SADIQ ƊAN DAKO 11&12

31 2 0
                                    

*SADIQ*
    ( _ƊAN DAKO NE_ ).

     NA

SHAMSIYYA USMAN MANGA

*MANAZARTA* *WRITER'S* *ASSOCIATION.*

*_BISMILLAHIR_* *_RAHMANI RAHIM._*

*DA SUNAN ALLAH* *MAI RAHAMA MAI* *JIN ƘAI.*

*ALHAMDULILLAH*
*ALHAMDULILLAH*
*ALHAMDULILLAH*

*ALLAH MUN GODE* *MAKA DA KABAMU* *IKON* *GANIN WANNAN* *SALLAH TA IDI* *SANNAN KUMA* *KABAMU IKO MUKA* *YITA LAFIYA*  *MUKA* *GAMA LAFIYA.*

*INA YIWA ƊAUKACIN* *MASOYA LITTAFIN* *SADIQ* ( *_ƊAN* *DAKO_ NE)* *BARKA* *DA SALLAH* *DA KUMA* *FATAN KOWA* *YAYI SALLAH* *LAFIYA* *ALLAH YA MAIMAITA* *MANA* *AMEEN YA HAYYU YA* *ƘAYYUM* 🤲🤲👏 *.

*_KAMAR* *YADDA_** *NA FAƊA* *IMMEDIATLY ANA* *YIN SALLAH ZAN CI* *GABA DA* *POSTING ƊIN* *LITTAFINNAN DAGA* *INDA NA* *TSAYA TO GASHI NA* *CIKA* *ALƘAWARI,SAI DAI* *KUMIN FATAN ALLAH* *YA BANI* *IKON GAMAWA* *LAFIYA AMEEN* 🤲😇

Page 11-12

..............Tashin hankali iya tashin hankali SADIQ ya shiga,to shi a ina ma zai fara nemowa dubu hamsin a cikin kwana ɗaya ,shida ko dubu goma bai taba riƙewa ba?

Tambayar kennan da yayiwa kan shi acikin zuciyar shi domin wallahi yasan shidai bashi da hanyar da zai samo waɗannan maƙodan kuɗin a cikin kwana ɗaya dai,maganar likitan ce ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi.

"Malam lafiya kake kuwa inata magana kayi shiru".

Murmushi ya ƙaƙaro wanda shi ba kuka ba shi ba dariya ba wai ance yaƙe kafi kuka ciwo ya dubi likitan da idanuwan shi da kana kalla zaka iya hango tsantsar tashin hankalin da yake ciki yace.

"Likita yanzu dole sai a cikin kwana ɗaya zuwa biyu zan kawo kuɗin bazai yiwu a yi masa aikin ba idan yaso daga baya sai na kawo kuɗin?"

Tambayar da SADIQ ya jefawa likitan kennan.

"A gaskiya bazai yiwu ba idan ma munyi wa mahaifinka aiki ba kuɗi to kuɗin magani fa wanda nasan a ƙalla shima zai iya kaiwa wajen dubu talatin to kaga dole ma sai ka nemo kuɗin maganar gaskiya, domin bazai yiwu a masa aiki ba kuɗi ba ni idan ta nine wallahi bani da matsala za'a iya masa aikin kyauta ma to amma ni bani kaɗai zanyi aikin ba sannan kuɗi na asibitine ba nawa ba ina fatan ka fahimce ni.

Kai kawai ya iya ɗagawa likitan inda ya miƙe da niyyar barin office ɗin domin yaje yaga abin da Allah zaiyi.

Idanuwan shi duhu suka masa inda da ƙyar yake iya ganin gaban shi ma, a haka ya fita daga office ɗin ya kama hanyar fita daga asibitin domin ya gama yanke shawarar ko wajen su Umma  bazai koma ba har sai ya nemo waɗannan kuɗaɗen.

A haka ya isa gate ɗin asibitin inda ya kama tafiya ba tare da yasan ko ina zai je ba saidai yana roƙon Allah ya kawo mashi mafita kawai.

Tafiya yayi sosai inda ya iso bakin wani shago ya samu ana sauƙewa mai shagon kaya da alamu sari yayi.

Cikin sauri ya ƙarasa bakin shagon har yana shirin faɗuwa kayan shima ya shiga jida yana miƙawa cikin shagon har suka gama tass.

Juyawa yayi yaje wajen mai shagon inda ya samu waɗannan waɗan da suka sauƙewa mai shagon kaya tare sun jaru a gaban shi da alamu jira suke ya sallame su.

Kuɗi mai shagon ya zaro a aljihun shi wanda SADIQ bai san nawa bane ya miƙawa ɗaya daga cikin mutanen da suke tsayen.

Kuɗin suka karba suka mishi godiya inda suka nufi hanyar fita a shagon.

SADIQ (ƊAN DAKO NE).Where stories live. Discover now