*SADIQ*
(ƊAN DAKO NE).NA
SHAMSIYYA USMAN MANGA.
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION.
Page 9-10
...........Mai napep SADIQ yaje ya nemo a bakin gate inda suna zuwa suka samu har Umman sun shirya shi ɗakko shi sukayi akan kujerar marassa lafiya(wheelchair) wanda shi baima san a wani hali yake ciki ba,a napep ɗin suka sanyashi inda Umma tazauna a gafenshi AISHA ma tazagaya ta ɗayan bangaren.
SADIQ ne yazauna a gefen mai napep ɗin inda suka fice daga asibitin suka nufi titin da zai sadasu da babban asibitin da likitan ya turasu.
Sun ɗanyi tafiya mai ɗan tsayi kafin suka iso gate ɗin asibitin kasancewar asibitin yana farkon garine.
*YOBE STATE* *TEACHING HOSPITAL* shine naga an rubuta da manyan baƙi a saman asibitin.
Kallon asibitin SADIQ yakeyi yanajin gabansa yana faɗuwa saboda tun daga yanayin asibitin kasan akwai cin kuɗi.
Tsayar dasu securities ɗin dasuke bakin gate ɗin sukayi kasancewar a dokar asibitin public car bata shiga indai ba ma'aikacin asibitin bane a ciki ba ko kuma irin unconcious patient ɗinnan.
Tambaya suka shiga yi musu sukuma suna basu amsa saida suka bincika napep ɗin tsaf kafin su buɗe musu gate ɗin su shiga.
Direct ACCIDENT AND EMERGENCY UNIT suka nufa dashi kasancewar mai napep ɗin yasan kan asibitin sosai shi yayi musu jagora.
Nurse ɗin datake on duty suka samu a zaune a kan wata kujera,miƙamata takardar hannun su sukayi,karba tayi ta duba inda tabawa wani mutum da yake gefenta da alamu likitane.
"Bawan Allah kaje ka siyo mana babban kati(folder)likita zaiyi rubutu a ciki.
Juyawa yayi ya nufi ƙofa inda ya bar su Umman a wajen don zuwa nemo katin da akace mashi.
Bayan wasu ƴan mintina sai gashi ya dawo hannunsa ɗauke da babban katin.
Miƙa ma nurse ɗin katin yayi ita kuma ta baiwa likitan,karba yayi ya ɗanyi wasu ƴan rubuce - rubuce a ciki.
"Sister kifaɗawa Sub staff ɗinki su ɗauki wannan patien ɗin ya rakasu ɗakin maza( *MALE WARD*)".
Wani mai purple ɗin kaya nurse ɗin ta kira ta bashi folder ɗin tace ya kai ɗakin maza.
Karban katin yayi yacewa su SADIQ su biyoshi dan zuwa ɗakin da aka tura su.
* * *
Yau wajen kwana uku kennan kullum MUFEEDA tana biyo titin da take ganin SADIQ amma sai bata ganinshi,tun abun bai damunta har tafara jin wani abu a ranta ita dai tasan tana tausayin shi kuma tana da ra'ayin taimaka mashi.
Yau ma kamar kullum ta taso daga school wajen ƙarfe huɗu parking mota ɗinta tayi a gefen hanya tana kallon masu wucewa takusa kaiwa awa a wajen amma ko mai kama da SADIQ bata gani ba.
Gajiya tayi da tsayuwar ta tayar da motar ta ta nufi gida amma ta ƙudirta a ranta cewar gobe zata shiga cikin unguwar ta tambaya ko zata samu wanda ya san shi domin ita gaskiya tana ji a ranta ba ƙalao ba kuma yana buƙatar taimako.
Ta isa gida inda ta iske Momy a falo tana zaune tana kallo ,zama tayi a kujerar dake kusa da Momyn tana mata barka da hutawa.
"MUFEEDA kindawo amma sai naga kaman kin daɗe yau ɗin fatan dai lafiya".
Ajiyar zuciya MUFEEDA ta sauƙe tana duban Momy ita a gaskiya bata iya boyewa mahaifiyarta komai da ya danganci rayuwarta.
"Wallahi kuwa Momy yau kam na ɗan daɗe,yawwa Momy nikam ina wannan ƊAN DAKON da na taba baki labari na kusa kaɗewa"
Shiru Momy tayi kaman mai nazarin wani abu can sai tace
"Eh na tunashi wani abune ya faru da shi?"
