" *SADIQ* "
( _ƊAN DAKO_ _NE__ ).NA
SHAMSIYYA USMAN MANGA.
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION.
Page 5-6
.............Office ɗin likitan SADIQ ya nufa hankalinsa duk a tashe saboda bai san mai likitan zai faɗa masa ba.
Handle ɗin ƙofar ya kama ya tura ƙofar da sallama ɗauke a bakinsa.
Amsa sallamar likitan yayi yana cigaba da rubutu a file ɗin da yake gabanshi.
Ɗagowa yayi da alama ya gama rubutun kennan inda yakai dubanshi wajen SADIQ da yake tsaye kaman gunki,kujerar dake gaban shi ya nunamasa yanamasa alama da ya zauna.
Zama yayi a kan kujeran yan mai fuskantar likitan domin shidai ya matsu yaji mai yake damun mahifinsa.
Likitanne ya ɗago yana mai dubanshi yace.
"Malam SADIQ ko,to abun da yasa na ƙiraka bakomai bane sai dan inason zanabaka wasu gwaje-gwaje zakaje ko iyo mana domin musan takamai mai abun da yake damun mahaifinka domin muma asibiti bama abu uphead dole sai anyi gwaji abun da gwaji ya nuna dashi muke anfani fatana dai kawai shine kar Allah yasa abun da nake suspecting ya tabbatta,anyway kar nacika ka da surutu ga waɗannan takardun zakaje ɗakin gwaji watau Lab zaka mana wannan gwajin kuma a yau nake buƙatar sakamakon don haka ma yasa a jikin ko wane gwaji na rubuta urgent saboda su san cewa da gaggawa nake buƙata.
Investigation form ɗin SADIQ ya karba yanajin zuciyar shi tana wani irin bugu saboda bai san kuma mai zaije ya tarar a lab ɗin ba.
Ɗagowa yayi a hankali da idanunsa da sukayi jajir kamar wuta ya dubi likitan yace.
"Amma yalla'bai menene abun da kake tunanin yana damun mahafina".
Murmushi likitan yayi yace.
"Karka damu bawani abun tashin hankali bane ba koma meye zamuji idan result ya fito kaidai kawai kaje kayi gwajin da na baka".
Tashi yayi jikinsa duk a sanyaye ya nufi ƙofar fita daga office ɗin.
Tafiya yake amma shi kanshi bai san ina yake jefa ƙafar shi ba,sai yayi tafiya mai ɗan nisa kasancewar asibitin da girma kafin ma ya tuna cewar shifa bai san ma inane wajen gwajin ba gashi ya bar su Umma a can bakin ɗakin da Abban yake ciki,har ya juya zai koma wajen Umman ya musu bayani kawai sai ya tuna da likitan fa yace dasauri yake son result ɗin.
Wasu samari ya hango su uku sun nufi wata hanya da takarda a hannunsu kamar irin wacce likitan yaba shi,nufar su yayi cikin sauri ko zai yi dacen Allah yasa inda zashi suma zasu.
Sallama ya musu inda suka amsa suna kai duban su gare shi.
"Bayin Allah tambaya nake ko kun sani don Allah"shine abun da naji yace.
"Allah yasa mun sani"suka haɗa baki wajen bashi amsa.
"Don Allah ɗakin gwaji nake so ku nuna min idan ba damuwa"
"To kaci sa'a muma can muka nufa muje kawai".
Hanyar lab ɗin suka nufa duk su huɗun.
* * *
MUFEEDA tana isa gate ɗin gidansu horn tayiwa mai gadi inda yazo dasauri ya buɗe mata gate in tashiga.
Tun daga parking lot in takejin ƙamshin girke-girke iri-iri yana tashi a gidan murmushi tayi domin tasan Momy ba daganan ba indai wajen iya girkine.
YOU ARE READING
SADIQ (ƊAN DAKO NE).
Ficción GeneralLabarine mai cike da abun tausayi,tsantsar Sadaukarwa,fa'idar biyayyar iyaye da kuma tsantsar zalunci.