso cikin Airport ɗin.
Parking sukayi a wurin da aka tanada domin ajiye motoci.
A hankali yake saƙowa daga matakalar jirgin inda yake sanye da wasu Ash colour ɗin suit fuskar shi sanye da glass siriri fari da alama na ƙarin ƙarfin idone,kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa ɗan boko ne na sosai waɗan da suka sha boko suka gaji da ita.
YOU ARE READING
SADIQ (ƊAN DAKO NE).
Genel KurguLabarine mai cike da abun tausayi,tsantsar Sadaukarwa,fa'idar biyayyar iyaye da kuma tsantsar zalunci.