"A'a Momy ba abun da ya faru dashi kawai dai kwana biyu ne na saba ganin shi a hanyar dawo wa ta daga school amma yau waje kwana uku bana ganinshi sai nake jin kaman akwai abun da ya same shi kamar yana buƙatar taimako"ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka.
"To ikon Allah! to ke meye naki a ciki don bakya ganin shi kwana biyu meye damuwan ki?"Momy ta faɗa da alamar mamaki shimfiɗe a fuskarta.
"Momy bakomai wallahi kawai dai yana bani tausayi ne daga ganin shi kinsan yana ganin rayuwa"
"To Allah ya kyauta " cewar momyn.
Shigowar Dad ɗin MUFEEDA falon shi ya katse musu hirar tasu.
"Dad sannu da dawo wa" MUFEEDA ta faɗa tana ƙoƙarin tashi tabar wajen don bata son Dad ɗin ya fahimci cewar tana cikin damuwa.
Amma ina ta makara domin kuwa kallo ɗaya Dad ɗin ya mata ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita.
"Doughter kaman kina cikin damuwa?" ya jefo mata tambayar da batayi tsammanin jin ta a bakinsa ba,tsintar kanta tayi da bashi amsa.
"Dad kaina ke ciwo nasha magani zanje na kwanta"
"Subahannallah to ko dai na ƙira likita yazo ya ganki" ya ƙarasa maganar cikin ruɗewa.
"A'a Dad zanje nakwanta ƙila bacci ne idan natashi zai daina".
"To shikennan abinci fa kin ci amma ko?"
"Dad sai na tashi zanci".
Bata jira mai zai ƙara cewa ba ta nufi ɗakinta cikin sauri don bata son magana she need rest.
* * *
SADIQ na hango zaune a office ɗin likita da alama bayani yake masa akan jinyar mahaifin na shi.
Likitan nagani wani ɗan kyakyawan mutum bafulatani fari tass dashi maganar shi naji yana cewa.
"Naga duk bayanan wancan likitan da ya turoku a cikin takardar da ya baka,to kaman yadda ya faɗa ma mahaifinka yana buƙatar aiki na wankin ƙoda watau( *DIALYSIS*) kuma a gaskiya a wannan asibitin aikin da za'a wa mahaifinka yana buƙatar kuɗi kimanin naira dubu hamsin(50,000) banda kuɗin magani da za'a buƙata idan anyin aikin da kuma kuɗin gado,don haka zaka iya tafiya ka kawo kuɗin zuwa gobe ko jibi insha Allahu za'a fara aikin mahaifinka wannan shine kaɗai bayanin da zan iya maka a yanzu saidai zan ƙara tuna maka kayi duk ƙoƙarin da zakayi don ka kawo waɗannan kuɗaɗen a kan lokaci domin mahaifinka yaje stage ɗin da aikin kawai shine best choice namu".
Tashin hankali iya tashin hankali SADIQ ya shiga to shi a ina ma zai fara nemo dubu hamsin a cikin kwana ɗaya shida ko dubu goma bai taba riƙewa ba?.
_Allah sarki SADIQ ni_ _kaina na tausaya_ _ma gashi ku bawata_ _ƙwaƙwarar kadara ba_ _balle ku siyar_ _wayyo SADIQ kuna_ _ina team SADIQ kuzo_ _mu koka_ 😢😭😭😩.
_Nayi typing yau insha_ _Allah bayan_ _sallah zamu ci gaba_ _banso na tsaya ba_ _saboda inason na ci_ _gaba da sambaɗo_ _muku labari amma_ _bakomai immediately_ _after_ _sallah i will be back_ _fatan za'ayi sallah_ _lafiya sannan ayi a_ _hankali kar aci nama_ _da yawa azo_ _ayi ta zaryar toilet_ 😄😜.
FOLLOW
VOTE
COMMENT*SHAMSIYYA* ✍️.
YOU ARE READING
SADIQ (ƊAN DAKO NE).
Genel KurguLabarine mai cike da abun tausayi,tsantsar Sadaukarwa,fa'idar biyayyar iyaye da kuma tsantsar zalunci.